>
 

 

 

... Jarida Mai Ratsa Zukata

Gida  Labarai  Ra'ayi  Shafukan Musamman  Tattaunawa  Dandali  Tsokaci  Kudin Talla   Gamu Da Mu   A Tuntube Mu

LABARAN CIKIN GIDA

 

Alhamis 7 zuwa Lahadi 10 ga Agusta, 2008

 

 

 

Za A Dasa Itatuwa Miliyan 1 A Jihar Katsina

ABDULLAHI MOHAMMED, Daga Katsina
GWAMNATIN Jihar Katsina za ta dasa itatuwa da yawansu ya kai miliyan ]aya a fa]in jihar.
Gwamna Ibrahim Shehu Shema ne ya sanar da haka a wajen bikin dasa itatuwa na wannan shekara da aka gudanar a garin Dankama ta }aramar hukumar Kaita.
A wajen bikin sai da aka dasa itatuwan da yawansu ya kai dubu bakwai.
Gwamnan ya ce a cikin mako guda za a shuka duk itatuwan da aka tanada domin shirin ba domin komai ba saboda ana lokacin damina.
Haka kuma Alhaji Shema ya ce kowane hakimi a fa]in jihar za a ba shi iri guda dubu sai makarantun firamare su za a ba kowace guda ]ari biyu domin dasawa a yankinsu.
Ya umarci cewa, za a tanadi kadada shida a wuraren da jihar ta yi iyaka da }asar Nijar domin dasa itatuwan.
Gwamnan ya ce ana sa ran nan da shekara uku masu zuwa za a dasa itatuwan da yawansu ya kai miliyan bakwai zuwa miliyan goma. Ya ce za su taimaka wajen rage kwararowar hamada da zaizayar }asa.
Ya umarci kwamishinan ilimi da mai ba gwamna shawara a kan ilimi mai zurfi da su tabbatar irin da ake dasawa a makarantu, an rene su har su girma.
Ya yi garga]in cewa, shi da kansa zai ri}a zagayawa lungu-lungu na fa]in jihar domin ya tabbatar da ana aiki da umarninsa.
Tun da farko kwamishinan aikin gona, Alhaji Abdul’Aziz Muhammad, ya ce, ]umamar yanayi da zaizayar }asa da kwararowar hamada sun zame wa shugabanni abin damuwa.
Ya ce a kowace shekara ana dasa itatuwa da tsawonsu ya kai kilomita ashirin a fa]in jihar domin a taka wa kwararowar hamada birki.
A }arshe, Gwamna Shema ya yi kira ga jama’a da su ha]a hannu da gwamnatin domin ya}i da zaizayar }asa da kwararowar hamada.

 

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmasters: Emmanuel C. Bello & Suleiman A. Adamu