|
Sanata Waku Ya Yi Allah-Wadai
Da Jingine Soke Za~en David Mark
ISAH AHMED DAGA JOS
Wani tsohon Sanata daga Jihar Binuwai Sanata Joseph Waku, ya yi
Allah- wadai da hukumcin da kotun ]aukaka kara da ke Jos ta yanke na
jingine hukumcin soke za~en Sanata mai wakiltar maza~ar Binuwai ta
Kudu kuma shugaban Majalisar Dattijai, Sanata David Mark da kotun
sauraron }ararrakin za~e da ta yi zama a garin Makur]i ta riga ta yi
na soke za~en kujerar Sanatan a ranar Talatar nan da ta gabata.
Sanata Joseph Waku ya yi Allah- wadai da wannan hukuncin ne bayan da
kotun ]aukaka }arar ta yanke hukuncin a lokacin da yake zantawa da
’yan jarida a harabar kotun.
Sanata Waku wanda shi ne jagoran masu mara wa Alhaji Usman [an
Abubakar Mai Shanu na Jam’iyyar ANPP baya a kan wannan Shari’a ya yi
bayanin cewa, wannan hukumci da kotun ta yanke na jingine hukuncin
da kotun sauraron }ararrakin za~e ta riga ta yi, kisan gilla ne ga
Shari’a a }asar nan. Ya ce hukuncin da kotun sauraron }ararrakin
za~en ta yanke na soke wannan za~e ta yi shi ne a kan hujja.
Tun da farko dai kotun ]aukaka }arar da ke Jos ta jingine hukuncin
da kotun sauraron }ararrakin za~en ta yanke na soke wannan za~e a
zaman da ta yi a ranar Talatar.
Da take karanta yanke wannan hukunci wadda ta yi sama da awa 2 tana
karantawa, Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa ta ce hukuncin da kotun
sauraron }ararrakin za~en ta yanke a kan wannan za~e na Shugaban
Majalisar Dattijai Sanata David Mark ta yi shi a bisa kuskure. Ta ce
tun da farko kotun sauraron }ararrakin za~en ta yi kuskure da ta }i
amicewa da hujjar da Lauyan Sanata David Mark ya gabatar mata na
sakamakon za~en }ananan hukumomi 2 a cikin }ananan hukumomi guda 9
da ake da su a wannan maza~a, ta yi gaban kanta ta yanke wannan
hukunci.
Mai shari’a Zainab Bulkachuwa ta yi bayanin cewa, tun da an riga an
rubuta sakamakon za~en wa]annan }ananan hukumomi a cikin takardun
hukumar za~e ta INEC, a doka ba daidai ba ne Jami’in za~en ya soke
sakamakon wannan za~e ba.
Ta ce tun da an riga an rubuta sakamakon wannan za~e a tashoshin da
aka gudanar da wannan za~e kuma dukkan wakilan Jam’iyyu sun sanya
hannu, to, jami’in za~en ba shi da ikon soke sakamakon wannan za~e.
Don haka sai mai shari’a Zainab Bulkachuwa ta ce wannan ]aukaka }ara
da Sanata David Mark ya yi yana da hujja. A kan haka ta ce kotun ]aukaka
}arar ta jingine wancan hukunci da kotun sauraron }ararrakin za~en
ta yanke a ranar 28 ga watan Fabrairun da ya gabata na soke wannan
za~e na Sanata David Mark.
Yanke wannan hukunci ke da wuya sai magoya bayan Sanata David Mark
suka fara sowa da rungume juna da ka]e-ka]e da raye da raye a
harabar wannan kotu.
Da yake zantawa da ’yan jarida bayan yanke wannan hukunci, Lauyan
Sanata David Mark cewa ya yi “muna matu}ar farin ciki da wannan
hukunci”. Ya ce “a ganina wannan hukunci ya }ara mutunci da }imar
sashin shari’a a Nijeriya”.
Shi ma da yake zantawa da ’yan jarida, Lauyan Alhaji Usman [an
Abubakar Mai Shanu Robert Clark ya ce a duk inda ~angarori biyu suke
ya}i dole ne ~angare ]aya ya sami nasara. Ya ce “mu dai mun yi
iyakar }o}arinmu amma a kwana da sanin cewa ko ba da]e ko ba jima
gaskiya za ta yi halinta a kan wannan kujera”.
A zaman wannan kotu dai shugaban Majalisar Dattijan Sanata David
Mark da Alhaji Usman [an Abubakar Mai Shanu dukkansu ba su sami
halartar zaman kotun ba. Amma wata tawaga a }ar}ashin jagorancin
tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sanata Saminu Turaki da ta }unshi
Nicholas Ugbane da Emmanuel Okpede da Kanar Baba Nyam da Alhaji Sule
Audu da Ambasada Ogbe Ogbande da Abba Omoru da kuma Agbo Oghah ta
wakilci Shugaban Majalisar Dattijan.
|