... Jarida Mai Ratsa Zukata

GidaLabaraiSiyasaSana'o'iTattaunawaTsokaciDandaliKiwon Lafia IlimiKudanciHudubaFadi Sonka{asan WajeGamu Da MuTuntu~e Mu

ILIMI

LITININ 16 ZUWA LARABA 18 GA AGUSTA, 2010
6 ZUWA 8 GA RAMADAN, 1431 BAYAN HIJIRA


 

Za Mu Ci Gaba Da Ba Wa Yara Ingantaccen
Ilimi Ga Kawunansu —Hajiya Safiya

shugabar Makarantar “Baba Memorial Schools” Hajiya Safiya Mahmoud Baba Bici ta ce za su ci ga ba da baiwa yara ingantaccen ilimi ta yadda za su kasance masu amfani ga kawunansu da kuma }asa baki ]aya. Ta yi wannan albishir ne cikin hirarsu da wakilinmu, Jabiru A. Hassan Ga yadda kuma hirar ta kasance:
GTK: Hajiya menene dalilin kafa makarantar ki ta “Baba Memorial Schools” a wannan gari na Bici?.
Hajiya Safiya: Gaskiya na yi farin ciki da samun wannan dama bisa yardar Allah (SWT) ta zantawa da jaridarmu mai tsohon tarihi domin tattauna abubuwan da suka shafi makarantarmu.
Da farko dai na zo nan Bici ne sai na lura cewa babu wata makaranta ta yara mai zaman kanta inda yaranmu za su ri}a zuwa suna karatu a mataki na farko duk da cewa akwai makarantu na gwamnati.
Amma domin ni ma in bada tawa gudunmawar, sai na fara tunanin kafa makaranta domin in taimaki ‘ya ‘yanmu su sami ginshi}in ilimi kafin su tafi dukkan inda Allah ya nufa domin fa]a]a karatun su.
Kuma ina godiya ga Allah ma]aukakin Sarki da maigidana Honorabul Mahmoud Baba Bici saboda goyon bayan da na samu daga gareshi, wanda dukkan irin nasarorin da muka samu a wannan makaranta ta dalilin wannan goyan baya da ya bani ta samu kuma a gaskiya ya cancanci yabo da godiya }warai da gaske.
Wannan shi ne farkon yun}urin kafa makarantar “Baba Memorial Schools” kuma ga shi a yanzu Allah ya ba ta ]aukaka kuma muna ci gaba da }ara ~ullo da sababbin hanyoyi na bun}asa ta, ta yadda al’ummar wannan yanki za su amfane ta sosai
GTK: Yaya matsayin makarantar taku take a yanzu tun da a }alla kun sami shekaru wajen 6 da farawa?
Hajiya Safiya: Babu shakka wannan makaranta ta “Baba Memorial” tana samun ci gaba idan aka dubi yadda muka fara ta. kusan in ce mun fara ne da ]alibai 2 wato ‘ya ‘yan gidanmu amma a yau ina farin ciki cewa muna da ]alibai masu tarin yawa wanda saboda yawan su sai da muka fa]a]a makarantar domin Alhamdulillahi al’ummar wannan yanki sun gamsu da irin kyawawan aiyukan da muke koya wa ‘ya ‘yan su tare da tarbiyyartar sa su.
Sannan a shekarar da ta gabata ne muka yi bikin yaye ]alibai karo na biyu kuma duk wanda ya halarci wannan taro ya ga irin yadda ]alibai masu fita suka nuna irin abubuwan da ake koya masu wanda hakan abin jin da]i ne garemu da iyaye da su kansu ]aliban.
Haka kuma kwanan nan ne muke shirye - shiryen yin bikin yaye ]aliban mu karo na uku inda iyayen yara da sauran manyan ba}i da za’a gayyato za su sake ganin irin ci gaban da wannan makaranta take samu da taimakon Allah da na malamai da iyayen yara da kuma sauran ma’aikatan mu.
GTK: Hajiya ko akwai wasu }arin tanade-tanaden da kuke yi wa wannan makaranta taku domin }ara inganta yanayi na koyo da koyarwa?
Hajiya Safiya: To, da farko dai na yi maka bayanin cewa muna fa]a]a ta domin mun gamsu da yadda al’umma ke kawo mana yara a kodayaushe. Sannan muna }ara kyautata yanayin koyo da koyarwa, ga shi kuma har ana ta }o}arin samar da wadatattun kayan aiki domin yara mu su ci gaba da samun ilimi ingantacce, wa]annan suna daga cikin manufofin mu a wannan makaranta.
GTK. Yaya dangantakar ku take da iyayen yara da kuma hukumomin kula da makarantu masu zaman kansu?
Hajiya Safiya: Wannan tambaya ce mai muhimmancin gaske domin kuwa muna da kyakkyawar fahimtar juna tsakanin mu da iyayen yaran mu sannan ita kanta }ungiyar PTA tana ba mu goyon baya da taimako ta kowane fanni musamman yadda shi kansa shugaban }ungiyar wato Alhaji Adamu Ibrahim Nago]i, mutum ne wanda ba shi da kasala kana kuma baya }osawa wajen tabbatar da ganin wannan makaranta tana samun ingantuwa.
Bugu da }ari, dukkan sauran masu ruwa da tsaki na wannan makaranta suna }o}ari wajen ganin ana samun ci gaba ta kowane fanni wanda hakan abin alfahari ne garemu da wa]anda muke yi domin su wato ]aliban mu.
Maganar sashen kula da makarantu masu zaman kansu kuwa, zan iya cewa ba mu da matsala da su domin ma’aikatar ilimi ta jihar Kano tana aiki bisa sanin ya kamata kuma suna ba mu }a’idojin gudanar da makarantunmu ta yadda kwalliya za ta ri}a biyan ku]in sabulu, muna godiya }warai da gaske.
Haka ma ita }aramar hukumar Bici babu matsala tsakaninmu da su kuma suna amsa dukkan wata gayyata da muka yi masu na wani biki ko taro ,wanda hakan ya isa a fahimci cewa akwai fahimtar juna tsakaninmu da dukkan wa]anda ka ambata.
GTK.: Menene sa}onki ga al’umma da su kansu daliban wannan makaranta ta “Baba Memorial Schools?”.
HAJIYA SAFIYA: Sa}ona shine ina godiya ga duk wani wanda yake da hannu cikin al’ummar tafiyar da makarantar mu, musamman mai gidana Alhaji Mahmoud Baba Bici wanda shi ne ya bani }warin gwiwar fara wannan aiki na alheri ga shi a yau abin ya sami ci gaba.
Sannan ina godiya ga al’ummar garin Bici da kewaye yadda suke yarda cewa makarantar “Baba Memorial School” ta dace da ‘ya’yansu har suke ta kawo yaransu daga sassa daban - daban na wannan yanki namu mai albarka.
A }arshe, ina tabbatarwa da al’umma cewa wannan makaranta za ta zamo abar alfahari ga yaranmu wa]anda su ne shugabannin wata rana. Ina fata kuma Allah ya saka wa da malamanmu da ma’aikatan mu da alherinsu, su kuma ]alibai Allah ya }ara bu]e masu }wa}walwar samun ilimi ingantacce amin.


Madarasatul Abdul’Azeez Ta Yaye [alibai 189

MOHAMMED IBRAHIM, Daga Kaduna

MADARASATUL Abdul’Azeez da aka fi sani da Ali [an Hassan da ke Tudun Wada, Kaduna ta yaye ]alibai 189 a ranar Asabar da ta gabata.
Shugaban makarantar, Ustaz Alhassan Abdulha-mid da ya zanta da wakilin-mu a lokacin bikin yaye ]alibai da aka gudanar a harabar makarantar da ke kan layin Surajo ya ce, daga cikin yawan ]aliban da aka yaye, su maza 65 ne mata kuma 124.
Da yake bayyana ka]an daga cikin matsa-lolin da makarantar ke fuskanta, Ustaz Alhassan ya ce akwai matsalar rashin biyan ku]in wata-wata da iyayen yara ke yi.
Babbar matsalarmu shi ne na rashin biyan ku]in makaranta da iyaye ke yi a kan lokaci kuma ku]in a wata bai wuce Naira ]ari biyu ba, amma wasu iyayen ba su iya biya, inji shi.
A cewarsa da ku]in da iyayen yara ke biya makarantar ke biyan malamanta. Don haka sai ya yi kira ga su iyayen yara su ri}a ]aukar karatun yaransu da muhimmanci.
Ustaz Alhassan ya kuma bayyana cewar, makaran-tar Ali [an Hassan an kafa ta ne a shekarar 1980 da ]alibai biyu, daga bisani aka bu]e ta ga ‘yan unguwa bayan shekara guda.
Ya ce sun fara yaye ]alibai a makarantar tun a shekarar 1987 kuma har yanzu suna yaye ]alibai a kowace shekara.
Abubuwan da aka gudanar a wajen bikin yaye ]aliban sun ha]a da karatun Al}ur’ani mai girma daga bakin ]aliban da aka yaye.
Manyan ba}i da suka halarci bikin sun ha]a da babban Editan jaridar New Nigerian, Alhaji Bala Mohammed wanda ]ansa na ]aya daga cikin ]aliban da aka yaye a wannan rana, tare kuma da sauran iyayen yara.


Jami’ar Bayero Na Hul]a Da Jami’ar Warsaw Ta {asar Poland Tun Dauri — Furofesa Rasheed

ABUBAKAR SADIQ YUSUF, Daga Kano

MU{ADDASHIN Shugaban jamilar Bayero da ke Kano Furofesa Abubakar Adamu Rasheed ya bayyana matu}ar gamsuwarsa da dangantakar da ke tsakanin jami’ar Bayero da Jami’ar Warsaw ta }asar Poland.
Furofesa Abubakar Rasheed ya bayyana haka ne lokacin da shugabar sashin nazari a kan harshe da kuma al’adun Afirka ta Jami’ar Warsaw Farfesa Nina Pawlak ta ziyarce shi a ofishinsa.
Ya ce jami’o’in biyu sun da]e suna taimakekeniya a tsakaninsu ta fuskar nazari da bincike ta hanyar musayar ]alibai a tsakaninsu.
Don haka sai ya yi fatar wannan dangantaka za ta ]ore a tsakanin jami’o’in biyu
Ya kuma gode wa Furofesa Nina Pawlak saboda wannan ziyarar da ta kai Jami’ar Bayero sai ya yi fatar hakan zai }ara taimaka wa jami’o’in biyu
Tun da farko a jawabinta da ta yi a harsen Hausa, Furofesa Nina Pawla ta bayyana cewar ta zo Jami’ar Bayero don ta sada zumunci a tsakaninta da Jami’ar Bayero.
A nasa jawabin shugaban sashin nazarin harsunan Nijeriya na jami’ar Dokta Hafizu Miko Yakasai ya bayyana cewar Furofesa Nina Pawlak da cewar ta zama uwa ga jami’ar Bayero.
Dokta Hafizu Yakasai ya ce shi kansa a wajenta ya yi karatun digirinsa na uku a can }asar Poland, a yanzu haka akwai Malam Isah Charmo wanda take duba shi a karatunsa na digiri na uku
Yace a lokacin ziyarar Furofesa Nina ta duba kundin digiri na Uku na Dokta Yakubu Azare ta kuma gabatar da Ma}alu na ilimi a majalisi daban daban a jami’ar Bayero
Tuni dai Furofesa Nina ta bar kano zuwa Poland bayan da ta kammala ziyarar ta tsawon kwanaki hu]u.

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmaster: Emmanuel Bello