|
Jami’an NDLEA Sun Kamo Tsoho [an Shekara 80
AMINU BALARABE, Daga Gusau
Hukumar hana sha da fataucin miyagun }wayoyi (NDLEA) reshen
Jihar Zamfara ta gabatar da wasu da take tuhuma da tu’ammali da miyagun }wayoyi
a ofishinta da ke Gusau.
Daga cikin wa]anda ake tuhumar har da wani tsoho mai kimanin shekaru tamani (80)
mai suna Garba Maigemu Sabon Garin Gusau wanda ake zargin ya shahara da zama
kuncin mashaya.
Garba Maigemu da aka kama yana tare da wani saurayi mai suna Yakubu [an-Mutuwa
mai shekara 24.
Ana zargin saurayin yana ha]a baki da tsohon a wajen gudanar da mummunar
sana’arsu.
Kwamandan rundunar hana sha da fataucin miyagun }wayoyi a jihar, Alhaji Ibrahim
Muhamamd Dodo, ya ce tuni ma’aikatansa suka kama wa]anda ake tuhumar a wani
samame da suka kai a wurin da suke gudanar da sana’ar su ta miyagun }wayoyi.
Ya gabatar wa ‘yan jarida da wa]anda ake tuhumar a wani ~angare na bikin ranar
ya}i da miyagun }wayoyi ta Majalisar [inkin Duniya wanda aka yi a ofishin
hukumar a Gusau, cibiyar Jihar Zamfara.
Alhaji Ibrahim Muhammad Dodo ya ce rundunarsa a shirye take ta ya}i ]abi’un sha
da fataucin miyagun }wayoyi a wannan jihar. Ya }ara da cewa, a shekarar da ta
gabata sun sami nasarar }wace miyagun }wayoyi da dama daga masu tu’amali dasu.
Ya ce a wannan shekara sun kama ganyen tabar wiwi da nauyinta ya haura kilogirrm
]ari uku da wasu kayan sa maye wadanda nauyinsu ya haura kilogiram ]ari hu]u.
|