... Jarida Mai Ratsa Zukata

GidaLabaraiSiyasaSana'o'iTattaunawaTsokaciDandaliKiwon Lafia IlimiKudanciHudubaFadi Sonka{asan WajeGamu Da MuTuntu~e Mu

DANDALI

LITININ 16 ZUWA LARABA 18 GA AGUSTA, 2010
6 ZUWA 8 GA RAMADAN, 1431 BAYAN HIJIRA


 

“{wallon Beckham Ta Kare A Ingila”

MAI horar da ‘yan wasan }asar Ingila, Fabio Capello ya ce ba zai ]auki David Beckham domin buga wa tawagar }asar }wallo kuma ba.
Mai horar da ‘yan wasan ya ce yana son ya ri}a amfani da ‘yan wasan da shekarunsu ba su kai na David Beckham ba wanda yake da shekarun haihuwa 35.
An dai tambayi Capello shin ko Beckham na cikin tsare-tsaren shi nan gaba sai ya ce, “a’a ba zan }ara kiransa ba, David ]an wasa ne }wararre amma ina ganin muna bu}atar sababbin jini ne a tawagar }asar.”
Capello ya ce Beckham zai iya buga wa Ingila wasa guda a filin Wembley domin ya yi bankwana da ‘yan kallo.
Mai horar da ‘yan wasan }asar dai ya ce bai tattauna da Beckham game da makomarsa ba, amma ya ce idan ]an wasan ya sami isasshen lafiya zai yi amfani da shi a wasa guda.
Capello dai ya furta wa]annan kalaman ne bayan Ingila ta sami nasara kan }asar Hungary a wasan sada zumunta da suka buga a filin Wembley, a wasan da }asar ta buga na farko, bayan mummunar rawar da ta taka a gasar cin kofin duniya da aka kammala a }asar Afirka ta Kudu.
David Beckham bai sami buga }wallo a gasar cin kofin duniya a }asar Afirka ta Kudu saboda raunin da ya samu.
Theo Walcott da Adam Johnson ne suka buga a ~angaren da Beckham ke bugawa a hannun dama, kuma sun haskaka a wasan.
“Na ga matasa hu]u da suka burge ni,”in ji Capello a hirarsa da manema labarai. “Za mu ci gaba da amfani da matasa domin inganta tawagar }asar”.
Tsohon kyaftin ]in Ingila, Beckham ya bar Ingila ne ya koma }ungiyar Los Angeles Galaxy a Amurka a shekarar 2007, kuma ]an wasan ya buga wa Ingila }wallo sau 115.

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmaster: Emmanuel Bello