>
 

 

 

... Jarida Mai Ratsa Zukata

Gida  Labarai  Ra'ayi  Shafukan Musamman  Tattaunawa  Dandali  Tsokaci  Kudin Talla   Gamu Da Mu   A Tuntube Mu

 

Litinin 8  zuwa Laraba 10  ga Satumba, 2008

 

 

Kakar Wasanni Ta Bana:-Enugu Rangers Ta Yi Shiri Sosai

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
A {O{ARINTA na ganin ta taka muhimmiyar rawa a gasar wasanni na Premier a kakar wasanni ta bana wadda bai fi kwanaki a fara ba, }ungiyar wasan }wallon }afa ta Enugu Rangers da ke garin Enugu ta sami zaratan ’yan wasa da za ta kara da kowace }ungiya a fa]in }asar nan ba tare da wata shakku ba a kakar wasanni shi ya sanya }ungiyar ta sami ’yan wasa da take ji da su wa]anda za su iya fitar da ita kunya har guda talatin da shida daga }ungiyoyin }wallon }afa na }asar nan daban-daban.
Jami’in hul]a da ’yan jarida, Mista Foster Chime, ne ya fa]a wa ’yan jarida haka. Ya ce }ungiyar tana da ’yan wasa 22 ne yayin da 14 daga cikinsu sababbi ne aka sayo daga wasu }ungiyoyi.
{ungiyar wasan }wallon }afa ta Enugu Rangers ta yi fama da matsaloli na ku]i a kakar wasanni ta bara amma yanzu }ungiyar ta yun}uro domin fitar da kanta daga kunya shi ya sa ma suka koma garin Abalakiki suka yi sansani suna horar da ’yan wasansu, ya zuwa rubuta wannan labari, }ungiyar ta yi wasannin sada zumunta da }ungiyoyin }wallon }afa ma}wabta domin gwada }arfinta, kuma ga alama ha}a tana neman cimma ruwa.


 

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmasters: Emmanuel C. Bello & Suleiman A. Adamu