... Jarida Mai Ratsa Zukata

GidaLabaraiSiyasaSana'o'iTattaunawaTsokaciDandaliKiwon Lafia IlimiKudanciHudubaFadi Sonka{asan WajeGamu Da MuTuntu~e Mu

MANYAN LABARAI

ALHAMIS 17 ZUWA LAHADI 20 GA FABRAIRU, 2011
14 ZUWA 17 GA RABIUL AWWAL, 1432 BAYAN HIJIRA


 

Kwamitin Kamfen [in Jonathan Ya
{alubalanci Shugabannin Dattawan Arewa

KWAMITIN kamfe na ]an takarar shugaban }asa, Dokta Goodluck Jonathan ya koka game da wata takardar bayan taro da kwamitin da ya kira kansa shugaban }ungiyar siyasar Arewa ya ci karo da ita.
Takardar koken na ]auke da sa hannun daraktan kafafen ya]a labarai, Malam Abba Dabo, inda suka koka game da yadda kwamitin da ke kiran kansa shugabannin }ungiyar siyasar Arewacin Nijeriya, inda suka yi kira ga sauran jam’iyyu cewa, su ha]u domin su ha]a kai su yi wa PDP taron dangi a za~e mai zuwa.
Takardar ta ci gaba da cewa, Adamu Ciroma da kansa ya bayar da gudunmawa wajen kafawa tare da rainon jam’iyyar PDP da kuma irin maganganun da ya yi na cewa, ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen gina }asa a shekaru da dama da suka gabata.
Amma mun kalli abin ta wata fuska daban kasancewar Malam Adamu Ciroma wani mutum ne da ake matu}ar girmamawa zai ha]a kansa da wa]anda manufarmu ta sha bamban da bu}atun }asa.
Sakamakon faruwar wannan lamari da ya fito fili yana bayyanawa, lallai sai muka ji abin ya kasance wani abu daban, musamman irin yadda yake yin kiran a rusa ainihin gidan da ya sha wahalar ginawa.
A matsayin mutum wanda yake }o}arin tabbatar da dimokura]iyya, mun yi tsammanin zai goyi bayan irin bu}atun mutane masu rinjaye.
Amma ci gaba da yin irin wa]ancan maganganu da za su iya bayar da wata alamar rarrabuwar kai ba za ta haifar da ci gaban da jama’a ke bu}ata wajen ciyar da }asa da jama’arta baki ]aya gaba ba, saboda haka ya zama wajibi a ri}a sara ana duban bakin gatari, domin a tsira da mutunci.
Muna fatar dai Malam Ciroma ba zai mi}a wuya ga mutanen da ba ‘yan jam’iyyar PDP ba, wanda }o}arinsu shi ne su kar~i mulki ta kowane hali.
Muna }ara fa]akar da Ciroma cewa, lallai ya dace ya tabbatar da mi}a wuya ga harkokin kamfe na Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo, wanda ya kasance a matsayin ]an jam’iyyar PDP na asali.

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmaster: Emmanuel Bello