|
Ganin {yashi
Ke Kawo Sa-In-Sa A Tsakanin ’Yan Fim–Ru}ayya Usman
GTK:
Mai karatu zai so sanin cikakken sunanki.
RU{AYYA: Sunana Ru}ayya Usman, ni, ’yar fim, ce ta Kaduna, kuma ina zaune ne a
Zariya. Ina aiki }ar}ashin kamfanin “Bayajidda Productions”.
GTK: A matsayinki na ’ya mace, wa]anne irin }alubale kike fuskanta cikin wannan
harka?
RU{AYYA: To, ba zan ce ba na fuskantar }alubale ba, domin gaskiya akwai musamman
ma ta fannin ’yan uwana da dangina, kasancewa ita wannan harka ta fim za a iya
cewa, tana da farin jini, haka kuma tana da ba}in jini. Kafin a ce mutum ya
shige ta, da zarar ya furta, to, fa ’yan uwa za su fara cewa a’a, ba su amince
ba, saboda ganin cewa ana wa ’yan fim kallon ’yan Iska. To, amma kuma wata
sana’a ce ta dogaro da kai, muddin dai mutum ya yarda da ita, za ta iya sama
masa duk wani abu wanda zai iya dogara a gareta.
GTK: Akwai wata gudunmawa da kike bayarwa don ganin kin kare mutuncin addininki
da al’adarki a harkar fim?
RU{AYYA: Eh, gaskiya, ina bada gudunmawa domin da ma shi ]an fim mai fa]akarwa
ne a kowane lokaci. Cikin gudunmawar da nake bayarwa ni ma a yanzu zan iya kiran
kaina furodusa domin na shirya fim, ya shiga kasuwa, kuma jama’a da da ma suna
ta bugo mini waya suna mini sam-barka, suna mini fatar Allah Ya }ara mini basira
domin ci gaba da shirya irin wa]annan fina-finan.
A cikin wannan fim ]in da na shirya, har aka yi, aka gama, ba inda ake sa }ananan
kaya daga mazan har matan, haka kuma babu inda aka yi rawa da za a ce tir.
GTK: Wane fim kenan?
RU}AYYA: Sunan shi “Zaman Aure” kashi na ]aya ya fito, na biyu kuma yana kan
hanya.
GTK: Ga shi dai ke matashiya ce, kina kuma da kusan dukkan kamannin da furodusa
ke nema idan zai sa wata ’ya mace a matsayin budurwa a fim ]insa, amma sai na ga
kin fi fitowa a matsayin babba ko in ce matar aure, ko akwai wani dalilin yin
hakan?
RU{AYYA: Gaskiya, ba ni da wani dalili, kawai dai yanayi ne da duk inda aka sa
ka, haka za ka fito.
GTK: Ana ganin cewa ba ki da]e a harkar fim sosai ba, amma sai ga shi kin ]auki
harkar furodusa a lokaci ]aya, kina ganin abu ne mai sau}i da za ki iya ci gaba
da shi?
RU}AYYA: Eh, to, gaskiya, ba abu ne mai sau}i ba, domin aikin furodusa, wato mai
shirya fina-finai abu ne mai matu}ar neman rikita mutum, amma idan ka bi a
hankali ka sa ro}on Allah a gaba to, komai zai zo maka da sau}i.
GTK: A cikin fina-finanki, wane ne ya fi kwanta miki a rai?
RU{AYYA: To, ba don kar a ce son kai ba, sai in ce fim ]ina na “Zaman Aure” ya
fi kwanta min a rai.
GTK: Wane sa}o kika so bayarwa ga al’umma a wannan fim ]in?
RU{AYYA: Wani babban muhimmin sa}o ne zuwa ga mata, matan kuma wa]anda suke bada
aminci ga }awaye, suna ]aukar sirrinsu suna fa]awa }awayensu.
Wannan fim ]in ya nuna cewa, ba abu ne mai kyau ba, ki ri}a ]aukar sirrin da ke
tsakaninki da mijinki kina fa]a wa }awarki domin ta hakan, tana iya fitar da ke
daga gidan, idan da dama ma ita ta shige. To kin ji sa}on da muka gabatar.
GTK: Wa]anne irin matsaloli kuke fuskanta wajen shirin fim?
RU{AYYA: Irin wannan aiki babu yadda za a yi a guje wa matsala domin wani lokaci
za ka so ka tara ’yan wasa, idan ka ba su lokacin da za a ha]u, wani zai zo,
wani kuma ba zai so ba, shi wanda ya zo zai uzura maka cewa, ya }osa ya yi
aikinsa ya tafi, sannan kai kanka ya yi zafi kana ta }o}arin ganin cewa lallai
wanda ake jira ya zo “Location”, wato wurin shirya wasa ya iso, saboda haka
akwai ire-iren wa]annan matsalolin.
GTK: A matsayinki na ’yar fim, ya kuke ji idan kin shiga wasu wurare kuma kika
ga hankalin jama’a ya karkato kanki, ana ta ga wance, ga wance?
RU{AYYA: A gaskiya, ina jin da]i, saboda in banda dalilin fim, babu wanda zai
kalle ni ya ce ga wance.
GTK: Za ki iya bayyana mana ka]an daga cikin alheran da kika samu a sakamakon
wannan sana’a ta fim?
RU{AYYA: Gaskiya, suna da dama, amma babban alherin da zan ce na samu shi ne na
ganin ni ma na shirya fim nawa na kaina, kuma sauran ’yan fim sun tagaza mini
sosai wajen shirya fim ]in. Alhamdulillahi, wannan ma babbar nasara ce da na
samu a fim industiri.
GTK: Me ke kawo yawan sa-in-sa a tsakanin ’yan fim, musamman ma mata?
RU}AYYA: Ganin }yashi ne kawai ba wani abu ba. Domin zai iya yiwuwa wata ta ri}a
ganin yaushe wance ta zo industiri har ta yi suna, yaushe wance ta zo har za ta
]aura zani iri kaza, ko za ta hau mota iri kaza? Ni a ganina irin wa]annan
abubuwa su ke kawo sa-in-sa a tsakanin mata.
GTK: Ana neman sa dokar hana rawa da wa}a a fim, kina ganin idan babu wa]annan
abubuwa, fim zai yi armashi?
RU{AYYA: Eh, zai iya yiwuwa tun da a da can ana fim babu wa}e-wa}e ko raye-raye,
kuma ana sayarwa a kasuwa, saboda haka yanzu ]in ma idan aka ce an soke su ba
wata matsala ba ce.
Ka ga kamar fim ]inmu na kamfanin “Bayajidda”, ba rawa ba wa}a kuma ya shiga
kasuwa, wanda har daga }asashen waje, an yi ta bugo mana waya ana mana godiya
game da wannan fim ]in.
GTK: Yaya kika ji a rana ta farko da darakta ya fara aza kyamara a kanki?
RU{AYYA: A gaskiya, gabana ya yi ta fa]uwa, ina ganin kamar ba za a sami abin da
ake so ba daga gareni amma daga baya sai na saki jikina.
GTK: Wane fim ne kika fara yi a Hausa fim industiri?
RU{AYYA: Fim ]in da na fara yi na farko zan iya cewa, har yanzu bai shiga kasuwa
ba amma mabiyinsa shi ne “Kawali” na kamfanin “Mirror Of The Moment” da ke
Zariya.
GTK: Ko kina da wata shawara ga ’yan uwanki, ’yan fim, musamman ma mata?
RU}AYYA: To, a duk inda mutum yake ya kamata ya ria kame kansa musamman ma mata,
domin a ko’ina ita mace uwa ce, ko ba jima ko ba da]e kina sa ran za ki yi aure
ki haihu, saboda haka ’ya’yanki da kika haifa za su taso su ga abin da kika
aikata ko su ji labari.
Don haka ya kamata a duk inda muka tsinci kanmu, mu kasance masu ]a’a, masu
mutunta kanmu, domin sai ka mutunta kanka ne sannan wani zai mutuntaka.
GTK: Akan yi zargin cewa, mata ’yan fim saboda jin da]in fim da kuma yadda suke
samun ku]i yana hana su yin aure da wuri, wasu kuma idan sun yi auren ba sa zama,
me za ki ce game da hakan?
RU{AYYA: To kowa dai da ra’ayinsa, kuma ni ina ganin aure wani abu ne da yake da
rai, idan Allah Ya riga ya }addara mutuwarsa kuma, to, ba yadda za a yi. Kuma
idan jama’a sun lura, mata da yawa a gari suna }in yin aure har shekarunsu su
wuce na shekarun ’yan fim, amma kin ga ba a duban su.
Ni na san cewa, akwai }awayen da nake da su wa]anda a}alla sun kusa shekara
talatin da wani abu, ba su yi auren fari ba kuma ba ’yan fim ba ne, ba kuma a
tambayar su me ya sa ba ku yi aure ba. Saboda haka wannan duk ba hujja ba ce.
GTK: Ko za ki iya auren ]an uwanki ]an fim?
RU{AYYA: Idan Allah Ya }addara ]an fim mijina ne zan iya auren sa.
GTK: Kina da burin yin aure nan kusa?
RU{AYYA: Eh to, da yake aure abu ne da na ta~a yi, na san da]insa na san rashin
da]insa, ina da burin yin aure insha Allahu, ina kuma ro}on Allah Kada ya ]auki
raina sai na yi aure. |