>

 

... Jarida Mai Ratsa Zukata

Gida  Labarai  Ra'ayi  Shafukan Musamman  Tattaunawa  Dandali  Tsokaci  Kudin Talla   Gamu Da Mu   A Tuntube Mu

LABARAN CIKIN GIDA

 

Alhamis 17 zuwa Lahadi 20 ga Yuli 2008
 

 
 

Hukumar Tsaro Za Ta Inganta Harkokinta A Jihar Zamfara — Manjo Lawal Bala

AMINU BALARABE, Daga Zamfara
HUKUMAR tsaro ta }asa ta Jihar Zamfara, wadda Manjo Lawal Bala (ritaya) ke shugabanta, ta yi }udurin ~ullo da wasu ofisoshin ‘yan sanda da wasu }ungiyoyi na tabbatar da tsaro a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Mai bada shawara na musamman ga Gwamnan Jihar Zamfara kan harkokin tsaron }asa, Manjo Lawal Bala Gusau (ritaya), kuma Shettiman Gusau, ne ya furta haka a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi kan ayyukan hukumarsa a ofishinsa da ke fadar Gwamnatin Jihar Zamfara a Gusau.
Manjo Lawal Bala ya ce yin haka shi ne manufar }ara inganta sha’anin tsaro a garin Gusau da ma yankunan }ananan hukumomin jihar.
A cewar mai ba da shawarar, gwamnatin Alhaji Mahmuda Aliyu Shinkafi (Dallatun Zamfara), ta yi wannan hangen nesa ne a bisa la’akari da muhimmancin tsaro a cikin al’umma.
Daga nan sai ya shawarci ]aukacin jama’ar Jihar Zamfara da su bayar da tasu gudunmawa domin samun nasarar tabbataccen tsaro a Gusau da Kewaye.
Ya }ara da cewa, tun daga lokacin da wannan gwamnati ta hau karagar mulki, ta samar da kayayyakin aiki ga ‘yan sanda da kuma }ungiyoyin tsaro da ke fa]in jihar.
Manjo Lawal Bala (ritaya) ya ce a kwanan nan ma gwamnatin Alhaji Mahmuda Aliyu Shinkafi ta raba wasu motoci guda 54 ga ‘yan sanda da wa]ansu }ungiyoyin tsaro da ke cikin Jihar Zamfara, domin cimma manufarta na ganin sun shiga cikin lunguna da sa}o domin ya}ar miyagun ~ata-gari a cikin jihar.
Haka kuma, gwamnatin Alhaji Aliyu Shinkafi ta gina wa]ansu gidaje wa]anda aka raba su ga ‘yan sandan kwantar da tarzoma da kuma wa]ansu jami’an ‘yan sanda da ke Gusau, babban birnin jihar.
Har ila yau, gwamnatin ta gina hedikwatar rundunar ‘yan sanda da ke jihar. Ya ci gaba da bayyana wa manema labarai cewa, gwamnati za ta }ara gina wasu ofisoshi na ‘yan sanda da masu aikin tsaro a wasu unguwanni a Gusau, har ma an ba da kwangilar aikin.
A cewarsa, hukumar ta Hisbah ta jihar tana tare da ofishinsa na tsaro, domin kuwa, duk wa]ansu bu}atu na hukumar Hisbah ga gwamnati, suna zuwa ne gare shi. Sannan ya kai wa gwamnati domin biyan bu}ata, haka kuma, kwamitin nan na sasanta Fulani da manoma, shi ma yana }ar}ashin ikonsa ne.
A }arshe, sai ya bu}ace su da su ]ore da namijin }o}arin da suke yi da manufar tabbatar da cikakken tsaro a ko’ina cikin fa]in Jihar Zamfara. Da aka yi masa wata tambaya, dangane da rikicin siyasa da ya kunno kai, tsakanin magoya bayan Gwamna Mahmuda Aliyu Shinkafi da magoya bayan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani, Yariman Bakura, Manjo Lawal Bala, ya ce shi kan baya da masaniya hakan.

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmasters: Emmanuel C. Bello & Suleiman A. Adamu