>
 

 

 

... Jarida Mai Ratsa Zukata

Gida  Labarai  Ra'ayi  Shafukan Musamman  Tattaunawa  Dandali  Tsokaci  Kudin Talla   Gamu Da Mu   A Tuntube Mu

LABARAN CIKIN GIDA

 

Alhamis 16 zuwa Lahadi 19  ga Oktoba, 2008

 

 


 

 

Mataimakiyar Gwamnan Filato Ta {addamar Da Kwamitin Bun}asa Ilimi

ISA AHMED, Daga Jos
MATAIMAKIYAR gwamnan Jihar Filato kuma kwamishiniyar ilimi ta jihar, Misis Pauline Tallen, ta }addamar da wani babban kwamiti na mutum 28 da zai bayar da shawarwari a kan hanyoyin da za a bun}asa ilimi a jihar a gidan gwamnatin jihar da ke Jos, babban birnin jihar.
Da take jawabi a lokacin }addamar da kwamitin, mataimakiyar gwamnan ta bayyana cewa, duk da ma}udan ku]a]en da gwamnatin jihar ke kashewa a kan harkokin ilimi a jihar har yanzu akwai }arancin gine-gine da kayayyakin aiki a makarantun jihar da a sakamakon haka ilimi ke yin baya a jihar.
Misis Pauline Tallen ta bu}aci kwamitin a kan ya samar da nagartattun shawarwarin da za su taimaka wajen bun}asa ilimi a jihar. Ta ce babu shakka gwamnatin jihar ta tashi tsaye wajen ganin ta bun}asa ilimi a jihar. Kuma ta ]eba wa kwamitin wa’adin shekara ]aya ya mi}a rahotonsa.
Da yake jawabi a madadin ’yan kwamitin, shugaban kwamitin, Mista Mataimaki Tom Maiyashi, ya yaba wa gwamnatin Jihar Filato a kan kafa wannan kwamiti. Ya bayar da tabbacin cewa, kwamitin zai yi iyakar }o}arinsa wajen ganin ya sauke wannan babban nauyi da aka ]ora masa.
Wannan kwamiti mai mambobi 28 ya }unshi masu ruwa da tsaki a kan harkokin ilimi na ~angaren gwamnati da masu zaman kansu. Mista Mataimaki Tom Maiyashi ne yake shugabancinsa a yayin da daraktan bincike da tsare-tsare na ma’aikatar ilimi ta Jihar Filato, Mista Laurance Ba}o, ne sakatarensa.

 

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmasters: Emmanuel C. Bello & Suleiman A. Adamu