>
 

 

 

... Jarida Mai Ratsa Zukata

Gida  Labarai  Ra'ayi  Shafukan Musamman  Tattaunawa  Dandali  Tsokaci  Kudin Talla   Gamu Da Mu   A Tuntube Mu

LABARAN CIKIN GIDA

 

Litinin 8  zuwa Laraba 10  ga Satumba, 2008

 

An Bu}aci Kawu Yakasai Ya Ja Kunnen Mataimakinsa

TIJJANI LASISI, Daga Soba
AN bu}aci shugaban }aramar hukumar Soba, Alhaji Kawu Ibrahim Yakasai da ya ja wa mataimakinsa, Alhaji Munka’ila Hari, kunne saboda halin ko-in-kula da yake nunawa a tsakaninsa da jama’a.
Abubakar Shehu Mai Masara da Bello Isa Bakanike, dukkansu mazauna garin Soba, ne suka bu}aci haka a zantawarsu da wakilinmu.
Sun ci gaba da cewa, kowa ya san Alhaji Munka’ila Hari mutumin kirki ne amma tun da ya sami mu}amin mataimakin shugaban }aramar hukumar Soba ya canza hali.
Suka ce bayan Honorabul Kawu Yakasai ya ]auki Alhaji Munka’ila Hari a matsayin mataimakinsa, Allah Ya bada sa’ar cin za~e, ganin haka, inji su, sai Munka’ila ya canza daga halin da aka sani shi da shi a da.
Bello Isa da Abubakar Shehu suka ce wata bakwai ke nan da kasancewar Munka’ila Hari a matsayin mataimakin shugaban }aramar hukumar Soba amma duk ranar Asabar da Lahadi da }arfe shida na safe suka yi zargin yake fita gidansa zuwa Zariya ya ma}ale a wani wuri ya }arasa barci, in kuwa ranakun aiki ne jama’a ba sa ganin sa.
Sun ci gaba da cewa, saboda canza halayensa na kirki da ya yi suna tunanin cewa, zai shafa wa Honorabul Kawu ba}in fenti tun da shi mutumin kirki ne, mai sauraron jama’a da taimaka musu. Suna masu cewa, dole ne mataimakinsa ya canza hali.
 

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.