|
|
|
Za A Dawo Da Gasar Cin Kofin “WAFU”
A {ARSHEN watan Nuwamba 2008 ne aka bayar da sanarwar cewa, za a dawo da gasar
cin kofin }wallon }afa na }asashen Afirka ta Yamma wato (WAFU-Cup).
Shugaban hukumar shirya wasan }wallon }afa na Afirka ta Yamma, Dokta Amos Adamu,
ya fa]i haka. Ya ce }asashe 12 daga Afirka ta Yamma za su shiga gasar na matasa
wanda aka shirya za a fara daga 30 ga watan Nuwamba zuwa 14 ga Disamba, 2008.
Tun a shekarar 2004 ne aka daina yin gasar cin kofin “WAFU” saboda siyasa ta
shiga cikin al’amarin.
Amma tun da Adamu ya kar~i shugabancin hukumar ta WAFU a watan Afrilu, ya
tabbatar cewa, za a gudanar da gasar kuma zai }ayatar inda zai jawo ra’ayoyin
wasu mutane da dama.
Dokta Adamu wanda mamba ne a kwamitin zartarwa na hukumar }afa ta duniya “FIFA”
da kuma hukumar shirya wasan }wallon }afa ta Afirka “CAF” ya fa]i a gidan
Rediyon “BBC” cewa, wannan shi ne farko a cikin abubuwa masu kyau da za a
gudanar.
“Matasa da ke shiyyar Afirka ta Yamma suna bu}atar ci gaba, kuma hakan muke
bu}ata mu yi masu”.
“A da yara matasa daga shiyyar Afirka ta Yamma su ne suka mamaye nahiyar Afirka
a gasar wasan }wallon }afa a Afirka saboda haka muna so mu ci gaba da hakan.
“Gasa ta gaba da za a shirya ita ce ta manya, a shiyyar amma yanzu muna son mu
fara da na yara matasa domin a dawo da martabar gasar cin kofin “WAFU”.
Za a yi gasar ce a Jihar Delta da ke Kudancin Nijeriya.
{ungiyar }wallon }afa ta ’yan }asa da shekara 20 ta Nijeriya wadda za ta kar~i
ba}uncin gasar, za ta fafata ne da }asashen Kwaddebuwa da Ghana da Togo da
Gambiya da Jamhuriyyar Benin da Nijar da Saliyo da Gini da Laberiya da Senegal
da Cape Verde.
Rikicin shugabanci da aka samu tsakanin Adamu da ]an }asar Kwaddebuwa, Jacques
Anouma, shi ya kawo wa hukumar cikas.
Amma daga baya hukumar }wallon }afa ta Afirka “CAF” ta sasanta su kuma ta ba
Adamu umarnin ya kar~i shugaban hukumar “WAFU” daga hannun Anouma a matsayin
shugaban hukumar wanda aka yi hakan a farkon wannan shekara.
|