An Bai Wa Ma’aikata 640 Wa’adi
Su Fice Daga Gidajensu
MUHAMMAD SHAFI’U SALEH, Daga Yola
A YANZU haka dai kimanin ma’aikatan gwamnati 640 da ke zaune a rukunin gidaje na Adamawa Motel ne, al}alin kotun shari’ar gidaje a Yola, Mista Johnson Samuel ya ba su wa’adin kwanaki 21 domin su fice daga gidajen da suke zaune a ciki. A cewar mai shari’ar ma’aikatan suna zaune ba tare da }a’ida ba.
Wannan hukunci ya biyo bayan shigar da }ara da gwamnatin Jihar Adamawa ta yi a kotun.
Ita dai gwamnatin jihar ta gurfanar da ma’aikatan ne bayan ta ba su takardar garga]i, na cewa su fice daga gidajen tun da sun kasa biyan ku]a]en hayar gidajen, inda kuma ta dam}a gidajen ga wasu ma’aikatan domin su ci gaba da zama amma suka yi biris da takardar garga]in da ta basu, ganin haka ne ta kai su gaban kotun gidaje domin ]aukar matakin shari’a game da lamarin.
Da yake yanke hukunci, Al}alin kotun, Mai Shari’a Johnson Samuel, bayan sauraron wa]anda ake }arar, sai ya yanke hukuncin cewa, ya basu wa’adin kwanaki 21 su gaggauta ficewa daga gidajen, inda ya ce suna zaune ne ba bisa }a’ida ba, kafin cikar wa’adin, kuma masu zama a gidajen na halas su shiga ba tare da ~ata lokaci ba.
Tun da farko, gwamnatin jihar ta da]e tana }o}arin ganin mazauna gidajen sun fita ba tare da an kai ruwa rana ba, domin wa]anda ta bai wa gidajen su shiga, amma suka }e}asa }asa suka ce su ma ai ma’aikatan gwamnati ne, wanda kuma gwamnati ne ta basu wuraren su zauna, amma ba su zauna ne a ra’ayin kansu ba.
Da yawa daga cikin mazauna rukunin gidajen da wakilinmu ya tattauna da su, sun bayyana cewa, suna zaune ne a rukunin gidajen don ba su da wani wurin zaman. Suka ce kuma a baya suna biyan ku]a]en hayar gidajen, amma da yawansu sun tsayar da biyan ne bayan sun yi ritaya daga ciki, wanda hakan ya sa suka kasa biyan ku]a]en, wanda a baya gwamnati ta ce ta yafe masu, amma yanzu kuma an ce su biya ko kuma su bar gidajen, to, ba su san ko yaya za su yi ba.
Malam Muhammad Haruna wanda makaho ne, ya ce yana zaune a wurin ne bisa lalura, wanda kuma ya kashe sama da shekaru 50 a wurin, a yanzu }arfi ya }are, kuma ba shi da komai. Yana cewa, “ba ni da ku]in biya balle kuma ku]in da zan biya haya a wani wajen daban, domin ku]a]en sallama na aiki har yanzu ba a biya ni ba”.
|