|
An {ara Jaddada Muhimmancin
Amfani Da Gidan Sauro Ga Mata Masu Ciki
MUSA ISA, Daga Lafiya
GWAMNATIN Jihar Nasarawa ta sake jaddada }udurinta na bada magani
kyauta ga mata masu juna biyu a jihar.
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar, Alhaji Abubakar Sarki [ahiru, ne
ya bayyana haka a lokacin da yake raba gidan sauro mai magani ga
mata masu ciki a }auyen Nakere da ke }aramar hukumar Wamba ta Jihar
Nasarawa.
Alhaji Abubakar Sarki [ahiru ya ce, ma}asudin shirya shirin shi ne
don ci gaba da wayar da kai da kuma ilimantar da mata mazauna
karkara a kan yadda za su iya amfani da gidan sauro mai magani, don
rage yawan zazza~in cizon sauro da kuma mace-mace a tsakanin }ananan
yara.
Ya yi bayanin cewa, gidan sauro mai magani, yana iya taimakawa wajen
kawar da cutar maleriya da sauran cututtuka zuwa kashi 70 bisa ]ari,
tare da cewa akwai bu}atar a yi amfani da gidan sauron yadda ya
dace.
Kwamishinan wanda Daraktan kula da asibitocin karkara Alhaji
Mailafiya ya wakilta, ya ce, gwamnatin tana shirin zuba jari nan
gaba don shawo kan yawan cututtukan zazza~in cizon sauro da kuma
rage yawan mace-macen }ananan yara sakamakon maleriya.
Alhaji Abubakar Sarki [ahiru ya yaba wa }ungiyoyin bada agaji irin
su, UNICEF da COMPASS saboda goyon bayan da suke bayarwa tare kuma
da kula da lafiyar jama’a.
A nata jawabin, jami’ar kiwon lafiya ta UNICEF tana goyon bayan
shirin ne domin magance cututtuka masu kisan }anana yara a }asar nan.
Tun farko a jawabinta, Darakta kula da ma’aikata ta }aramar hukumar
Wamba, Misis Julis Ibrahim, ta yi kira ga kowa da kowa da ya ha]a
kai don ya}i da cutar maleriya, wadda ta ce, tana barazana ga
lafiyar jama’a.
Daga cikin muhimman abubuwan da aka yi a wajen taron sun ha]a da
yadda ake amfani da gidan sauro mai magani ga jama’a. |