|
|
|
Shekarau Ya Aza
Harsashin
Gina Matatar Ruwa Ta Watari
ABUBAKAR YUSUF SADIQ, Daga Kano
GWAMNAN Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya aza harsashin gina wata
katafariyar matatar ruwa wadda za ta ci ku]i har Naira miliyan dubu biyar da
miliyan ]ari uku a madatsar ruwa ta Watari da ke yankin }aramar hukumar |agwai.
A jawabinsa a wajen aza harsashin ginin matatar ruwan, Gwamna Ibrahim Shekarau
ya ce in aka kammala aikin, za ta tace ruwa har lita miliyan saba’in da biyar a
kullum.
Ya ce tuni har gwamnati ta bai wa kamfanin da zai gudanar da aikin kafin
al}alami na Naira miliyan dubu ]aya, inda su kuma suka yi al}awarin za su
kammala aikin a cikin watanni ashirin da hu]u.
Gwamnan ya bayyana farin cikinsa ga }ananan hukumomin jihar su 44 saboda ha]in
kai da goyon baya da suke ba gwamnatin jihar a }o}arinta na raba jama’ar jihar
da }arancin ruwan sha.
Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa, a wannan aiki na sabuwar matatar ruwan,
}ananan hukumomin sun yi al}awarin bayar da gudunmawar Naira miliyan dubu ]aya
don a kai ga nasara.
A jawabinsa, mataimakin gwamnan jihar kuma kwamishinan ruwa na jihar, Injiniya
Tijjani Muhammad Gwarzo, ya ce in aka kammala aikin, matatar ruwan za ta samar
da ruwan sha ga jama’ar }ananan hukumomin |agwai da Bichi da Dawakin Tofa da
Tsanyawa da Ungogo da }aramar hukumar Minjibir.
Injiniya Tijjani Gwarzo ya yaba wa gwamnatin jiha saboda dawo da tsarin bayar da
ruwan sha na shiyya wanda a cewarsa hakan ba }aramin taimakawa ya yi ba wajen
wadata jama’ar jihar da ruwan sha.
Ya bai wa jama’ar jihar tabbacin cewa, da yardar Allah gwamnati za ta tsaya
tsayin daka don kammala wannan aiki kamar yadda ta kammala ta Tamburawa.
|