|
|
|
Mutanen
Kudan Sun Yi Dacen Shugaba
DIMOKURA[IYYA
tsari ne da ke ba jama’a cikakken ’yanci ta hanyar siyasa na su za~i wanda suke
bu}ata ko kuma mutum ya sami cikakken ’yancin tsayawa domin jama’a su za~e shi a
kan kowane irin matsayi da tsarin mulkin }asa ya bayar da dama ga jama’a, su
nema tun daga matakin }aramar hukuma zuwa jiha da }asa baki ]aya wato tarayya.
Sakamakon wannan dama ce ta siyasa a tsarin dimokura]iyya ya sa mutane da dama
ke zaune a wurare daban-daban tun daga matakin unguwa zuwa gari da manyan
garuruwa da suka zama mazaunin jiha da ake ganin nan ne mazaunin gwamnatin jiha
da ke tara al’umma da yawa fiye da sauran sassa.
A wa]ansu wurare, za ka ji irin wa]annan al’umma da suke zaune a wurare
daban-daban za ka ji wa]ansu na yin murnar samun ingantaccen shugaban da suka
za~a ta hanyar tsarin dimokura]iyya, za ka ji suna murna, wasu kuma suna cikin
wani hali na rashin gamsuwa sakamakon rashin samun ribar dimokura]iyya.
Kuma wannan samun riba ko rashin samun ribar dimokura]iyya ya kusa zama ruwan
dare a tsakanin al’ummar Nijeriya, saboda za ka ji wa]ansu na kukan cewa, su tun
da suka za~i wane a matsayin wakili ko wani da zai ri}e masu wani ofis da ya
zama dole sai ta hanyar siyasa ne, za a iya za~en duk wanda zai yi wa al’umma
jagora, saboda a wani lokaci za ka ji abin ya zamanto wa]ansu mutane na cigiyar
ainihin ]an majalisarsu da suka za~a ta hanyar tsari irin na dimokura]iyya domin
ya yi masu ~atan dabo, sun rasa inda za su lalubo shi ballantana kuma su san
shirin wane, irin shugabanci ne suke fuskanta.
Ma’ana dai shin yana kare masu bu}atunsu ne ko a’a? Saboda sanin kowa ne irin
wannan tsari na dimokura]iyya da ke da ’yancin yi nza~e suka kuma za~i ainihin
wanda suke so don yi masu mulki, ko wakilci, su ba su damar su yi idanu hu]u da
wakilinsu ko wanda suka za~a sai a matakin }ananan hukumomi a }asar nan baki ]aya.
Saboda wani wakilin in ya tafi Abuja in na tarayya ne, in kuma na jiha ne shi
kenan zai tafi ne ya kama yin hidimar gabansa da sunan yana wakiltar wasu jama’a
da ya fito daga cikinsu, domin hasalima ma za ka ji a fili yana cewa, shi
za~a~~en wakili ne tun da dai ga wata shaidar takarda da ke nuna cewa, an za~e
shi daga waje kaza ya zo tarayya ko jiha domin ya wakilce su.
To, a bisa dukkan alamu al’ummar da ke zaune a }aramar hukumar Kudan da ke cikin
Jihar Kaduna sun yi dacen shugaba wanda zai yi masu shugabanci daidai da irin
bu}atunsu domin share masu hawaye ta hanyar aiwatar masu da aiki kamar yadda ya
dace su sami ci gaba. Ka ga kenan a iya cewa al’ummar }aramar hukumar Kudan da
ke cikin Jihar Kaduna sun yi dacen shugaba, mai kishin ci gabansu wato Alhaji
Abdullahi S. Ahmad.
Shi wannan bawan Allah, Alhaji Abdullahi S. Ahmad mutum, ne da mutanen }aramar
hukumar Kudan ba su ta~a samun mutum irinsa ba, domin shi ne ya rungumi jama’a
marasa galihu yake tallafa masu ta yadda rayuwarsu za ta inganta, saboda shi ya
fito fili ya bayyansu da cewa su ma mutane ne kamar kowa, don haka sun cancanci
kowane irin taimako kasancewarsu a cikin wannan }aramar hukuma ta Kudan da ta
kasance ]aya daga cikin }ananan hukumomin Jihar Kaduna da ke tarayyar Nijeriya.
Koda irin wannan ka]ai kawai aka tsaya, mutane za su zama shaidar cewa al’ummar
wannan }aramar hukuma ta Kudan sun sha bamban da sauran wa]ansu al’ummar da ke
ta famar cewa su ba su sami damar da na kan keke zuwa ga masu tafiya a kan babur
ko mota kai har ma da masu amfani da jaki da dai sauransu.
Ta ~angaren samar da ilimin makarantar firamare, kai ka ce babu wani wurin da
aka ta~a gudanar da wata hidima ta ci gaba sai nan kawai, saboda duk makarantun
firamare da ke fa]in }aramar hukumar babu makarantar da ba a kai mata ]aukin
ayyukan da suka dace daidai da bu}atarta ba.
Uwa uba kuma sai ta ~angaren }arin albashin malaman makaranta tare da kula da
lafiyarsu, duk domin }ara inganta matsayin ilimi a fa]in }aramar hukumar baki ]aya.
A halin da ake ciki, na je na gane wa idanuna irin yadda asibitoci aka wadata su
da magunguna iri-iri, kamar dai yadda ya dace a yi ga kowane irin asibitin da
ake samun ribar dimokura]iyya a cikinsa kuma manya da yara maza da mata ke
ta}ama da shi a duk fa]in Nijeriya baki ]aya.
{aramar hukumar Kudan, }ar}ashin jagorancin Alhaji Abdullahi S. Ahmad ba ta
tsaya a nan ba, domin kuwa idan aka dubi irin ]imbin ayyukan raya }asa da aka
gudanar domin ci gaban al’umma, nan ma sai a ga cewa, ba a barta ta daga baya.
Daga cikin ]imbin ayyukan da za a iya yi wa makaranta wannan jarida ta Gaskiya
Ta Fi Kwabo bayani, sun ha]a da wa]anda aka rigaya aka kammala, yayin da wa]ansu
kuma ana nan ana yinsu a halin yanzu, da suka ha]a da hanyar Kudan zuwa [ankado
da wadda ta tashi daga Kudan zuwa {auran Wali da Kudan zuwa Garu zuwa La~a ta ~ulla
{auran Wali duk domin a sau}a}a wa masu tafiya }asa da masu ababen hawa.
Daga cikin asibitocin da na ziyarta wa]anda ko dai aka gina ko kuma aka yi masu
kwaskwarima aka }awata su sun ha]a da na garin Kudan da na [andako da Za~i da
Ta~a da na Likoro da kuma wanda yake a garin Hun}uyi. Duk wa]annan asibitoci ana
ba su kyakkyawar kulawa don jin da]in al’ummar }aramar hukumar Kudan.
A bisa haka ne na sami damar tattaunawa da wasu jama’a da ke zaune a }aramar
hukumar don jin ta bakinsu a game da irin shugabancin shugaban }aramar hukumar,
Alhaji Abdullahi S. Ahmad, shin akwai da]i ko a’a?
Sun bayyana mini cewa tun da suka kasance a }aramar hukumar Kudan, ba su ta~a
ganin shugaban da ya yi masu aiki irin Ahmad Abdullahi ba. Sun bayyana cewa,
dalilin fa]in wannan magana kuwa shi ne, babbar sana’ar da mutanen garin Kudan
suke ta}ama da ita shi ne noma. Suka ce a daminar bana an raba takin zamani mai
yawa da ba a ta~a raba irinsa a lokacin baya ba, kuma manoma na ha}i}a aka bai
wa takin, ba ’yan kasuwa ko ’yan siyasa masu sayar wa a kasuwar bayan fage ba.
Haka abin yake a ~angaren samar da wutar lantarki a }aramar Hukumar Kudan, inda
babu wani gari da ke }ar}ashin }aramar hukumar da ba a wadata shi da wutar
lantarki ba.
Ko a kwanaki sai da shugaban }aramar hukumar Kudan, Alhaji Abdullahi S. Ahmad,
ya gayyaci Gwamnan Jihar Kaduna, Mazayyani Muhammadu Namadi Sambo inda ya je }aramar
hukumar Kudan ya }addamar da bayar da bashi ga manoma. Ka ga a nan ma wani ci
gaba ne aka samu a }aramar hukumar.
Wa]annan ayyuka da ma wa]ansu da ba a kammala ba, fatarmu dai a nan ita ce Allah
Ya }ara ba shugaban }aramar hukumar Kudan, Alhaji Abdullahi S. Ahmad hikima da
basira da }wazo da tausayin talakawa na ci gaba da ayyukan alherin da ya soma.
Allah kuma Ya kare shi daga ma}iya da mahassada da ’yan hana ruwa gudu.
|