>

 

... Jarida Mai Ratsa Zukata

Gida  Labarai  Ra'ayi  Shafukan Musamman  Tattaunawa  Dandali  Tsokaci  Kudin Talla   Gamu Da Mu   A Tuntube Mu

MANYAN LABARAI

 

Litinin 30  zuwa Laraba 2 ga Yuli, 2008


Gwamna Mahmud Shinkafi Ya Ce:-AHMAD SANI YANA GOYON BAYANA

AN zargi masu baza jita-jita dangane da rahotonnin da ake yawan samu a kan ~a~ewar dangantaka tsakanin Gwamna Shinkafi da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura, a game da manufa da rikicin siyasa.
Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Mahmud Aliyu Shinkafi, ne ya yi zargin a lokacin da ya ziyarci kamfanin buga jaridu New Nigerian da Gaskita Ta Fi Kwabo (NNN) a kwanaki a Kaduna.
Ya fa]i cewa, ba kamar yadda aka ]auka ba, Alhaji Ahmad Sani wanda a yanzu Sanata ne ya bayyana goyon baya a game da shirye-shiryen da yake aiwatarwa tun da aka rantsar da shi a watan Mayun 2007.
Shinkafi shi ne mataimakin tsohon gwamna Ahmad Sani na shekara takwas kuma a kwanakin baya ana bayar da rahotanni kan }azamin fiti-na-fito a tsakanin magoya bayansu.
Kuma Gwamna Shinkafi ya amince cewa, an ]an sami sa~ani a tsakaninsa da Sani a baya. Ya ce sun sasanta junansu lami lafiya a sanadiyyar sanya bakin fitattun dattawa musamman Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.
Gwamnan Zamfara ya lura cewa, babu wani da zai iya fa]in takamaiman abin da ya haddasa rashin fahimta a tsakaninsu don hatta shi ma bai sani ba. Ya ce, “an dai warware komai”.
“Ba a ta~a samun lokacin da muka yi fito-na-fito ba, abin da ga alama ake ganin matsala ce shi ne mutane suna yin zantuttukan siyasa wa]anda ba daidai ba kuma wasu suka ]auke su na tayar da zaune tsaye”, inji shi.
Gwamna Shinkafi ya ce “ha}i}a, Yarima yana farin ciki da }o}arin da muke yi a gwamnatina don ciyar da Jihar Zamfara gaba”.
Ya ce wani ~angare ne na sanya bakin manya a kan rikicin shi ne bu}atar su tsawata wa magoya bayansu a kan su guji ta’annati. Ya ce da yardar Allah abubuwan da ke kawo masu rarrabuwa sun kau.
Haka kuma ya ce ra]e-ra]in rahotannin cewa, majalisar dokokin Jihar Zamfara tana shirye-shiryen }addamar da bincike a kan ayyukan gwamnatin Sani daga 1999 zuwa 2007 ba gaskiya ne ba.
Ya yi bayanin cewa, niyyar ’yan majalisar ita ce gudanar da sanin dukkan ayyuka da kwangilolin da gwamnatiu da ta gabata ta bayar kuma ba a kammala su ba.
Gwamna Mahmud Shinkafi ya ci gaba da cewa, akasarin ayyukan na Gwamnatin Tarayya ne kuma dalilin binciken shi ne don a rubuta rahoto zuwa ga Gwamnatin Tarayya a kan abin da za a yi don hanzarta kammala ayyukan.
Ya nuna ba}in ciki a game da ra]e-ra]in. Ya ce “ban san inda mutane suka sami wa]annan ra’ayoyi ba”.
Gwamna Shinkafi ya ce “babu wasu ayyuka wa]anda ba a kammala su a zamanin gwamnatin Yarima da na soke su ba. Mutanen da suka fa]i sa~anin haka, suna ya]a }arairayi ne”.
Ya ce kashi 80 daga cikin ]ari na tsare-tsaren da ya gada daga Yarima da suka ha]a da ma’aikata da ayyuka suna nan. Ya }aryata wani rahoto kan ya shirya sallamar ’yan majalisar zartarwa na yanzu wa]anda daga gwamnatin Sani suke, inda ya ce, “kuna iya tafiya ku tabbatar ban ta~a wani ba”.

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmasters: Emmanuel C. Bello & Suleiman A. Adamu