... Jarida Mai Ratsa Zukata

MANYAN LABARAI

ALHAMIS 17 ZUWA LAHADI 20 GA FABRAIRU, 2011
14 ZUWA 17 GA RABIUL AWWAL, 1432 BAYAN HIJIRA


 

RMAFC Ta Garga]i Hukumomin Gwamnati Kan {in Aiki Da {a’ida


HUKUMAR tara da raba ku]a]e (RMAFC) ta ce ba za ta sake lamuntar yadda hukumo-min gwamnati ke }in aiki da hanyoyin tara ku]a]e da biyan su ba.
Hukumar wadda ta damu a kan kasawar da akasarin hukumomin suke yi wajen biyan ku]a]en, ta ce a halin yanzu tana inganta matakai da nufin ba wakilanta ikon magance wa]annan kurakurai.
Shugaban kwamitin harkokin jama’a da sadarwa na hukumar, Ambasada Zubairu Dada, ya fa]a wa wakilinmu cewa, sun }uduri aniyar ganin ana yin gaskiya a wajen tara da tafiyar da ku]a]en da za su shiga asusun tarayya.
Ambasada Zubairu Dada ya ce yana da muhimmanci a sanar da sababbi da tsofaffin wakilan hukumar a kan yadda hukumar take gudanar da ayyukanta.
Ya ce wakilan za su kasance a shirye don fuskantar }alubale kan ingantuwar harkar ku]i da tayarwa a tsimi wajen tara dukkan ku]a]en shigar da ake sanya su a lalitar gwamnati yadda ya kamata.
Ambasada Dada ya ce tayar da su a tsimin zai sanya su iya tafiyar da abubuwan da aka ci karo da su a yayin tattaunawa kuma za su iya sanya ido da tayarwa a tsimi wajen tara ku]a]e da raba su a tsakanin matakan gwamnati uku.
Shugaban kwamitin ya ce sabon tsarin da ake da shi a hukumar ya sanya wakilan hukumar suna mayar da hankali a kan abin da zai amfani }asa ba tunanin abin da jihohinsu na asali suke so ba.

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmaster: Emmanuel Bello