... Jarida Mai Ratsa Zukata

LABARAI

ALHAMIS 17 ZUWA LAHADI 20 GA FABRAIRU, 2011
14 ZUWA 17 GA RABIUL AWWAL, 1432 BAYAN HIJIRA


Al’ummar Kura Suna Zaune Da {abilu
Lafiya — Tafidan Kano

JABIRU A. HASSAN, Daga Kano

HAKIMIN Kura, kuma Tafidan Kano, Alhaji Tijjani Abubakar ya ce ana zaune lafiya tsakanin al’ummar ta Kura da dukkan }abilun da suke wannan yanki, wanda hakan ce ma ta sanya ake samun }aruwar arzi}i da mutunta juna a fa]in }aramar.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Tafidan na Kano, lokacin da yake gabatar da na]in Sarkin Yarbawan Kura, Malam Aminu Sadi}u Ojuronje a fadarsa, inda ya }ara da cewa, duk wanda ya san yadda }aramar hukumar Kura take zai amince, cewa akwai zaman lafiya tsakanin ]aukacin al’ummar yankin da dukkan }abilun da ke zaune a }aramar hukumar.
Sannan ya sanar da cewa, Jihar Kano jiha ce wadda Allah ya sanya take zaune da kowace }abila ta }asar nan, kana jiha ce wadda take }aunar kowace }abila don zaman tare kamar yadda masarautar Kano ta kasance mai bu}atar zaman lafiya da }aunar juna.
Haka kuma Tafidan na Kano, Alhaji Tijjani Abubakar ya ce fadar hakimin Kura ta na]a sarkin na Yarabawa ne domin }ara kyautata ala}a tsakanin }abilar Yarabawan da al’ummar }aramar hukumar ta Kura ta yadda al’amura za su da]a ingantuwa na zaman tare.
Daga nan, sai ya hori Sarkin na Yarabawa, Malam Aminu Sadi}u Ojuronje da ya kasance jagora mai adalci da }o}arin ha]e kan al’umma domin a ci gaba da gudanar da rayuwa mai cike da mutunta juna a kodayaushe.
A }arshe, Alhaji Tijjani Abubakar, Tafidan Kano, ya taya sabon sarkin murna tare da fatar wannan na]i da aka yi masa zai zamo wani }alubale a gareshi na kyautata al’amura a }aramar hukumar Kura.
Da yake jawabin amincewa da na]in nasa, Sarkin Yarabawan Kura, Malam Aminu Sadi}u Ojuronje, wanda ya fito daga Ilesa ta Jihar Osun, ya nuna jin da]insa bisa yadda Hakimin na Kura, kuma Tafidan Kano, Alhaji Tijjani Abubakar ke gudanar da jagorancin al’ummarsa bisa adalci da sanin ya kamata.
Sannan ya tabbatar wa da Hakimin cewa, zai yi aiki da gaskiya wajen kawo ci gaban al’ummar wannan yanki tare da mutunta sauran al’ummar da suke zaune a kowane sa}o na }aramar hukumar ta Kura cikin yardar Allah.
A }arshe, Malam Aminu Sarkin Yarabawa ya gode wa dukkan mutanen }aramar hukumar Kura saboda halartar bikin na]insa da aka yi tare da fatar Allah ya ba shi ikon gudanar da shugabanci mai nagarta.

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmaster: Emmanuel Bello