Bankin Bada Rance Na [ambatta Ya Ciri Tuta
Daga
JABIRU A. HASSAN Wakilin Gaskiya Ta Fi Kwabo A Kano
TUN kafa bankunan al’umma da gwamnatin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta yi a }asar nan ta kama hanyar samun ingantuwar tattalin arzi}i da kyautatuwar zamantakewar al’umma inda aka kakkafa ire-iren wa]annan bankuna na al’umma masu yawan gaske a kowane lungu da sa}o na }asar nan.
Amma da tafiya ta yi tafiya, sai aka wayi gari ire-iren wa]annan bankuna sun dur}ushe, amma wasu ma babu dalilinsu sakamakon rashin iya tafiyar da al’amuran wa]annan bankuna a matakai na unguwanni kamar dai yadda manufofin kafa su yake.
Haka kuma wasu bankunan ba a ma jin ko labarinsu balle a san me suke ciki tun a wancan zamani, amma ka]an daga cikin wa]ancan bankuna na al’umma har yau ]in nan suna aikin tallafa wa al’umma domin inganta tattalin arzi}insu da kuma kyautata dogaro da kai.
Daga cikin ire-iren wa]annan bankuna wasu ma har sun sami ]aukaka zuwa bankunan bada rance ga masu }ananan sana’o’i wato Micro Finance Banks (MFBS) wa]anda suke ‘yan }alilan ne musamman a Arewacin }asar nan.
“[ambatta-Mako]a Microfinance Bank, yana ]aya daga cikin bankunan bada rance ga masu }ananan sana’o’i da a yau ya zamo zakaran gwajin dafi a Jihar Kano, wanda tanade-tanadensa suka sanya ya ciri tuta wajen kyautata tattalin arzi}in al’ummar wannan yanki ba tare da nuna gajiyawa ba.
Shugaban sashen kasuwanci da bada rance na bankin, Alhaji Bello Magaji Muhammad ya ce bankinsu yana da hanyoyi masu yawa na taimaka wa al’umma abokan hul]a har ma da }ungiyoyin masu sana’o’i da mata da kuma matasa.
Alhaji Bello Magaji Muhammad ya bada misali da yadda wannan banki ya yi fice wajen bada goyon baya ga al’umma bakin gwargwado domin su sami ingantuwar al’amuransu na zamantakewa domin a cewarsa, dogaro da kai abu ne mai muhimmancin gaske musamman ma a wannan zamani.
Ya bada misali da yadda suke hul]a ta aminci da }ungiyoyi masu yawa, kamar }ungiyar masu wankin hula da kaya da }ungiyar samarin mahauta ta [ambatta da }ungiyar matasa ta {ofar Fada da kuma }ungiyar TORAN wato Tricycle Owners and Riders Association of Nigeria wadda }ungiya ce ta masu haya da babura masu }afa 3.
Bugu da }ari, Alhaji Bello Magaji ya ce suna kuma da dangantakar hul]a da }ungiyoyin manoma da kuma su kansu manoman ]ai]aiku masu sha’awar bun}asa nomansu wanda hakan abin alfaharin su ne a wannan banki wanda aka kafa da kyakkyawar niyyar kawo ingantuwar arzi}i a wannan yanki.
Haka kuma ya bayyana cewa, a }ungiyar nan ta TORAN, bankin bada rance ga masu }ananan sana’o’i na [ambatta ya sami nasarar bayar da bashin babura masu }afafu 3 har guda 15, kuma tuni aka kama hanyar mayar da ku]a]ensu saboda wa]anda suka amfani wannan shiri suna }o}ari sosai wajen biyan ku]a]ensu ga bankin.
Dangane da maganar }ungiyar nan ta tsaya da }afarta kuwa, Alhaji Bello Magaji ya sanar da cewa, an sami wani ]an majalisa mai kishin ci gaban al’ummarsa, wato Honorabul Hafizu Sani Maidaji wakilin }aramar hukumar [ambatta a majalisar dokoki ta Jihar Kano, wanda ya ha]a hannu da wannan banki wajen taimaka wa al’ummar wannan yanki.
Ya ce a dalilin wannan kishin }asa na Alhaji Hafizu Sani Maidaji an bada bashin motoci }irar gwaf har guda 20 ga al’umma suna haya da su kuma a cewarsa, kwalliya tana biyan ku]in sabulu musamman idan aka dubi irin nasarar wannan shiri.
Bisa haka ne Alhaji Bello Magaji Muhammad ya jinjina wa Alhaji Hafizu Sani Maidaji saboda taimaka wa al’ummarsa da yake yi suna fita daga cikin }angin talauci, tare da yin irin wannan yabo ga tsohon babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta tarayya, Alhaji Nu’uman Barau [ambatta saboda irin nasa taimakon na ha]in gwiwa da wannan banki nasu.
Alhaji Bello Magaji daga nan sai ya yi kira ga majalisun }ananan hukumomin [ambatta da Mako]a da su ri}a ~ullo da wasu shirye-shirye na tallafa wa masu }ananan sana’o’i ta yadda za a ha]u a rage matsalar nan ta rashin aikin yi a tsakanin al’umma.
Sannan ya bu}aci da a sassauta yanayin yadda makarantu ke sayar da takardun neman shiga karatu wato Application form ta yadda su ma bankunan bada rance ga masu }ananan sana’o’i wato Micro Finance Banks za su sami ikon sayar da ire-iren wa]annan takardun kamar sauran manyan bankuna domin sau}a}a wa ]alibai samun wa]annan takardu.
Haka kuma ya danganta ]imbin nasarorin da bankinsu ke samu da jagoranci mai kyau wanda Alhaji Usman Ali ke yi wa bankin, wanda kuma a cewarsa nan gaba ka]an bankin zai }ara cimma nasarori masu yawan gaske musamman wajen ha~aka sana’o’i na dogaro da kai.
Ya kuma gode wa ]aukacin ma’aikatan wannan banki tare da yaba masu bisa }wazon da suke nunawa har ake samun nasarori, sannan daga }arshe ya bayyana cewa, za su }ara himma domin kyautata tattalin arzi}in al’umma ta kowace fuska.
[aya daga cikin wa]anda suka amfana da bashin motocin, Malam Tijjani Bala {ofar Kudu [ambatta, ]an }ungiyar tsaya da }afarka ya bayyana wa Gaskiya Ta Fi Kwabo cewa, wannan banki ya cancanci yabo, musamman yadda a kodayaushe suke ta }o}arin taimaka wa al’umma ba tare da }osawa ba.
Sannan ya yaba wa ]aukacin ma’aikatan bankin da jagoran bankin, wato Alhaji Usman Ali saboda irin ha]in kai da suke baiwa abokan hul]arsu wanda hakan ya nuna a fili cewa, bankin [ambatta-Mako]a Micro Finance Bank abin dogara ne }warai da gaske.
A }arshe, Malam Tijjani Bala {ofar Kudu [ambatta ya yi godiya ta musamman ga Honorabul Hafizu Sani Maidaji wakilinsu na majalisar dokokin Jihar Kano saboda fitar da su da ya yi daga zaman saurare wanda a cewarsa, a halin yanzu suna da cikakken rufin asiri da taimakonsa. |