Yadda Ake
Noma Rogo
Daga
Kyaftin Bello Abubakar (Mai ritaya)
Ya kamata mai karatu ya fahimci cewa lokaci ke za~a mana abubuwan da muke tattaunawa. A can baya, idan ba a manta ba, kafin shigowar damina da kuma lokacin da ba ta yi nisa ba mun ta’alla}a bayananmu a kan ababen da gona ke bu}ata gabanin shuka.
A wancan lokaci mun yi bayanai kan sassa da dama da noma ba ya yiwuwa sai da su, kamar sharar gona da hu]a da tayar da kunya da dai sauransu. To, a wannan makon za mu gabatar muku ne da abin da ake kira noman rogo.
Noman rogo wani abu ne da akan gabatar da shi bayan sauran amfanin gona sun yi nisa da shukawa. Wasu ma har an fara cin gajiyarsu. To, a irin wannan lokacin ne ya kamata a tattauna nomansa saboda masu sha’awar yi ko kuma }arin haske ga masu yin noman.
Muna da rogo iri biyu. Mai za}i da mai ]aci:
1.Rogo mai za}i:- Yana nuna da wuri, fiye da rogo mai ]aci. Yakan nuna tsakanin wata shida zuwa wata tara, kuma yana bu}atar kula da zarar an tono shi domin ba ya bu}atar a ajiye shi cikin gona na tsawon lokaci bayan an tono shi, idan ya ]auki dogon lokaci, zai iya lalacewa.
2.Rogo mai ]aci:- Yana ]aukar dogon lokaci kafin ya nuna, yakan kai watanni goma sha biyu (12) zuwa sha takwas (18), kuma za a iya barin shi cikin gona bayan an tono shi na wani tsawon lokaci ba tare da ya lalace ba.
Rogo na bu}atar yanayi mai zafi da kuma lema, ba ya bu}atar yanayi mai sanyi. Idan lema ta yi }aranci rogo kan bar girma kuma ya ri}a zubar da ganyayyakinsa manya. Lokacin da lema ta samu sai ya ci gaba da girmansa kuma ya fito da sabon ganye. Wannan yanayin ke sa rogo juriyar fari. Rogo na jure wa fari in dai har ya rigaya ya girma. Amma ba ya bu}atar fari a yayin da yake ’yan makwanni da dasawa.
Rogo na bu}atar }asa mai laushi, watau ba ta~o ko laka ba. Yana yi sosai a }asar da ba ta da taki na gargajiya ko na Turawa sosai. Haka nan kuma yana da bu}atar rana domin ya sami damar sakin saiwarsa cikin }asa, saboda haka a lokutan da rana ta fi dare tsawo ya fi sakin saiwarsa sosai. Haka nan kuma yana bu}atar iska sosai. Rogo na yi sosai a wuraren da iska ya wadata sosai.
Gyaran gonar Rogo
Gyaran gonar rogo ya ha]a da sare itatuwa tun daga tushe da sassabe sa’annan kuma a }one sassaben da aka yi. Ya zama dole a ri}a aiwatar da haka domin a tabbatar an }one dukkanin wasu cututtuka da ka iya yi wa irin da aka samo lahani bayan an dasa shi cikin gonar.
Ana dasa rogo kan hu]ar tantan ko ta shanu, akan kuma yi masa tudu da hannu. Ana kuma yin dashen rogo ne ta hanyar dasa shi a mi}e ko a ]an karkata shi a cikin }asa.Sai dai a nan Afirka ta Yamma an fi dasa shi kan manyan tudu ko kuma kunyar gona. Kuma tudun kan fara daga tsawon santi-mita 30 zuwa santi-mita 60, tsakanin tudu da tudu yakan kai fa]in mita ]aya zuwa biyu.
Yadda ake shuka rogo ko
kuma dasa shi
Akan gudanar da noman rogo ne ta hanyar shuka shi ko kuma dasa shi. Akasari sun fi dasa shi ta hanyar sassara iccen. Haka nan kuma akan sari dashen bayan an tone rogon, daga nan sai a ]auko itacen domin a sassara su daidai wa daida kafin a ci gaba da dasa su.
Kafin a dasa iccen rogon sai an duba mai lafiya wanda ba shi da wata cuta. Za a sassara shi ne kawai idan lokacin dashe ya }arato, kuma ana sassara shi ne daga gindi ba daga sama ba, saboda daga gindin ya fi ba da nagarta sosai.
Ana sara shi tsawon mita ]aya zuwa biyu domin a ]aure shi a ajiye zuwa kwana biyu ko uku kafin a dasa shi. Yankan daidai-wa-daida da ake yi na dasa rogo, sai ranar da za a dasa shi a gona ake yi.
Dogon yanka ya fi ba da amfani mai yawa, sai dai kuma yana da wuyar aiki a lokacin da ake gyaran gonar rogon. Ana son ka yanka sandar iccen rogon da za ka dasa ya zuwa tsawon santi-mita ashirin zuwa ashirin da biyar. Kuma ana dasa shi cikin }asa misalin kashi biyu cikin uku na wannan yankan da ka yi. Watau ana barin kashi ]aya daga cikin uku a waje, wanda zai yi tsiro daga jikinsa.
Kuma ana dasa rogo ne a yayin da aka samu wadatacciyar lema da kuma wanda ake samun ruwan sama sosai, domin haka ba a dasa rogo sai da damina.
A wuraren da ake ha]a rogo da sauran amfanin gona kamar su wake da masara da gero da dawa da gya]a da dai sauransu, sai a jirkinta dasa rogon har sai damina ta yi nisa sosai, an kusa girbe sauran amfanin gona, sannan sai a dasa .
Noman Rogo
Yana da matu}ar amfani bayan dashen rogo da sati uku ko hu]u sai a yi masa fartanya da hannu, bayan an sanya shanu sun yi beta.
Kuma wa]anda suke da hali, maimakon su yi noma da hannu sukan yi masa feshin maganin ciyawa. Maganin feshin da aka fi yin amfani da shi shi ne, DILL NON wanda ake fesa nauyin kilo 1.6 a kowace kadada ta gona. Idan aka fesa shi a gona, noma ]aya ka]ai yake bu}ata kafin ka girbe shi, ko ka tone shi, kafin rogon ya mamaye gonar.
Kuma ana fesa masa Atrazine kilo biyu a kowace kadada kuma yana da nagarta, ana kuma fesa masa 2, D ester shi ma kilo biyu a kan kowace kadada ]aya, kuma ana son a fesa maganin rana ]aya kafin a dasa rogon. Amma kuma ba a faye son a yi amfani da maganin }wari ba a wajen da ke da }asa mai laushi.
To, iyakar abin da za mu iya gutsura muku ke nan a wannan makon sai kuma wani makon in Allah Ya kaimu, za ku ga ci gaban noman rogon da kuma sauran abubuwan da ba a rasa ba da suka ji~anci noman rogon.
Zuba taki
Rogo yana girma ba tare da an watsa masa taki na gargajiya ko na Turawa ba. Akan watsa masa taki daga lokaci zuwa lokaci, amma ba ko’ina ake watsa masa takin ba. A noma irin na zamani akan watsa masa takin Turawa amma ya danganta da yanayin }asar, Ana watsa masa takin kamfa mai suna 12-12-18 kimanin kilo 450 zuwa 672 a kowace kadada ]aya kuma hakan ya danganta da yanayin }asar gonar. Kuma akan so a watsa takin a lokacin da aka yi dashen.
|