>
 

 

 

... Jarida Mai Ratsa Zukata

Gida  Labarai  Ra'ayi  Shafukan Musamman  Tattaunawa  Dandali  Tsokaci  Kudin Talla   Gamu Da Mu   A Tuntube Mu

GAMU DA MU

 

Alhamis 11 zuwa Lahadi 14  ga Janairu, 2007

Mutuwa Rigar Kowa

 


 

Daga:

MUHAMMAD ADAMU

Da SAFIYA JIBRIN

KAMAR yadda Hausawa kan ce, ba mutuwa akan yi wa kuka ba, sabo. Babu shakka, marigayi Ahmad S. Nuhu ya bar duniya a lokacin da tauraruwarsa ke }ara haskawa, ya kuma tafi ya bar mahaifiyarsa da matarsa da kuma ’yan uwansa ’yan wasan Hausa, kai har ma da ma’abota kallon fina-finan Hausa cikin alhini da kewarsa.

Masu iya magana kan ce, abin da mutum ya shuka shi yakan girba, kuma kowa ya yi da kyau, zai ga da kyau. Sau da yawa mutum kan yi kakkausar suka game da yadda akan shirya fina-finan Hausa da ma wasu ]abi’u na wasu daga cikin ’yan wasan, sai ga shi ta fannin marigayi Ahmed S. Nuhu, hakan ya sha bamban, saboda harkar fim da wasu ke kushewa har suna }o}arin kafirta wasu ’yan wasa saboda a cewarsu suna wuce gona da iri, ita ta fito da Ahmed S. Nuhu, ta kuma sa Nijeriya da ma wasu }asashen duniya suka san shi suke kuma sha’awar fina-finansa.

Shaidar da jama’a da dama ke yi wa marigayi Ahmed S. Nuhu, ita ce yadda yake mu’amala da kowa ba tare da wani munafunci ko rashin gaskiya ko cin amana ba. Ga shi kuma da haba-haba da jama’a, yana kuma daga cikin ’yan wasan Hausa da jama’a kan girmama saboda natsuwarsa da kamun kai.

Wannnan yabo da marigayin ya samu ya sanya jama’a da dama suna yi ta tururuwa don zuwa jana’izarsa, wanda hakan babbar shaidar alheri ce ga dukkan mamaci, ana kuma sa masa ran rahamar Ubangiji saboda kyawawan shaidun da ya samu daga jama’a.

Hakan ya yi nuni da cewa, ba wai a fina-finai ba, a’a, ko wace sana’a ta duniya za a iya samun na }warai da kuma bara-gurbi. Ga dai a dalilin fina-finan da marigayin ya yi, ya sa mutane da dama wa]anda ma ba su ta~a ganinsa ido da ido ba, balle wani abu ya shiga tsakaninsu, suke ta sa masa albarka suna kuma yi masa addu’ar Allah Ya sada sa da rahamarSa, wanda hakan shi ne burin kowane ]an adam bayan ya bar duniya.

Baya ga addu’ar da marigayin ya samu daga jama’a, babbar ita ce wacce mahaifiyarsa ta yi masa, inda ta yi masa kyakkyawar shaidar cewa, Ahmed ]a ne nagari wanda ke kauce wa duk abin da zai kawo ~acin ran iyayensa, ta kuma }ara da ro}on Allah Ya gafarta masa.

Babu ko shakka, kowane mai rai mamaci ne. Mutuwar Ahmed S. Nuhu kamar famin ciwo ne ga masu shirya fina-finan Hausa in aka yi la’akari da yadda a shekarun baya aka rasa wasu jiga-jigai a duniyar fina-finai kamar su Darakta Tijjani Ibrahim da ’yar wasa Balaraba Muhammad wacce ita ma ta rasu sakamakon ha]arin mota.

Marigayi Ahmed Sadiq Nuhu, wanda ]an asalin garin Jos ne, an haife shi a shekarar 1976. Ya yi makarantar firamare da ta sakandare a Jos. Ya kuma samu shaidar Difloma a ilimin kwamfuta.

Ya kuma shiga harkar fina-finan Hausa ne shekaru kusan goma da suka wuce wanda ]an uwansa kuma amininsa, wato Ali Nuhu, ya yi masa hanya.

Muna kuma iya cewa, ya shiga da }afar dama saboda ya yi fina-finai da dama wa]anda suka kar~u a wurin jama’a. Ya kuma samu lambobin yabo a dalilin wa]annan fina-finai.

Cikin fina-finansa na farko akwai kamar su Akasi da U}uba da Linzami da Wuta. Ya kuma yi wasu da dama wa]anda suka ha]a da Mujadala da Khusufi da Sansani da Yaye da Adali da kuma Fil’Azal.

Har ila yau, marigayi ya kasance jarumi a fina-finai kamar su Shahada da Zabari da {ugiya. Ba kuma zan manta da fim ]insa ba wanda ya yi tashe sosai a shekarar da ya fito, waton fim ]in Sarmadan, wanda a wannan fim ]in, jarumi, Ahmed S. Nuhu ya taka rawar gani sosai inda har ta kai ga ya mutu ya kuma dawo a fim ]in, amma sai ga shi ya yi mutuwar da ba a dawowa.

Babu shakka marigayi Ahmed ya bar tarihi a duniyar fina-finan Hausa, saboda yana ]aya daga cikin matasan da suka taimaka wajen ]aukaka darajar fina-finan Hausa a }asar nan da ma wasu }asashen duniya, kasancewarsa }wararren ]an wasa, ya kuma shirya fina-finai da dama, hakazalika Darakta ne, wato mai bada umarni a wasu fina-finan kamfanin FKD.

Fim ]in da marigayin ya yi na }arshe wanda bai kai ga fitowa kasuwa ba shi ne fim ]in furodusa Rufa’i Nasidi wanda Nasir S. Gwangwazo ya rubuta mai taken MUSHARAKA.

Marigayi Ahmed Sadiq Nuhu ya rasu ya bar mahaifiyarsa da kuma matarsa, Hafsat Shehu wacce ita ma tsohuwar ’yar wasan fim ]in Hausa ce.

Allah Ya ji}ansa Ya kuma gafarta masa, amin.

 
 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.