Global Stars Ba Ta Shakkar
Karawa Da Kowace {ungiya
MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
SHUGABAN }ungiyar Global Stars da ke garin Fatakwal ya bayyana cewa,
}ungiyarsa ba za ta yi shakkar kara wa da duk wata }ungiya.
Shugaban ya bayyana wa wakilinmu haka ne yayin da aka kammala wasan
da }ungiyar Iwu Stars da ke Owerri.
Global Stars da ke garin Fatakwal wadda ke yin wasa a rukunin ’yan
dagaji ce ta zama zakara a gasar wasan ’yan dagaji rukuni na hu]u.
Wasan da aka yi shi a filin wasa na U.J. Esuene da ke garin Kalaba.
Global ta lallasa takwararta ta Iwu Stars da ke garin Owerri da ci
3-0 yanzu }ungiyar Global ta sami matsa wa zuwa rukuni na uku
sakamakon nasarar da ta samu kan ’yar uwarta ta Iwu.
Bayan da aka tashi daga wasan wakilinmu ya ke~e shugaban }ungiyar
Mista Obi Ifeanyi wanda shi ma ya zo kallon wasan domin ya tofa
albarkacin bakinsa game da nasarar da }ungiyarsa ta samu sai ya ce
“na yi matu}ar farin ciki game da wannan nasara da Allah Ya ba mu,
kuma za mu ci gaba da }o}artawa a rukunin da muka shiga, shi ma mu
ga mun haye.”
“Haka nan kuma da sauran shirye-shirye na ganin ’yan wasan sun ci
gaba da }ulla abin arzi}i.
Mista Ifeanyi ya }ara da cewa, za su yi namijin }o}ari wajen
kyautata wa ’yan wasan da kuma ganin cewa suna ci gaba da samun
nasara a duk fafatawar da }ungiyar ta yi.
Bugu da }ari, ya ce ko kakar wasa ta gaba, ta ~ullo ba ya shakkar
kowace }ungiya da za }ungiyarsa za ta kara da su.