Sama Da Mutane Miliyan 1 Suka
Halarci Maulidin Markazin Na
[ahiru Bauci
UMAR SAYE, Daga Bauci
SAMA da mutane
miliyan guda ne daga cikin }asa da }asashen }etare suka halarci bikin murnar zagayowar Maulidin haihuwar Manzo (SAW), wanda Markazin Sheikh [ahiru Usman Bauci ya gudanar a dandalin Babangida da ke Bauci ranar Asabar da ta gabata.
Sheikh [ahiru Bauci cikin jawabinsa ga al’ummar Musulmi musamman ‘yan siyasa, ya garga]e su kan su guje wa shagalta da hidimomin duniya, suna mancewa da addininsu, inda ya bayyana cewa, hakan zai kai su ga rasa lahirarsu don gyara duniyar wasu.
Haka kuma, ya garga]i Musulmi su ha]a kai su nisanci kafirta juna, su tara hankali waje guda don za~o shugabanni na }warai da za su taimaki Musulunci da Musulmi da kuma ri}e amanar dukkan jama’ar }asa, don haka ya bu}aci jama’a su ]auki addini da sau}i, su ha]a kai don a sami gina addini yadda ya dace ta hanyar bin koyarwar da Manzo (SAW) ya zo da ita.
Don haka ya bu}aci jama’a, su nisanci kafirta juna da kuma tsanani a harkar addini ko cin zarafin wani don bambancin a}ida.
Haka kuma ya yaba game da yadda ake samun }aruwar mahaddatan Al}ur’ani maigirma, saboda a shekarun baya ba su wuce mutane 15 mahaddata a garin Bauci, amma yanzu babu adadi, don haka ya bu}aci a ri}e Al}ur’ani, a yi aiki da shi don samun makoma tagari.
Shi ma Khalifa Tijjani Sheikh Tahir, ya bayyana cewa, Maulidin bana ya }ayatar sosai saboda mutane sun halarta daga }asashen Afirka masu yawa da kuma Saudiyya da akasarin jihohin }asar nan.
Don haka ya shawarci jama’a su fito don yin za~en wanda ke }aunar addininsu ba wanda zai na}asa addininsu ba, shi ne zai kai su zuwa tudun mun-tsira ba.
Sama da makarantun Islamiyya 800 suka shiga jerin gwanon zaga garin na Bauci tun daga safiya har zuwa la’asar don murnar zagayowar ranar haihuwar Manzo (SAW) akasarinsu daga ciki da wajen garin Bauci.
|