|
|
|
Za A Kafa Sabon
Kamfanin Siminti A Sakkwato
ZA a kafa sabon kamfanin sminti a Sakkwato da zai ri}a samar
da siminti tan miliyan ]aya da rabi a shekara.
Wata sanarwa ]auke da sanya hannun Alhaji Mukhtar Aliyu Shinkafi ta bayyana cewa,
kamfanin na ha]in gwiwa ne tsakanin wani kamfani na }asar Sin (China) mai suna
Zhonghao Overseas Construction Engineering Company Limited (CZOCEL) da kuma
abokin ha]in gwiwarsa na nan Nijeriya mai suna Loratt Capital, inda za a kira
kamfanin da sunan Northrich Cement Limited.
Tun ranar 23 ga Yuli, 2008 aka yi bikin sanya hannu kan yarjejeniyar kafa
kamfanin a hedkwatar kamfanin CZOCELL da ke birnin Beijing.
Manajin Daraktan Kamfanin “CZOCELL, Mista Lia O. Qingling, ne ya sanya hannu a
madadin kamfaninsa a yayin da Alhaji Mukhtar Aliyu Shinkafi ya sanya hannu a
madadin kamfanin Loratt Capital Limited.
Alhaji Mukhtar Shinkafi ya shaida wa wa]anda suka halarci bikin, }udurin
gwamnatin Shugaba ’Yar’Aduwa na warware matsalar wutar lantarki tare da dawo da
amincin da Nijeriya ke da shi.
Wannan kamfanin siminti na Sakkwato dai kamfanin na }asar Suin ne zai mallaki
jarin kashi 55 a yayin da kamfanin Lorat Capital zai mallaki kashi 25 kuma za a
sayar da sauran kashi 20 cikin 100 ga jama’ar Jihar Sakkwato da sauran ’yan
Nijeriya.
Bankin kula da shigowa da fitar da kayayyaki na }asar Chaina (Exim Bank) zai
samar da kashi 90 cikin 100 na ku]in da ake bu}ata yayin da kamfanin
Intercontinental Plc na Nijeriya zai lamunci samar da kayayyakin da ake bu}ata a
nan cikin gida.
Za a yi amfani da fasahar }asar Sin kuma }asar Sin ]in ce za ta gina tare da
tsara yadda za a gudanar da kamfanin har komai ya kankama sannan a horar da ’yan
Nijeriya su ci gaba da gudanar da harkokinsa.
Sanarwar ta ce an za~i Jihar Sakkwato ce don kafa wannan kamfani saboda ita ce
ta fi ko’ina sinadarin da ake yin siminti da shi a duniya a yayin da ake sa ran
samun sinadarin kwal daga Jamhuriyyar Nijar da kuma fatar da ake da ita ta samun
wutar lantarki mai }arfin megawatt 50 daga kamfanin lantarkin da ake shirin
kafawa a Zamfara da zai taimaka wajen fara aikin kamfanin kafin wadatuwar gas a
yankin.
A cikin wannan wata ne ake sa ran isowar }wararru daga }asar Sin domin za~en
inda za a kafa kamfanin a yayin da ake sa ran fara aikin gina kamfanin a Nuwamba
mai zuwa inda ake sa ran ya ]auki tsawon shekaru uku kafin a kammala gina shi.
|
|
|