>
 

 

 

... Jarida Mai Ratsa Zukata

Gida  Labarai  Ra'ayi  Shafukan Musamman  Tattaunawa  Dandali  Tsokaci  Kudin Talla   Gamu Da Mu   A Tuntube Mu

MANYAN LABARAI

 

Alhamis 12  zuwa Lahadi 15ga Yuni 2008

 

   

AN KASHE WANI MATASHI A BAKORI

ANA zargin wani yaro mai suna Mu’ammar Tukur Idris, ]an tsohon ]an majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar }ananan hukumomin Bakori da [anja da ke Jihar Katsina ya kashe wani matashi mai suna Shafir Muktar da ke Layin Makama a garin Bakori a yayin rabon gardama.
Rahotannin da muka samu sun ce Sagir Madawaki da Ibrahim Madawaki, ’yan uwan uban Shafir da ke zaune a Layin Madawaki inda iyayen Shafir suke, sun tabbatar da cewa, faruwar wannan kisan ya biyo bayan zargin zagin da wani ]an gidan Tukur Idris ya yi wa wani mutum dattijo kuma wani Bashir da suke tare ya ce me ya sa yake zagin babban mutum. Sai Shafir ya ce don Allah su bari shi ke nan ya isa haka nan.
Kamar yadda bayanai suka nuna daga ~angaren ’yan uwan Shafir, an ce bayan an kammala wannan ne, Shafir yana zaune, sai aka yi zargin Mu’ammar Tukur Idris ya zo kamar yana nuna masa komai ya wuce sai da ya ga ya sakankance, sai kawai ya fito da wu}a ya da~a masa a wuya, ya ja.
Daga nan jini ya fara ]ibar sa, kafin ’yan mintuna ya ce ga garinku nan wato ya rasu.
Wakilinmu ya je gidan tsohon ]an majalisa Tukur Idris don jin ta bakinsa ko wani nasa amma yun}urinsa ya ci tura domin a ranar Juma’a ne aka ce mai gidan bai yi sallar Juma’a a Bakori ba kuma babu wani da zai yi magana kan lamarin.
Sai dai wakilin namu ya ga motar ’yan sanda fara ]auke da jami’an tsaro a }ofar gidan domin tabbatar da tsaro a gidan Makaman da kuma tabbatar da zaman lafiya.
Da wakilinmu ya tuntu~i shugaban }aramar hukumar Bakori, Alhaji Halilu Yahya, don jin ta bakinsa, ya tabbatar masa cewa, lallai abin ya faru. Ya ce a matsayinsa na babban jami’in tsaro, zai tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, “kuma za mu yi gaskiya da adalci ga kowa.”
Alhaji Halilu Yahya ya yi kira ga ]aukacin al’ummar }aramar hukumar Bakori da su ci gaba da zama lafiya da junansu dangane da faruwar wannan lamari.
“Mun je wani gida ni da DPO da sauran ma’aikatansa inda ake zargin Mu’ammar na ~oye ba mu ga kowa ba”, inji shi.
Babban jami’in ’yan sanda na }aramar hukumar, Alhaji Buhari |atagarawa, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce suna nan suna neman Mu’ammar Tukur don jin yadda lamarin ya faru.

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmasters: Emmanuel C. Bello & Suleiman A. Adamu