... Jarida Mai Ratsa Zukata

MANYAN LABARAI

ALHAMIS 17 ZUWA LAHADI 20 GA FABRAIRU, 2011
14 ZUWA 17 GA RABIUL AWWAL, 1432 BAYAN HIJIRA


Matsalar Cunkoson Jama’a: Jonathan Ya Umarci
A Tura Jami’an Tsaro Wajen Horo

SHUGABAN }asa, Dokta Goodluck Jonathan, ya umarci jami’an tsaro da ba tare da ~ata lokaci ba da lallai su halarci kwas a kan tafiyar da dafifin jama’a. Umarnin shugaban }asa ]in yana da nasaba da turereniyar da ta auku a wurin taron gangami kan kamfen siyasa na neman shugabancin }asa da ya gudana a kwanaki a Fatakwal, cibiyar Jihar Ribas. Rayuka da dama sun salwanta a sanadiyyar turereniyar.
Dokta Goodluck Jonathan ya bayar da umarnin a wajen taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) na mako-mako. Ya ji takaicin faruwar lamarin tare da bayar da tabbacin hana aukuwar irin wannan ta tabbatar da jami’an tsaro sun sami horon da ya kamata a kan tafiyar da dafifin jama’a.
Haka kuma wakilan majalisar sun yi wa shugaban }asa da iyalan wa]anda lamarin ya rutsa da su ta’aziyya.
Ministan labarai da sadarwa, Mista Labaran Maku, ne ya sanar da alhinin wakilan majalisar. Ya yaba wa jama’ar shiyyar Kudu maso Kudu a kan yadda suka mara wa shugaban }asa baya a yayin da yake }o}arin ganin ya cimma burinsa na zama shugaban }asa.
Haka kuma ya yi bayanin cewa, wakilan majalisar sun }ara ku]a]en wasu kwangilolin da minista a ma’aikatar wutar lantarki, Mista Nuhu Samo Wya, ya gabatar saboda bu}atar samar da }arin wutar lantarki a }asa.
Ya yi bayanin cewa, an }ara ku]in kwangilar da aka ba kamfanin Rockson Engineering Limited ta wurin samar da lantarki na Gbarain mai }arfin megawat 225 daga Dalar Amurka 138,675,122.20 zuwa Dalar Amurka 220,101,976.79.
Ya ce }arin da aka yi, ya biyo bayan bu}atar ]an kwangilar ya canza tsarin wurin samar da wutar lantarkin don ya }unshi }arin sassa hu]u.
Har ila yau, majalisar ta amince da canza tsarin wurin samar da wutar lantarki na Egbema mai }arfin megawat 338. An bayar da kwangilar aikin a 2006.
Ya ce bu}atar canza tsarin wurin ta biyo bayan bu}atar }asa sassa don samar da wutar lantarki mai }arfin megawat 675. Ya ce an }ara ku]in kwangilar da aka ba kamfanin “Rockson Engineering Limited” daga Dala 128,366,751.74 zuwa Dala 183,021,115.37.
Ministan labaran ya ce majalisar ta amince da a gudanar da ayyukan tuntu~a a kan tsarin injiniya da tafiyar da aiki na aikin samar da wutar lantarki mai }arfin megawat 2600 na Mambila. An ba kamfanonin “Coyne et Bellier da WADSCO & De Crown”, a kan ku]i Dalar Amurka 37,220,067.72 kuma za a kammala aikin a wata 87.

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmaster: Emmanuel Bello