Kasafin Ku]in Naira Biliyan 49:
Majalisa Na Neman {arin Bayani
KWAMITI kan
bankuna da ku]a]e na majalisar wakilai a jiya, Laraba ta nuna shakkunta a game da inda hukumar ajiyar ku]a]en inshora na bankuna ta }asa (NDIC) za ta samo Naira biliyan 49 da miliyan 72 domin gudanar da kasafin ku]inta na kasafin ku]in 2011, saboda babu cikakken bayani a kan inda za ta samo ku]in.
Hukumar NDIC na ]aya daga cikin hukumomin gwamnatin tarayya guda 31 da majalisar ta nace sai sun gabatar da }ididdiga ta shekara a kan yadda za su samo ku]in shiga da kuma yadda za su kashe ku]in a bisa dokar gudanar da harkar ku]i, idan ko ba haka ba, to, ga majalisar ta sha alwashin }in gudanar da wani aiki a kan kasafin ku]in gwamnatin tarayya da ya kai Naira tiriliyan 4 da biliyan 2.
A lokacin da suke sauraron kare kasafin ku]in hukumar NDIC, mambobin kwamitin sun nuna takaicinsu a kan dalilin da hukumar NDIC take son kashe Naira miliyan 622 a kan tafiye-tafiye da kuma kashe Naira miliyan 126 a kan gyara motoci amma kuma babu bayyana dalla-dalla wa kwamitin a kan yadda za a kashe ku]in.
Sai dai kuma, shugaban hukumar NDIC, Alhaji Umaru Jibirin tare da daraktan ku]i na hukumar sun tabbatar wa kwamitin wanda Honorabul Ogbuefi Ozomgbachi cewa, za su kawo bayanan nan gaba.
Amma kuma duk da haka, Alhaji Jibirin ya bayar da ta}aitaccen bayani a kan kasafin na tafiye-tafiye inda ya shaida wa kwamitin cewa, sun sanya ku]i da yawa ne saboda suna horar da jami’an a ciki da wajen Nijeriya.
A kan ku]in kasafin na motoci kuwa, shugaban hukumar NDIC ya ce, “a duk bayan shekara 6, suna gwanjar da motocin su ne su sayi sababbi, saboda duk ma’aikatanmu da ke matakin mataimakin daraktoci da daraktoci sun cancanci a ba su motocin aiki, sannan mun ]auki sababbin ma’aikata kuma za mu }ara wa wasu girma”, inji shi.
Shi ya sa ma a cewar Alhaji Jibirin, ]aukar sababbin ma’aikata ya sanya suka sami }arin ku]in adashin fansho ya tashi daga Naira biliyan 10 da miliyan 3 a shekarar bara, zuwa Naira biliyan 11 da miliyan 3 a shekarar bana.
“A shekarar 2010 muna da ma’aikata 992, yanzu mun ]auki }arin ma’aikata 350, dalilin da ya sa muke samun }arin albashi ke nan”, inji shugaban NDIC.
Duk da haka dai, wakilinmu ya ruwaito cewar, mambobin kwamitin ba su gamsu da bayanan hukumar ba, don haka suka nemi hukumar ta }ara yi masu bayani a kan ma’aikatan da }arin albashin. |