>
 

 

 

... Jarida Mai Ratsa Zukata

Gida  Labarai  Ra'ayi  Shafukan Musamman  Tattaunawa  Dandali  Tsokaci  Kudin Talla   Gamu Da Mu   A Tuntube Mu

 

Alhamis 4 zuwa Lahadi 7 ga Satumba, 2008

 

An Tashi Wasan Uni-Rovers Da Bagobiri 1 Da 1

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
DUK da kasancewa an tashi kunnen doki a wasan sada zumunta da aka yi a ranar Lahadi tsakanin }ungiyar wasan }wallon }afa ta UNI-Rovers wato tsohuwar }ungiyar Kalaba Rovers da takwararta ta Bagobiri FC wadda ke yin wasa a rukunin ’yan dagaji a filin wasa na U.J. Esuene da ke garin Kalaba, ya ce nasara ce babba gare su mai horar da ’yan wasan Bagobiri FC da ke Unguwar Hausawa a Kalaba. Mohammed Idris ne ya shaida wa wakilinmu haka jim ka]an da kammala wasan sada zumuntar.
Ya ci gaba da cewa wannan canjaras da muka yi da su hakan ya nuna matakin farko gare mu na shiga gasar cin kofin Gwamnan Kuros Riba wanda za a fara shi bada da]ewa ba. Da yake wasa samun sa’a ne mai horar da Bagobiri FC Idris, ya }ara da cewa, “’yan kallo da magoya bayanmu sun yi tsammanin za a lallasa mu da kamar ci 3 babu ko ]aya amma sai ga shi an tashi 1 da 1”.
Wakilinmu da ya kalli fafatawar tsakanin }ungiyoyin biyu ya aiko cewa, a daidai minti na talatin da shida ne UNI Rovers suka samu dukan daga kai sai mai tsaron gida. [an wasan }ungiyar Bobo Sim ne ya buga }wallon a dukan fanaritin.
Haka aka ci gaba da yin wasa UNI Rovers na neman }ari, Bagobiri na neman farkewa, a daidai minti na sittin da takwas, ]an wasan gaba na Bagobiri FC Wishdom Bassey, ya farke cin da aka yi wa }ungiyarsu bayan da ya samu sa’ar wuce masu tsaron baya na Uni-Rovers. Haka aka tashi wasan.
Wakilinmu ya tunatar cewa wannan shi ne wasan sada zumunta na farko tun kafa }ungiyar Uni-Cem Kalaba wata uku kenan yayin da }ungiyar Bagobiri FC ta samu ciyarwa gaba daga rukunin da take wasa. An yi wasan lami lafiya, an tashi kowane na mai cike da farin ciki.

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.