|
|
|
Gasar KADA 2008:Jihar Kaduna Ta Shirya Wa
’Yan Wasa Sansani Mai Kyau
GWAMNATIN Jihar Kaduna tana shirin sama wa ’yan wasan da za
su halarci wajen gasar wasanni ta }asa karo na 16 wuraren kwana masu kyau a
wasannin da za a yi a Kaduna a cikin watan Nuwamba, 2008 wato (NSF).
Kwamishinan matasa da wasanni na Jihar Kaduna, Alhaji Shehu Adamu ya fa]a wa
wakilin Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) haka a ranar Alhamis a Kaduna, inda ya
ce ’yan wasa maza da mata za su sami wuraren kwana masu kyau da kuma duk
abubuwan da ya kamata su samu a sansanin da za a ajiye su wato “Games Village”.
Ya kamata ’yan Nijeriya su sanya a ransu cewa za su sami wuraren kwana masu kyau
daga garemu, saboda muna da su, inji shi.
Adamu ya ce wuraren kwanan da aka ware wa ’yan wasan zai ]auki kusan ’yan wasa
12,000 kuma akwai dukkan kayayyakin da ya kamata a sanya a wurin an riga an
sanya su.
An shirya za a sanya ofishin ’yan sanda da cibiyar kula da lafiyar ’yan wasa da
ofishin ’yan kwana-kwana wato masu kashe gobara da ofishin da za a sanya yanar
gizo da Banki da zauren wasanni da kuma wuraren da ’yan wasa za su ri}a
sha}atawa.
Har ila yau, akwai tankin ruwa da za a sanya da janareton mai }arfin 1019KVA
wanda zai ri}a taimakawa ana samun ruwan sha ba tare da an sami }arancinsa da
wutar lantarki, inji Kwamishinan.
Haka kuma Kwamishinan wasannin ya tabbatar cewa, dukkan kayayykin girki, za a
kawo a sansanin ’yan wasan.
Sansanin da aka ware wa ’yan wasan yana da kyau saboda akwai fili sosai kuma
akwai iska mai kyau da take horawa wadda za ta taimakawa ’yan wasan da suke
kusan su 12,000 wajen sha}ar iska mai kyau kuma an kusa kammala dukkan ayyukan.
Haka kuma Adamu ya yi bayani a kan wuraren yin bayan gida, ya ce su ma za a
gyara su.
Ya ce gasar wasanni ta }asa karo na 16 za ta zama zakaran gwajin dafi a tarihin
gasar wato za a yi wasannin da ba a ta~a yin irinsu ba a Nijeriya.
Ya bayar da misali na cewa, sakamakon wasannin da aka yi za a bayar da shi ta
hanyar yanar gizo, wanda hakan ba a ta~a yin irinsa a tarihin Nijeriya ba a
gasar wasanni ta }asa tun da aka fara a shekarar 1973.
Mun shirya abin da muke so, ’yan Nijeriya su saurare mu su ga irin kyautatawar
shirin da muka yi na shirya gasa mai }ayatarwa wadda ba a ta~a yin irinta a
Nijeriya ba, Adamu ya bayar da tabbacin hakan.
Za a gudanar da gasar “Kada 2008” daga ranar 15 zuwa 29 ga Nuwamba a Kaduna inda
ake sa ran zaratan ’yan wasan Nijeriya za su ha]u a Kaduna.
|