Kamfen [in Jonathan A Jos: An [auki Tsauraran Matakan Tsaro
ISAH AHMED, Daga Jos
A SHIRYE-shiryen
zuwan shugaban }asa zuwa Jihar Filato a yau, an baza matakan tsaro ciki da wajen jihar musamman a manyan titunan jihar wa]anda suka dangana da filin wasan Rwanpam inda shugaban zai gudanar da taron.
’Yan kasuwa da ke baje }olin kayansu a kasuwar Taminus da ke Jos an hana su kasa kayansu a wajen kamar yadda suka saba, saboda titin Ahmadu Bello an cika shi da matakan tsaro kuma an hana motoci bi kan hanyar.
Harkokin kasuwanci sun tsaya cik a kan titin Murtala Mohammed da Ahmadu Bello da titin Masallacin Juma’a har zuwa titin Tafawa wa]anda ke kusa da wajen taron.
Shagunan Inyamurai ma ba a bu]e ba, saboda tsoron rikicin da ya faru ranar Talata da rana, saboda gudun sake aukuwar irinsa.
Rundunar ‘yan sanda a jihar ta ce ta ]auki matakan tsaron da za su tabbatar da shugaban }asar ya zo kuma ya koma cikin }oshin lafiya.
A filin jirgin saman Yakubu Gowon inda shugaban }asar zai sauka, wakilinmu ya ce an ]auki tsauraran matakan tsaro inda jami’an tsaro na farin kaya da kaki suna tabbatar da an binciki duk wani abin hawa da ya zo wucewa domin magance duk wata tarzoma da ka iya tasowa.
A cikin wata hira da aka yi da shi, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Alhaji Abdurrahman Akano ya bayyana jami’ansa a shirye suke domin kama duk wanda ya nemi ya kawo cikas a wannan ziyarar ta shugaban }asar.
Shi ma a nasa tsokacin, jami’in hul]a da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mista Apev Jacob Terhemba (ASP), ya garga]i masu abubuwan hawa da kada su kuskura su bi hanyar da ta ha]e zuwa filin wasan Rwangpam wato wurin da shugaban }asar zai }addamar da kamfen ]insa.
Ya }ara da cewa, rashin bin wannan dokar zai jawo }wace abin hawan sannan kuma a ci wa mai shi tara kafin a ba shi abinsa. |