... Jarida Mai Ratsa Zukata

GidaLabaraiSiyasaSana'o'iTattaunawaTsokaciDandaliKiwon Lafia IlimiKudanciHudubaFadi Sonka{asan WajeGamu Da MuTuntu~e Mu

SA{ON KIRISTOCI

LITININ 16 ZUWA LARABA 18 GA AGUSTA, 2010
6 ZUWA 8 GA RAMADAN, 1431 BAYAN HIJIRA


 

Kirista Da Siyasa

RAJISTAR ZA|E: Abu na farko cikin harkokin siyasa shi ne yin rajista, ta wurin yin rajista ne mutum zai iya samun katin za~e. Wanda bai yi rajista ba, ba shi da ikon jefa }uri’a lokacin za~e, ina so in yi jan hankali game da muhimmancin yin rajistar za~e, domin na yi la’akari akwai Kiristoci da dama, wa]anda ba su damu da yin rajista ba, hujjarsu ita ce ba za su ~ata lokaci su je gun rajista ba tun da }uri’arsu ba za ta iya canza komai ba. Wannan magana ba gaskiya ba ne ko ka]an, }uri’ar ka za ta iya kawo canji a siyasar Nijeriya, idan kowa zai ce ba zai yi rajistar za~e ba, saboda yana ganin }uri’ar sa ba za ta iya yin wani tasiri ba, yaya siyasar Nijeriya za ta kasance ke nan?
MUHIMMANCIN YIN RAJISTA: Yin rajista yana da matu}ar muhimmanci, akwai maganar rajista cikin littafi mai tsarki, ji abin da Manzo Luka ya ce: “A kwanakin nan Kaisar Augustas ya yi shela, cewa a rubuta dukkan mutanen da ke }ar}ashin mulkinsa, wannan shi ne }irga na farko da aka yi a zamanin Kiriniyas, mai mulkin }asar Suriya. Kowa sai ya tafi garinsa a rubuta shi. Yusufu ma ya tashi daga birnin Nazaret a }asar Galili ya tafi }asar Yahudiya, ya je birnin Dauda da ake kira Baitalami (domin shi daga gidan Dauda ne, na cikin zuriyarsa) don a rubuta shi, duk da Maryamu tashinsa, wadda take kuma da ciki” (Luka 2:1-5)
Jama’ar Allah, ku dubi yadda rajista take da muhimmanci! Ku dubi yadda Yusufu mijin Nana Maryamu, ya bar aikinsa na kafinta, ya bar sana’arsa wadda yake samun maku]an ku]i da abinci, ya bar gida da ]akin kwanansa cike da kayan alatu, ya yi tafiya mai nisa kimanin kilomita 110 zuwa130 a kan jaki, ya tafi da Maryamu mai tsohon ciki wata tara wurin da babu tabbacin samun wurin kwana, domin ya yi rajista. Ina Kiristocin da suke ganin ba za su iya barin sana’arsu, ko aikinsu ko da na tsawon awa ]aya domin su yi rajista ba? Ku yi koyi da Yusufu mijin Maryamu, ya bar sana’arsa da duk harkokinsa ya je ya yi kwana da kwanaki domin yin rajista. Ina mataye Kiristoci wa]anda ba sa yin rajista? Ku yi koyi da Maryamu uwar Ubangijinmu Yesu Almasihu, tsohon ciki wata tara bai hana ta yin rajista ba, tafiya mai nisa a kan jaki ba ta hana ta yin rajista ba, tunanin rashin kyakkyawan wurin kwana bai hana ta yin rajista ba, dubi inda ta haihu saboda }o}arin yin rajista.
“Sa’adda suke can, sai lokacin haihuwarta ya yi, sai ta haifi ]anta na fari ta rufe shi da zanen goyo, ta kuma kwantar da shi a wani komin dabbobi domin ba su sami ]aki a masauki ba” (Luka 2:6-7).
Ta dalilin rajista ne aka haifi Yesu Almasihu a waje ba cikin ]aki ba, kowa ya san irin shirye-shirye da mata sukan yi idan lokacin haihuwarsu ya kusa, basa tafiya mai nisa, basa yin nesa da likita, musamman ma haihuwar fari! Amma Maryamu da Yusufu sun }udura sai sun yi biyayya da umarnin hukuma sun je sun yi rajista, ko da hakan zai shafi jin da]i da walwalarsu. Tafiyar Yusufu da Maryamu zuwa wurin yin rajista tafiya ce ba mai sauki ba, duk wanda ya san taswirar }asa mai tsarki, ya san tafiya ce cikin hanya mai rafuffuka, tsaunika, }warurruka, kwazazzabai, tuddai, hawa da gangara. Yusufu da Maryamu sun daure domin su cika umarnin hukuma.
Littafi mai tsarki ya bu}aci kowane mai bin Yesu Almasihu ya yi biyayya da hukuma. Ji abin da Allah ya ce, “Bari kowa ya yi biyayya ga mahukunta, gama babu wani iko sai da yardar Allah. Mahukunta da ke nan kuwa na]in Allah ne, saboda haka duk wanda ya yi wa mahukunta tsayayya ya yi wa umarnin Allah, kuma masu yin tsayayyar nan kuwa za a yi musu hukunci” (Rom 13:1-2).
Ina kira ga dukkan mabiya Yesu Almasihu da mu yi biyayya da hukumomin }asarmu Nijeriya, kamar yadda Allah ya bu}ace mu, dukan wa]anda suke mulkin }asar nan tun daga kansila har zuwa shugaban }asa, Allah ne ya na]a su, Allah ne ya ba su mulkin }asar mu, lokacin da suka bu}aci ’yan }asa su yi rajista wajibi ne mu yi musu biyayya mu je mu yi rajista.
Ina kira ga dukkan Kiristocin Nijeriya, mu yi kishin addininmu, mu yi kishin }asarmu, mu yi kishin jama’armu, mu yi biyayya da fa]akarwar Allah a Littafi Mai Tsarki, mu je mu yi rajista da zarar lokaci ya yi. Rashin yin rajista wula}anta ’yancinka ne na ]an }asa, rashin yin rajista tsayayya da hukuma ne, rashin yin rajista tsayayya da umarnin Allah ne, tsayayya da umarnin Allah zunubi ne. Katin za~e shi ne makaminmu na ya}ar zalunci, shi ne garkuwarmu domin kare kanmu, shi ne kuma asirin nasararmu, Kirista da bai yi rajista ya sami katin za~e ba, yana kama da soja a bakin daga da babu mu}ami a hannunsa, ya zama ganima.
Mataye Kiristoci, ku yi koyi da Maryamu uwar Yesu Almasihu, ta zama gurbi mai kyau gare ku wajen yin biyayya ga mijinta, ta bi umarnin Yusufu mai gidanta ba tare da wata gardama ba, haka Littafi mai tsarki ya koya mana.
“Ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji, domin miji shi ne shugaban mata tasa, kamar yadda Almasihu shi ne shugaban Ikkilisiya mai cetonta kuma” (Afis 5:22-23).
A }arshe ina barinku da wannan aya, “Sa’adda mutanen kirki suke sarauta, kowa da kowa yakan yi biki, amma sa’adda mugaye suka kama mulki mutane sukan ri}a ~uya….Mutane sukan ~uya sa’adda mugaye suka sami iko, amma sa’adda iko ya fita daga hannunsu adalai sukan }aru” (K/Mag, 28:12, 28)
Ta yaya za a iya samun shugabanni masu adalci? Ta yaya mutanen kirki za su yi mulkin Nijeriya? Dole sai mutanen kirki, masu tsoron Allah wa]anda aka maya haihuwarsu, sun yi rajista, sun jefa wa mutanen kirki }uri’a kafin a iya samun shugabanni masu adalci, idan Kiristoci mun }i yin rajista, mun juya baya ga siyasa, mun ce babu ruwan mu.
To, marasa bi za su mamaye harkokin siyasar }asarmu har za a iya kai wa matsayin da za a kafa dokar da za ta haramta wa’azi da ya]a Bishara a }asarmu. Kamar yadda na fa]i makon da ya gabata, Kirista da an maya haihuwarsu ka]ai ne za su iya gyara abubuwan da suka ~aci cikin siyasar Nijeriya. Mu lura, mai tsoron Allah ka]ai ne in ya sami mulki zai iya taimaka wa talaka ya bun}asa }asarmu ya kawo ci gaba iri-iri ya kuma sanya mutane su koma ga Allah mahaliccinsu, kamar yadda Sarki Yosiya ya yi. 2 Sarakuna 23:1-25.

 

©2005 New Nigerian Newspapers Limited.

Webmaster: Emmanuel Bello