>
 

 

 

... Jarida Mai Ratsa Zukata

Gida  Labarai  Ra'ayi  Shafukan Musamman  Tattaunawa  Dandali  Tsokaci  Kudin Talla   Gamu Da Mu   A Tuntube Mu

MANYAN LABARAI

 

Alhamis 17 zuwa Lahadi 20 ga Yuli 2008

 

An Sami Nasarar Raba Tagwaye A Saudiyya

MU’AZU HAR[AWA, Daga Jiddah
A wannan Asabar da ta wuce ne aka sami nasarar raba wasu jarirai biyu mata masu suna Safa da Marwa, ’yan }asar Maroko wa]anda aka haifa watanni biyu da suka wuce.
An dai sami nasarar raba tagwayen ne a yayin aiki kashi na bakwai da aka yi masu tun daga lokacin da aka haife su a manne ta }irji da cikinsu kuma suka ha]a hanta guda, lamarin da ya sa aka kawo su asibitin King Abdul’Aziz Medical Centre (KAMC) da ke Jiddah }ar}ashin ]aukar nauyin gudanar da aikin shugaban }asar Saudiyya, Sarki Abdallah, ya yi.
Rukunin Likitoci 24 ne suka shiga aikin fi]ar na sa’o’i tara inda aka sami nasarar raba su kamar yadda shugaban Likitocin, Dokta Abdullah Alrabi’ah, ya shaida wa manema labarai ciki har da wakilinmu jim ka]an da kammala aikin a Jiddah. Ya ci gaba da cewa, wannan shi ne irin aikin na 19 da suka gudanar a cikin nasara.
Dokta Abdullahi Alrabi’ah ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu akwai irin wannan aiki kashi na ashirin da za su gudanar kan wasu mannannun tagwaye ’yan }asar Ira}i da za a yi cikin watan Ramadan mai zuwa. An sami nasarar raba wasu tagwaye ’yan Misira da Oman da Sudan da Malesiya da Saudiyya kuma yanzu ’yan }asar Maroko.
Shi ma Jakadan }asar Maroko a Saudiyya, Malam Abdulkareem Al-Samar, da iyayen wa]annan ’yan mata da aka raba duk sun yaba da yadda aka gudanar da aikin cikin nasara ba tare da an rasa rayukan jariran matan biyu ba.
Kuma sun yaba da irin gudunmawar addu’a da jama’ar duniya suka yi masu da kuma tallafin ku]in aikin da Sarkin Makka ya biya kuma aka aiwatar.
 




 


 

 

 


©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmasters: Emmanuel C. Bello & Suleiman A. Adamu