>
 

 

 

... Jarida Mai Ratsa Zukata

Gida  Labarai  Ra'ayi  Shafukan Musamman  Tattaunawa  Dandali  Tsokaci  Kudin Talla   Gamu Da Mu   A Tuntube Mu

LABARAN CIKIN GIDA

 

Litinin 30 zuwa Laraba 2 ga Yuli, 2008

 

 

 

Dubun Masu Safarar Miyagun {wayoyi Ta Cika A Saudiyya

WASU ~ata-gari da suka yi nufin fasa }waurin miyagun }wayoyi daga wasu }asashen ma}wabta da ke makwabtaka da }asar Saudiyya sun fa]a hannun hukuma sakamakon kama wasu dabbobi da gwamnatin }asar ta yi suna sha}e da miyagun }wayoyi a cikin cikunansu.
Wakilinmu ya zanta da wani ]an jarida, wakilin Jaridar Almadina wadda ake bugawa a birnin Jeddah, Malam Rabe Sulaiman, wanda ya kasance cikin taron manema labaru da suka ga wa]annan dabbobi a lokacin da jami’an tsaron }asar Saudiyya suka nuna su ga ‘yan jaridu a birnin Makka.
Muhammad Rabe ya ce a halin da ake ciki, jami’an tsaron sun kama wa]annan dabbobi ne a lokacin da dubun wa]annan mutane ta cika. Ya ce sun shigo da dabbobin daga }asashen waje amma wasu daga cikinsu an fe]e cikunansu kuma aka cika su taf da miyagun }wayoyi da suka kai kilogiram sama da ]ari biyu kuma da sun wuce da su, to, za su }ara taimakawa wajen lalata tarbiyyar Larabawan Saudiyya kuma su sami ma}udan ku]a]en Saudiyya na Riyal.
Ya zuwa wannan lokaci, gwamnatin }asar Saudiyya ta ]auki tsauraran matakai na gwada dukkan dabbobin da za a shigo da su zuwa cikin }asar wajen ganin an caje su sosai saboda yadda a kullum masa fasa-}waurin miyagun }wayoyi ke sauya salon aika-aikar da suke yi ta yadda idan an toshe wannan kafa sai su fito da wata kafa.
Duk da irin kashedin da gwamnatin }asar Saudiyya ke yi kafin ta bayar da izinin shiga cikin }asar wato Visa, takan rubuta cewa, duk wanda aka kama da laifin safarar miyagun }wayoyi zuwa cikin }asar, to, hukuncin kisa ne ke kansa.
Kuma ana samun wasu da ke aikata wa]annan miyagun ayyuka kuma ana zartar musu da hukuncin kisa a duk lokacin da aka kama su bayan an gurfanar da su gaban kotu.
Dabbobi musamman a wannan lokaci sun kasance wata sabuwar hanyar fasa kwaurin miyagun }wayoyi zuwa cikin }asar Saudiyya kafin lokacin da dubu ta cika kuma aka kama wa]annan awakai masu tarin yawa shake da miyagun }wayoyi.

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmasters: Emmanuel C. Bello & Suleiman A. Adamu