... Jarida Mai Ratsa Zukata

GidaLabaraiSiyasaSana'o'iTattaunawaTsokaciDandaliKiwon Lafia IlimiKudanciHudubaFadi Sonka{asan WajeGamu Da MuTuntu~e Mu

HATSIN-BARA

LITININ 16 ZUWA LARABA 18 GA AGUSTA, 2010
6 ZUWA 8 GA RAMADAN, 1431 BAYAN HIJIRA


 

Al’ummar Musulman Filato Sun Yi Allah Wadai Da Kalaman Kwamishinan Ya]a Labaran Jihar

ISAH AHMED, Daga Jos

MAJALISAR al’ummar Musulman Jihar Filato wadda ake kira Ulama/Elders Council ta yi Allah wadai da kalaman da kwamishinan ya]a labaran jihar, Mista Gregory Yenlong ya yi a wani taron manema labarai da ya kira a kan rikicin jam’iyyar PDP reshen jihar, a inda ya yi kirarin cewa, idan har kwamitin ri}on jam’iyyar PDP da uwar jam’iyyar ta }asa ta na]o wani shugaba ya ci gaba da gudanar da ayyukansa a jihar za a sami tashin hankali.
Majalisar al’ummar Musulman ta yi Allah wadai da furucin kwamishinan ne a wata wasi}a da ta rubuta wa babban kwamandan runduna ta uku ta sojan Nijeriya da ke Jos kuma shugaban rundunar tsaro da ke kula da garin Jos da kewaye, Manjo Janar Saleh Maina da kodinetan majalisar, Malam [anjuma Khalid da jami’an ya]a labaran majalisar, Alhaji Sani Mudi suka sanya wa hannu.
Al’ummar Musulman sun ci gaba da cewa, duk da babu ruwansu da siyasa kuma babu ruwansu da wannan rikici da jam’iyyar PDP ke fama da shi, amma a matsayinsu na shugabannin addini kuma shugabannin al’umma ya zama wajibi a garesu su fito su yi magana a kan duk wani abu da suka ga zai kawo tashin hankali. Don idan rikici ya taso kowane iri ne, zai iya komawa na addini.
Majalisar ta ce domin ganin an magance dukkan wani abu da zai kawo tashin hankali a jihar, musamman ganin irin }o}arin da jami’an tsaro ke yi na ganin an sami zaman lafiya a jihar, ya sanya suka fito suka yi magana kan wannan furuci da kwamishinan ya yi.
Har ila yau, al’ummar Musulman sun ce babu shakka wannan furuci da kwamishinan ya yi ya nuna cewa, gwamnatin Jihar Filato ba ta son a sami zaman lafiya a jihar. Don haka sun bu}aci kwamandan ya ]auki matakin da ya dace a kan wannan furuci da kwamishinan ya yi.
Hakazalika majalisar ta yi Allah wadai da furucin da gwamnan jihar, Jonah Jang ya yi a }auyen Mazah a lokacin da ya je don jajenta wa al’ummar }auyen kan harin da aka kai masu a kwanakin baya. Shi dai gwamnan a lokacin da ya je }auyen ya yi kira ga al’ummar jihar kan su yi hankali da ba}in da suke shigowa jihar.
Suka ce irin wa]annan furuci da gwamnan ke yi tare da kwamishinoninsa suna matu}ar barazana ga zaman lafiya a jihar musamman ga al’ummar Musulman jihar wa]anda a kullum su ne rikice-rikicen da gwamnatin jihar take ]aukar nauyi yake shafa.
Don haka suka yi kira ga jami’an tsaro da ke jihar su tabbatar sun dakatar da irin hare-haren da ake kai wa al’ummar Musulmi a Unguwar Rukuba da Dutse Uku da Tina Junction da Bauci Ring Road da Lamingo da hanyar asibitin koyarwa na Jami’ar Jos. Suka ce wa]annan unguwanni da ke cikin garin Jos sun zama wurare masu matu}ar ha]ari ga al’ummar Musulmi da matafiya wa]anda ba su san hawa ba su san sauka ba, sai a auka masu.

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmaster: Emmanuel Bello