|
|
|
Za Mu Ci Gaba Da {o}ari A Kakar Wasanni Ta
Bana
–Mai Horar Da Gombe United
MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
OLADUNMI Oyekale mai horar da }ungiyar wasan }wallon }afa ta Gombe United, ya
fa]i a Kalaba cewa }ungiyarsa za ta ci gaba da yin }o}ari a kakar wasa ta bana
domin ta bai wa mara]a kunya, kuma ta kia ga cimma buri na lashe duk wasu kofuna
a wannan kakar wasa ta bana. Oyekale ya fa]i haka a Kalaba yayin amsa tambayoyin
wakilinmu.
Bugu da }ari, domin cimma burin gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu [anjuma
Goje, yana yin iyakacin }o}arinsa a kan }ungiyar don babu abin da za su ce masa
sai dai “Allah Ya saka masa da alheri”.
Daga nan sai ya bayyana cewa, fatarsu a wannan shekara su ga sun lashe kofin
Premier da na FA.
A wata sabuwa Kodinetan }ungiyar Gombe United, Malam Farouk Yarma, ya bu}aci
hukumar tarayyar }wallon }afa ta Nijeriya wato NFF da NFL su sama wa al}alan
wasa isasshiyar kariya ta jami’an tsaro da za su ri}a rakosu daga cikin fili
zuwa waje a yayin da aka tashi daga wasa.
Malam Yarma ya }ara da cewa, yin haka ne ka]ai zai sanya al}alin wasa ya sami
natsuwa, ya gudanar da aikinsa ba tare da wata fargaba ba, musamman ma su
al}alan wasan, suna aiki ne da doka da kuma }a’ida ta aikinsu don haka wajibi ne
hukumomin biyu su samar masu da ingantacciyar kula ganin cewa, duk iyakacin }o}arin
da al}alin wasa ya yi dole wa]anda ba su yi nasara ba a wasa magoya bayansu su
ce za su far wa al}alin wasa.
A }arshe, ya yi fatar hukumomin da ke da ruwa da tsaki a harkar za su samar da
cikakkun jami’an tsaro saboda kare lafiyar al}alan wasan.
|