|
PDP
Za Ta Yi Shekara 60 A Bisa Mulki — Ogbulafor
— Gwamna Namadi Ya Tallafa Wa ’Ya’yanta
MOHAMMED ADAMU, Daga
Kaduna
A LOKACIN da Gwamna Namadi Sambo ya rabar da kayayyakin rage ra]a]in
talauci a ci gaba da shirinsa na kyautata wa al’umma, shugaban
jam’iyyar PDP na }asa, Cif Vincent Ogbulafor ya da]a jaddada
aniyarsu na ci gaba da mulkin }asar nan har na tsawon shekaru 60.
Shugaban ya yi wannan batu ne a dandalin Murtala Muhammad da ke
Kaduna a yayin wani taro da gwamnatin Jihar Kaduna }ar}ashin
jagorancin Gwamna Namadi Sambo ta shirya don rabar da kayayyakin
rage ra]a]in talauci.
Cif Vincent ya ce, gwamnatin PDP a tarayya da jihohi na aiwatar da
ayyukan da za su ciyar da }asar nan gaba. Shugaban ya ce, nan da }arshen
wannan shekara, gwamnatin Umaru Musa ’Yar’Aduwa za ta samar da wutar
lantarki mai megawatt dubu shida.
Don haka sai shugaban ya shawarci masu }alubalantar jam’iyyar da
cewar, babu wata riba a irin wannan hali. Shugaban wanda ya kar~i
wa]anda suka canza she}a daga wasu jam’iyyu zuwa PDP, ya shawarci
mutanen da kada su nuna wani damuwa a zuciyarsu, saboda babu
bambanci tsakaninsu da ‘yan jam’iyyar wa]anda suka canza she}a da ma
can ‘yan jam’iyyar PDP ne, suka koma AC sun ha]a da Injiniya Bawa
Magaji da Dokta Bala Usman da kuma sauran da suka fito daga
jam’iyyar ANPP da PDP da kuma PRP.
Tun farko a jawabinsa, Gwamnan Jihar Kaduna ya ce, duk ]an jam’iyyar
PDP daga ko’ina idan ya zo Kaduna, ya zo gida ne, saboda haka inji
gwamnan a daidai lokacin da suke ba da kayan yanke talauci, suna
kuma marhaba da tsofaffin ‘yan jam’iyyar PDP.
Gwamna Namadi ya fa]i cewar, gwamnatinsa na taka rawar gani ta
fannoni da dama da suka ha]a da ~angarorin ilimi da gona da kiwon
lafiya da tsaro da samar da abubuwan more rayuwa.
Abubuwan da aka raba sun ha]a da motoci da babura da tarakita da
gidajen sauro da kayayyakin asibiti da kekunan ]inki. Sauran sun
ha]a da kekunan sa}a da fanfon ban ruwa da injunan ni}a da hulunan ]wano.
Sauran manyan ba}i da suka yi jawabi sun ha]a da shugaban jam’iyyar
PDP na shiyyar arewa maso yamma da kakakin majalisar dokokin Kaduna,
Honorabul Ahmed Hassan Jumare da Alhaji Tijjani Ramalan da Suleiman
Hun}uyi da Sanata Isaiah Balat da Sanata Musa Bello.
|