Arewa Na Tsaka Mai Wuya
KODAYAKE abu ne mai wuya ainun a sami hanya cikin sau}i wacce ta dace don neman ha]in kan Arewa a wannan mawuyacin lokaci, amma dai ba a makara ba idan mai karatu ya yi nazari a kan abin da zan zayyano. Duk mai tunani zai fahimci cewa, al’amura sun cu]e tun farkon hawan soja kan mulkin Nijeriya. Duk da yake sojoji sun ]inke ~arakar darewar Nijeriya daga 1967 zuwa 1970 kuma su ne dai suka shuka yiwuwar }ir}iro jihohin da muke da su a yanzu har 36, ka ga ba mu da ikon zarginsu bisa wasu daga illolin Nijeriya, sai dai tsara tafarkin siyasa shi ne illar da suka yi domin ba aikinsu ba ne, wannan aiki ne na farar hula wato ‘yan siyasa tsabagensu.
Ba za mu manta ba da cewa, a Nijeriya mai mulki komai lalacewarsa shi kawai ke da ikon yin abin da ya ga dama ba wai abin da jama’ar }asa ke so ba. Wannan halayya ta sama asali ne bisa shimfi]ar rayuwar mulkin soja. Gaskiya ta Allah abubuwa sun sukurkuce ne kususan a Arewa saboda har gobe talakan Arewa bai san komai ba illa ya bi mai mulki ko da kuwa babu wani amfani bisa tafiyar da mulkin.
Soja dai ba Arewa kawai ya mulka ba, duk Nijeriya ne wato kusurwowi hu]u kenan ko? Kusurwowi hu]un nan fa ba wai wata ta fi wata ba ne ta wauta ko kishiyarta, duk dai akwai rashin fahimta a ko’ina cikin Nijeriya.
Ga masu lura, a kan ce shugabannin soja duk daga Arewa suke, wannan idan an duba haka ne sai dai ai marigayi Aguiyi Ironsi ba ]an Arewa ba ne kuma ga shi, shi ne shugaban soji na farko a Nijeriya. Tafarkin da aka bi aka ham~arar da gwamnatin farar hula ta farko a wannan }asa a 1966, shi ne ummulhabi’isin ta~ar~arewar siyasa a Nijeriya kuma tun wancan lokaci Arewa ta girgiza kuma ha]in kanta ya sakwarkwace har ya zuwa yanzu.
Abin ba}in cikin ma shi ne hanyoyin kirki ba a ma tunaninsu balle a samo bakin zaren domin ]inke inda ake zaton ya yage. Wurin da yanzu babu daidaito kuma tsangwamar juna ya yi yawa wanda har ta kai ga an kasa gane santaleliyar hanyar gyara abubuwa, shin wannan abin takaicin da me ya yi kama? Manya wa]anda ake zaton za su iya kyautata ]inke ~arakar an yi biris da su domin ba su da ku]i saboda haka ba a ma tunanin tuntu~arsu bayan suna nan a raye! Wannan da ma wasu dalilai su ne suka hana ruwa gudu har goba.
An sami sabuwar shigar siyasa daga 1999 zuwa 2010, wa]anda suka sami kansu cikin mulki ban da girman kai da ganin sun tara dukiyar haramun ba sa tunanin komai sai kansu da ‘ya’yansu domin Arewa ko ta zauna lafiya ko a’a duk ba a gabansu take ba, illa kawai su yi mulki su }ara wa Borno dawaki!
Gaskiya ta Allah matu}ar wa]annan ‘yan jagaliya sun ci gaba da wannan halayya, samun ha]in kan Arewa sai yadda Allah Ya yi kawai, amma Hausawa kan ce abin da ya ci doma ba zai bar awai ba. Duk yadda ]an siyasa ya kai bai fi gundumar da ya fito ba. Saboda haka lalacewar Arewa lalacewar ‘yan siyasar Arewa ne gaba ]ayansu. Dole mu bi wa}ar Shata da yake cewa, “ashe mutane su ne kasuwa, ni ku raba ni da tarin rumfuna”.
Kodayaushe muna ta}ama da yawanmu amma akwai }arancin fahimtar juna domin son mulki kawai ba tare da gane juna ba. Duk masu son mulkin nan ba wai wani abu ba ne ke sa su yin haka illa mai}on arzi}in }asa da suke shara na jama’a. Da ba sa rigingine a kan dukiyar jama’a ba za ka sami ]aya bisa ukunsu ba a da’irar siyasar.
Yanzu dai abin ba}in ciki Arewa ta rasa wata ho~~asa ganin mulkin Nijeriya ba zai zo cikin gundumar Arewa ba tun lokacin da Allah Ya kar~i ran bawansa marigayi Alhaji Umaru Musa ’Yar’Aduwa Allah Ya ji}ansa. Marigayi ’Yar’Aduwa ya sha cara daga ‘yan Arewa abin kunya kuma ya bar su suna tagumi a yanzu da fatar Allah Ya ba shi Aljannar firdausi, amin.
Lokacin da wannan taliki ke mulki ya yi }o}ari }warai domin kyautata wa }asar nan gaba ]aya amma saboda kawai yana bu}atar ganin talaka ya sakata ya wala shi ma aka ]auki karan-tsana aka ]aura masa, to, ga irinta nan yanzu ya bar ma}iya da tagumi kuma tafiya ta tafi, ma}iyan Arewa sai tam~ele suke yi kuma sun cimma burinsu na raba kawunan ‘yan Arewa, ko rikicin Jos manuniya ce zahiran na wargaza Arewa! Saura da me inji Halilu Ahmed Getso sai kuma a sami hanyar warware wannan }ulli.
Dole ne ‘yan jabun siyasarmu wa]anda suka ]auki Obasanjo uwa-uba su saitu domin gane manufa. Allah Ya ganar da su, amin.
IBRAHIM ABDUL ZANGO, ne ya ruwaito daga Kano.
|