... Jarida Mai Ratsa Zukata

GidaLabaraiSiyasaSana'o'iTattaunawaTsokaciDandaliKiwon Lafia IlimiKudanciHudubaFadi Sonka{asan WajeGamu Da MuTuntu~e Mu

DANDALI

LITININ 16 ZUWA LARABA 18 GA AGUSTA, 2010
6 ZUWA 8 GA RAMADAN, 1431 BAYAN HIJIRA


 

Kaduna United Ta Lashe Kofin {alubale Karo Na Farko
— Ta Ci Enyimba 6-5 A Bugun Fanariti

A KARON farko tun bayan lokacin da aka ~ullo da gasar cin kofin }alubale ta }asa a shekarar 1954 wanda yanzu haka ake kira gasar cin kofin tarayya wato FA Cup, }ungiyar }wallon }afa ta Kaduna United ta lashe kofin a jiya, bayan ta fitar da takwararta ta Enyimba a filin wasa na Sani Abacha da ke garin Kano.
Kaduna United ta sami damar ]aukar kofin ne bayan an yi kare-jini-biri-jini inda aka share mintuna 120 a yayin da aka tashi wasan 3-3, lamarin da ya sanya aka je bugun daga kai sai mai tsaron gida inda Kaduna United ta ci 3-2.
Idan ba a manta ba dai Enyimba ce ke ri}e da kofin na FA wanda ta lashe a bara.
Yanzu dai Kaduna United za ta wakilci Nijeriya a gasar cin kofin Nahiyar Afirka wato Confederation Cup wanda za a fara a shekara mai zuwa.

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmaster: Emmanuel Bello