Yadda Ake Banka]o Bayanan
Albuzzaranci Da Facaka Da
Dukiyar Al’ummar A Kwangilolin Jihar Zamfara
A
farko farkon hawansa bisa ga karagar mulkin gwamnatin Jihar Zamfara, Gwamna
Ahmed Sani (Yariman Bakura), ya tabbatar wa Zamfarawa cewar shigowarsa cikin
mulki na da manufar ganin an inganta rayuwar al’ummar Jihar Zamfara tare da
tabbatar musu da samuwar ababen more rayuwa da inganta ayyukan yau da kullum.
Shekaru tara bayan saukarsa daga karagar mulkin jihar, sai ga shi kuma yanzu
majalisar dokokin jihar ta fara banka]o wasu bayanai, wa]anda ke nuna gwamnatin
Yarima ta yi facaka da dukiyar al’umma ga kuma rashin bin }a’aida wajen bayar da
kwangiloli, inda aka bayar da wasu kwangiloli ba takardun yarjejeniya, abin da
ya sa~a wa }a’iadar aiki da doka ko kuma ‘Due Process’, a Turance.
Duk hakan ta faru sakamakon zargin sharholiya da dukiyar talakawa da wasu manyan
jami’an gwamnatin Yarima da yanzu haka ke cikin wannan gwamnatin ta Mahmuda
Aliyu Shinkafi suka yi. Wannan abin da suka yi ta amfani da wannan damar wajen
facaka da kuma wawurar dukiyar talakawa abin kunya da takaici ne.
Tun farko dai a baya Babban Bankin Nijeriya ya ta~a fitar da wani bayani a cikin
shekarar 2004 zuwa 2005, inda ya ce, Jihar Zamfara ta kasance jiha ta biyu a
sahun jihohin da suka fi yawaitar talauci a Nijeriya, kuma jiha ta hu]u da ke da
ha]arin gudanar da kasuwanci da sanya hannun jari sakamakon cin rashawa da kuma
cewar ba tsayayyen mataki na bin }a’aida ga fitarwa da shigar da ku]a]e a cikin
baitulmalin gwamnati.
A }ididdigar da hukumar kula da }ididdigar ci gaban kasuwanci ta Nijeriya ta yi
a shekaru uku na tsakanin shekarar 2004 zuwa 2007 ta tabbatar da Jihohin Zamfara
da Jigawa da Yobe da Kebbi da Ebonyi da Oyo da Gombe da Bayelsa da kuma
Anambara a matsayin jihohin farko da suke da hatsari ga ci gaban inganta rayuwar
al’umma da kulawa da ci gaban kasuwanci da sanya jari ga al’ummarsu.
Wa]annan bayanan duk na masana ne wa]anda ke ganin wa]ansu ababe ba su tafiya
daidai a wasu wurare kuma sun fitar da bayanansu ba domin }iyayya ko }auna ba,
sai domin tabbatar da gaskiyar ababen da ke faruwa domin a yi gyara.
Wannan ne ya kawo mu ga batun binciken da majalisar dokokin Jihar Zamfara ta }addamar
a kan ayyukan da gwamnatin Jihar Zamfara }ar}ashin jagorancin Gwamna Ahmed Sani
Yarima. Wannan bincike an fara shi tun kusan watanni biyar da suka gabata,
lamarin ya yi zafi ne sakamakon ganin yadda wasu bayanan ke }ara tabbatar da
cewar ba a aiwatar da wasu ayyukan a-zo-a-gani na ku]a]en da aka ce an kashe ba,
musamman idan an kamanta da irin ma}udan Biliyoyin Nairori da aka ~atar.
Musamman wuraren da majalisar ta fi mayar da hankali a kan bincikenta sun }unshi
ayyukan hanyoyi da lafiya da ilmi da ruwan sha da kuma wutar lantarki. Akwai
kuma takin zamani da motocin tarakto da aka sayo da kuma sauran ababen da aka
kashe ma}udan ku]a]en gwamnati wajen aiwatarwa amma ana zargin babu su a fili.
A bayanan da suka fara fitowa ana zargin gwamnatin Ahmed Sani Yarima da facaka
da ku]a]en jama’a wajen biya da shirya gangamin taron siyasa da kuma na kamfen
na shugaban }asa, wanda shi tsohon gwamnan ya nemi tsayawa tun da farko.
An bayyana cewar gwamnatin Ahmed Sani Yarima ta ~atar da zunzurutun ku]i har
kusan Naira Biliyan biyu da ]ari shidda ga ayyukan tallar takarar shugabancin }asa
na ANPP da kuma bayar da ku]a]en kyauta, sai kuma yin wasu ayyuka da ba su shafi
al’ummar Jihar Zamfara ba, wa]anda aka rarraba tare da biyan ku]a]e ga wasu
jama’a domin sanya zanen hoton Gwamna Ahmed Sani Yarima na takarar shugabancin }asa
ga gidajensu a kusan ko’ina a Nijeriya.
Kodayake wasu na ganin yana da wuya a yarda da wannan zargin, wannan abin na da
tayar da hankali, idan an kimanta halin da mafi rinjayen matasan Jihar Zamfara
wa]anda ke neman tallafi suke ciki ko kuma yadda suke bu}atar ku]a]en da za a
tallafa musu ga karatunsu a makarantun gaba da sakandare da wa]anda ke a
sakanadare.
Jihar Zamfara dai tana da }ananan hukumomin mulki guda goma sha hu]u, daga cikin
yawan wa]annan }ananan hukumomin mulkin guda uku ne kawai ke kusa da babban
birnin jihar, wato Gusau.
{ananan hukumomin mulkin kuwa su ne Gusau da Tsafe da Bungu]u. Daga cikin
wa]annan }ananan hukumomin mulkin ba ko ]aya wadda aka ha]a ta da layin ruwan
sha na famfo daga gidan ruwa na Gusau, a baki ]ayan shekaru takwas da Yariman
Bakura ya yi yana mulki, inji wata majiyar majalisar.
Ha}i}a, wannan bincike wanda kwamitin musamman da majalisar dokokin Jihar
Zamfara ta kafa na banka]o bayanan da za su taimaka ga fitar da gaskiyar yadda
tsohuwar gwamnatin Yarima ta yi amfani da dukiyar jama’a a tsawon lokacin
wa’adinta bisa karagar mulki.
Irin }orafe-}orafen da wasu ke fa]a cewar wai ga alama ana wannan binciken ne
domin tozarta tsohon gwamna Ahmed Sani da kuma wasu mu}arrabansa, ba komi ne ba,
illa borin tukunya. Domin kuwa kamar yadda Shugaban babban kwamitin binciken na
majalisar dokokin, Alhaji Murtala Adamu Jangebe, ya bayyana, ba ruwan wannan
binciken da wata maganar tozarta wani, illa dai ‘yan Majalisa suna gudanar da
aikin da tsarin mulki ya ba su da ma kuma ya tanada musu, ba wata magana illa
iyaka.
Binciken ya fara gano cewar mu’amalar da aka yi da ku]a]en talakawa a lokacin
tsohuwar gwamnati ya kauce }a’ida, kuma yanzu ne lokacin da za a yi gyaran
wannan }a’idar, domin tabbatar da ita ga al’umma. Muddin ana son ci gaba ga
al’ummar Jihar Zamfara, dole ne a yi gyaran matsalolin da aka riska na
albuzzaranci da facaka da dukiyar talakawa ba bisa }a’ida ba. Ha}i}a, wannan ya
yi daidai domin kuwa zai gyara tafiyarta gaba.
Shi kansa shugaban masu rinjaye na majalisar dokoki jihar, Malam Mani Malam
Mummuni Masamar Mudi, yana ganin dacewar wannan binciken, domin kuwa zai taimaka
wa wannan gwamnati ta yanzu, wajen tabbatar da adalci da kuma gaskiya ga
lamurran mulkinta. Hakan in ji, Mani Malam Mummuni shi ne muhimmin gyara ga ci
gaban jiharmu ta hanyar bayyana gaskiyar yadda lamurra suka gudana a baya domin
amfanin gaba.
Muhimman ayyukan da za a fi kulawa ga binciken, inji wata majiya ta cikin
majalisar, sun }unshi kwangilolin hanyoyi da asibitoci da ruwan sha da lantarki
da samar da kujeri da kuma tebura ga makarantun firamare da na sakanadare. Kayan
noma da sauran ababen da aka bai wa muhimmanci ga ci gaban al’umma.
Baya ga ‘yan majalisa akwai su kansu manyan jami’an gwamnatin Jihar Zamfara
wa]anda suke ganin dacewar wannan aiki, wasu da yawa daga cikinsu a lokacin
gabatar da shaida gaban kwamitocin binciken guda biyu, sun jinjina wa ‘yan
majalisa kan soma wannan bincike tun tafiyar wannan sabuwar gwamnati ba ta yi
nisa ba, domin tabbatar da adalci ga al’ummar Jihar Zamfara baki ]aya.
Kamar yadda bayanin da mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar, Murtala
Adamu Jangebe ya yi, ya tabbatar cewar “Wannan binciken zai kwashe kusan watanni
uku ko ma fiye, kuma zai fi mayar da hankali ne ga irin yadda tsohuwar gwamnatin
Ahmed Sani Yariman Bakura ta aiwatar da mulkinta ga hanyoyin da suka shafi
rayuwar al’umma.
Ya nuna cewar wannan bincike, zai ta~o matsalar ku]a]en da aka kashe wajen bayar
da kwangila da kuma yadda aka bayar da wa]annan kwangilolin da wa]anda aka bai
wa kwangilar da kuma irin yanayin aikin da suka yi a wa]annan kwangilolin.
Haka ma za a binciko bayanan takardun yarjejeniya na ayyukan kwangilolin wa]anda
aka bayar da kuma inda kwangilolin suke. Sai kuma tabbatar da matsayin yanayin
aikin da aka yi da kuma darajarsa da wuraren da aka fa]i an yi wa]annan ayyukan.
Akwai kuma zancen hanyoyin da aka bi na aiwatar da ayyukan na gaskiya da wa]anda
ma babu, domin tantance lamarin bai ]aya ga al’ummar jihar. Wannan kuwa zai ]auki
lokaci ga su, ‘yan majalisar wa]anda za su ziyarci ayyukan domin gani da idonsu,
tare da tabbatar da nagartar aikin da aka yi.
Wannan binciken da aka yi wa la}abin ‘Gani Ya Kori Ji’, zai samar da ingantaccen
tafarki na bai wa al’ummar Jihar Zamfara dama ga sanin ababen da suka faru a
lokaci da kuma }arshen tsohuwar gwamnatin Jihar Zamfara ta Gwamna Ahmed Sani,
domin gano gaskiyar al}ibalar ayyukan na raya }asa da ci gaban al’umma da ake
nuna samuwarsu.
Ba shakka a }arshen zaman wannan kwamitin, al’ummar Jihar Zamfara za su fahimci
gaskiyar inda tun farko gwamnatin Ahmed Sani Yarima ta fuskanta, sakamakon yadda
tun farko ake zargin cewar an kasa gudanar da ayyukan raya }asa da kuma samar da
ci gaban al’umma a maimakon irin yadda gwamnatin ta ke fuskantar zargin
albuzzaranci da yin sama-da-fa]i da dukiyar talakawa a tsawon shekaru takwas na
mulkin Jihar Zamfara.
Wani abin sha’awa ga wannan binciken shi ne kusan duk mafi rinjayen ‘yan
majalisar dokokin Jihar Zamfara sun nuna amincewarsu a kan binciken, tare da
kuma da nuna goyon bayan gayyatar masu ruwa da tsakin gwamnati, wa]anda suka
kula da gudanar da tsohuwar gwamnatin Ahmed Sani yanzu kuma suna cikin wa]anda
ke damawa a ta yanzu.
Kamar yadda shugaban masu rinjayen majalisar, Alhaji Mani Mallam Mummuni, ya }ara
tabbatarwa, “babu wani da za a rufe dangane da wannan binciken, za a binciko
lamurran da suka shafi jama’a, kuma za a bai wa jama’a su yi al}alanci tare da
hukunta masu laifi a gaban hukumar da aka kafa.
Alhaji Mani Malam Mummuni ya bayar da tabbacin cewar, ba shakka wannan binciken
na gaskiya ne, kuma ba wani ja da baya sai har an kamalla shi. [an majalisar
wanda ke wakiltar maza~ar Bukkuyum, ya ci gaba da cewar “A yau kam, ba wani da
zai zo Jihar Zamfara ya yaudari jama’a, ya tafi da dukiyar su, mu, ‘yan majalisa
shi mu }yale shi ko wane ne.
Ba wani tunanin tsoro ko jin kunya a kan }wato ha}}in al’ummar Jihar Zamfara (inji
Mani Malam Mummuni) lamarin wannan bincike abu ne da ya shafi kowa, ba wata
saniyar ware, dole ne ‘yan kwangila da jami’an gwamnati su amsa tambayoyin da
suka shafi ayyukansu.
Duk dai yadda wannan lamarin ya kasance ba shakka, wannan binciken zai banka]o
bayanan sirri wa]anda aka hana jama’ar Jihar Zamfara su gani.
Sai dai kuma abin tambaya a nan shi ne shin yaya makomar wa]anda aka samu da
laifi a cikin wannan albuzzaranci da kuma facaka da dukiyar al’ummar Jihar
Zamfara za ta kasance, musamman ma ‘yan kwangilar da ake zargin suka lashe
dukiyar kwangilolinsu amma ba komi a }asa da kuma jami’an gwamnatin da yanzu ke
damawa a cikin wannan gwamnatin?
Shin ‘yan majalisar za su iya rufe ido kuwa, su hukunta kowa har ma da wa]anda
yanzu tsulliyarsu ta ]uri ruwa, suka fara kamun }afa ko suke bayyana wa duniya
cewar su ba su da masaniyar abin da ake ciki a tsohuwar gwamnati?
Wannan amsar ce, mataimakin shugaban majalisar dokokin, Alhaji Murtala Adamu
Jangebe, ya amsa da cewar, “Ba wani wanda ya fi }arfin doka, duk wanda muka gano
ya kar~i aiki, ya kuma yi wasa da shi bai aiwatar ba, hukuma za ta hannunta shi
bayan kamalla bincike, kuma mu gabatar wa gwamnati da bu}atunmu domin hukunta
shi”
Alhaji Murtala ya }ara tabbatar da cewar za a yi adalci wajen binciken, domin
haka masu ya]a jita-jita a kan wata barazana su ji tsoron Allah su bari, domin
wannan ba zai tayar da hankalinsu ga aikin da aka ba su ba.
Ba shakka dai babbar fatar da ake yi wa wannan kwamitin shi ne ya tabbatar da
gaskiya da adalci a tsakanin wa]anda yake bincike, domin zama abin tarihi da
kuma samar da ci gaba ga Jihar Zamfara.
Dole ne wannan kwamitin ya raba aya da tsakuwa cikin fahimta da hankali, kada a
yi saurin yin da-na-sani wajen hukunta wasu ko hana hukunta wasu domin ra’ayin
siyasa ko kuma neman suna. Wannan ne zai iya tabbatar da adalcin majalisa a
shekaru hu]u da za su kasance nan gaba.
A yi hattara!!
Dingyadi, Lamba 88 Titin Emir Yahaya, Sakkwato.