... Jarida Mai Ratsa Zukata

GidaLabaraiSiyasaSana'o'iTattaunawaTsokaciDandaliKiwon Lafia IlimiKudanciHudubaFadi Sonka{asan WajeGamu Da MuTuntu~e Mu

DANDALI

LITININ 16 ZUWA LARABA 18 GA AGUSTA, 2010
6 ZUWA 8 GA RAMADAN, 1431 BAYAN HIJIRA


 

Za~en Shugabannin Hukumar NFF:
Shiyyar Kudu Maso Gabas Sun
Za~i Ndubuoke Da Chukwu

MASU ruwa da tsaki kan harkar wasan }wallon }afa da ke shiyyar Kudu Maso Gabas sun amince tsohon shugaban }ungiyar marubuta labarin wasanni, Fan Ndubuoke da ya tsaya takarar neman shugaban hukumar }wallon }afa ta tarayyar Nijeriya (NFF) wanda za a yi ranar 21 ga wannan wata a Legas.
Haka kuma shiyyar ta amince tsohon kyaftin ]in }ungiyar }wallon }afa ta Super Eagles ta Nijeriya kuma wanda ya ta~a horar da ‘yan wasan Super Eagles, Christian Chukwu da Anyasi Agwu da su tsaya neman takardar wakilai a hukumar.
Kamar yadda muka sami labari cewa, an ba su damar su tsaya takarar ne bayan an yanke hukunci a wajen taron da aka yi a Owerri babban birnin Jihar Imo a ranar Labara da daddare har zuwa safiyar Alhamis.
Makamar labarin ya }ara da cewa, tsofaffi da sababbin shugabannin hukumar }wallon }afa na shiyyar sun halarci wajen taron tare da sakatarorinsu, kuma a wajen taron an }i amincewa da tsayawa takarar Obinna Ogba da Victor Umeh a matsayin mataimakan shugaban hukumar }wallon }afa ta tarayyar Nijeriya.
Shiyyar ta ce ba ta da sha’awar samun matsayin mataimakin shugaba saboda tana neman shugabancin hukumar }wallon }afa ta tarayyar Nijeriya ne.
Haka kuma shiyyar ta ba kodinetan shiyyar da ya tuntu~i sauran shiyyoyin da ke }asar nan domin neman goyon baya ga ‘yan takararsu.

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmaster: Emmanuel Bello