|
|
|||
|
|
|||
|
Gida Labarai Ra'ayi Shafukan Musamman Tattaunawa Dandali Tsokaci Kudin Talla Gamu Da Mu A Tuntube Mu |
|||
|
TSOKACI |
|||
|
Litinin 6 Zuwa Laraba 8 ga Yuli, 2009 |
||||
|
|
Rikicin PDP A Zamfara: Wanda Ya [aure Kura ...
Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Mahmuda Aliyu Shinkafi na ]aya daga cikin matasan ‘yan siyasa a Nijeriya da siyasa ba ta yi saurin yi masu halin ]an mangwaro ba. Duk da kasancewarsa ba wani sanannen ]an siyasa ba, dare ]aya Allah Ya tarfa wa garinsa nono da shi da tsohon ubangidansa, Sani Ahmad Yariman Bakura, inda suka kar~e kujerar jagorancin jihar Zamfara daga shekarar 1999 har zuwa shekarar 2007. Duk da yake a wancan lokaci ba wata basira ko ilimi ko ku]i ko hikima da ]aukaka suke da ita a fagen siyasa ba, amma kuma da rana tsaka suka yi wa gogaggun ‘yan siyasar Jihar Zamfara fintinkau, wa]annan ‘yan siyasar sun ha]a da tsohon gwamnan tsohuwar jihar Sakkwato, Alhaji Yahaya Abdulkarim da Janar Aliyu Gusau da kuma Ambasada M. Z. Anka. Wannan ne ya sanya MAS da kuma YARIMA suka kafa tarihi a matsayin za~a~~un gwamna da mataimakin gwamna na farar hula na farko tun lokacin da aka }ir}iro da jihar. Baya ga wannan Yarima da mataimakinsa MAS sun kafa tarihi a matsayin gwamna da mataimakinsa da ba a ta~a jin wani rikici ya ~arke a tsakaninsu ba duk tsawon shekara takwas da suka yi suna jan ragamar Jihar Zamfara. Ga kuma tarihin da suka kafa inda MAS ka]ai ne a duk fa]in Nijeriya da ke matsayin mataimakin gwamna da gwamnansa ya na]a shi a matsayin magajinsa. Sai dai kuma a halin da ake ciki yanzu rikici ya dabaibaye siyasar MAS. Da farko ya ~ata da ubangidan siyasarsa, Ahmad Sani Yariman Bakura har ta kai cewa, ba sa ga maciji da juna. Daga nan kuma ya canza she}a ya koma jam’iyyar PDP. Rikicin da ke tsakaninsa da Yarima ta yi }amari har ta kai ga cewa ya kwance wa duk wani mai goyon bayan Yarima zane a kasuwa, wasu daga cikin magoya bayan Yarima da rana tsaka aka li}a masu kashin kaji, aka tu~e su daga kan mu}amansu yayin da wasu har gidan maza aka kai su. Sai dai kuma a nawa ra’ayi, ba na tausayin Yarima a hannun MAS domin na san cewa, Yarima ba kanwar lasa ba ne ga hannun MAS, duk wanda ke musun haka ya tambayi Obasanjo. Irin matsalar da ‘yan PDP suka hango MAS zai shiga hannun Yarima ne ya sanya suka yi kyakkyawar shawarar yadda za su cece shi a hannun Yarima. Su ‘yan PDP sun fi MAS sanin Yarima a matsayin su na ‘yan adawa domin a tsawon shekara takwas da ANPP ta yi tana mulki a Jihar Zamfara ba su sha da da]i ba. Wanda ya yi wannan kyakkyawan tunanin ceto MAS a hannun Yarima shi ne Alhaji Namadi Ango, shugaban jam’iyyar PDP na jihar. Wata }wa}}warar majiya ta tabbatar da cewa, Namadi Ango ne da kansa ya tuntu~i Janar Ali Gusau da kuma wasu gaggan ‘yan siyasa a jihar, ya kuma cusa masu wannan tunani da ra’ayi nasa, har suka amince da a shigo da MAS a cikin PDP. Ko a wancan lokaci akwai wasu ~angarori da suka nuna adawa da }in amincewarsu da MAS ya shigo PDP, domin a cewarsu kirarin Yarima da MAS ]aya ne wato ‘maso uwa ya so ]anta.’ Suka ce ba wani bambanci tsakanin Yarima da MAS, jirgi ]aya ne ya ]auko su. Amma kuma babbar hujjar da Namadi Ango yake da ita, ba ta wuce cewa, ganin irin yadda Yarima ke adawa da shirin MAS na ‘mu gani a }asa’ inda ake ta yin ayyukan raya jihar da zimmar ciyar da jihar Zamfara gaba, ba shakka akwai bu}atar a taimaka masa wajen kashe mahaukacin kare domin tun asali Hausawa na fa]ar cewa ‘kashin ba}i sai taro.’ Bayan cece-ku-ce da dogon Turanci da aka da]e ana tafkawa, daga }arshe sai Alhaji Namadi Ango ya ja tawagarsa inda suka ha]u da MAS suka kuma nuna masa goyon bayansu ga irin ayyukan raya jiha da gwamnatinsa ke aiwatarwa, suka kuma tabbatar masa da cewa ba su adawa da duk wani wanda ya nuna, ya kuma tabbatar wa duniya cewa burinsa shi ne ciyar da Jihar Zamfara gaba. Alhaji Namadi Ango ne ya bayyana wa MAS cewa, su a jam’iyyarsu ta PDP sun shirya domin su kar~e shi a matsayin sabon mamba a jam’iyyar PDP, shi wannan goron tayin da suka yi masa sun dabaibaye shi ne da damarsu, suka ba shi ya sake tsayawa takarar gwamnan jihar a karo na biyu bayan wa’adin mulkinsa ya }are. Sun tabbatar masa da cewa, shi ne ]an takararsu tilo da ba ya da abokin jayayya. Wannan ne ya sanya MAS ya kar~i wannan tayi da sauri ba tare da wata jayayya ba. Bayan MAS ya shigo PDP sai kuma wasu ‘ya’yan PDP wa]anda ke jayayya da wannan al’amari suka amince da shigowarsa cikin jam’iyyar tare da bayar da goyon bayansu a kan wannan jan namijin da Namadi Ango ya yi. A matakin }asa, jam’iyyar PDP ta yi na’am da wannan }o}ari da reshen jam’iyyar a Jihar Zamfara ya yi, aka kuma shirya gagarumin bikin bai wa MAS tutar PDP a jihar. Sai dai kuma daga ranar da MAS ya shiga PDP, sai wasu ‘yan tsiraru da ya zo da su daga tsohuwar jam’iyyar ANPP suka fara yi masa zagon }asa ta hanyar nuna masa cewa, lallai ne ya }wace jam’iyyar PDP daga hannun su Namadi Ango ya hannanta jam’iyyar ga na hannun damarsa. A matakin }asa jam’iyyar PDP ta rushe dukkan shugabannin jam’iyyar tun daga jiha zuwa }ananan hukumomi har zuwa maza~u. Jam’iyyar ta na]a kwamitin ri}on }warya }ar}ashin jagorancin Alhaji Mahmud Abdulmalik, tsohon mataimakin gwamnan Jihar Bauci. Sauran mambobin kwamitin sun ha]a da Alhaji Ibrahim Mallaha, tsohon shugaban jam’iyyar ANPP da Alhaji Musa Zubairu Nasarawa Mailayi, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Jihar Zamfara kuma tsohon sakataren jam’iyyar ANPP da Ambasada Adamu Umar, tsohon ]an takarar shugaban jam’iyyar PDP da kuma Alhaji Namadi Ango, tsohon shugaban jam’iyyar PDP mai barin gado. Shi dai wannan kwamiti ya fara aiki ne daga ranar 12 ga watan Janairu, shekarar 2009 bayan an rarraba masu takardun wannan nauyi da aka ]ora masu mai ]auke da kwanan wata, 6 ga watan Janairu, 2009, Alhaji Abubakar Kawu Baraje, Sakataren Jam’iyyar PDP na }asa ya sanya wa takardun hannu. Manyan ayyuka hu]u ne aka ]ora wa kwamitin ya gudanar da suka ha]a da gagarumin shiri da tsarin da zai tabbatar da cewa, an shirya da kuma sasanta duk wani rikici da rashin jituwa da ke tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, da tabbatar da cewa, an soma shiri nan take na yadda za a gudanar da sabon za~e domin cike gi~in da aka samu a matakin jiha da }ananan hukumomi da kuma maza~u. Sai kuma bayar da wasu shawarwari masu amfani ta yadda za a samar da zaman lafiya a cikin jam’iyyar PDP a jihar da kuma tabbatar da cewa, an na]a babban kwamitin dattawa da shugabanni su kuma fara taro nan take. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan kwamiti da aka bai wa kwanaki 90 ya gudanar da wannan aiki, ya yi aikinsa kamar yadda aka umarce shi? Wace irin matsala ko matsaloli suka ci karo da shi a lokacin wannan aikin nasu? Za a iya cewa, ba shakka da farko kwamitin ya yi iya }o}arinsa wajen tabbatar da cewa, ya gudanar da aikinsa. Ya yi kazar-kazar wajen zagayawa musamman a garuruwan Gusau da Sakkwato da Kaduna da Abuja, ya kuma sami kusan dukkanin }usoshi da jiga-jigan jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, ya yi taro da su kuma an ]auko hanyar yin sabon tsari inda ake kyautata zaton cewa, da an kai }arshe, da an sami ha]in kai da goyon bayan kowa, kuma da jam’iyyar PDP ta sami zaman lafiya da ci gaba a jihar. Wa]anda ke da hannu wajen ruguje wannan tsari da aka ]auko a bayyane suke, musamman shi jagoran wannan tafiyar wato Alhaji Mahmud Abdulmalik wanda daga baya ya koma ~angaren tsofaffin ‘yan jam’iyyar ANPP, su Alhaji Ibrahim Mallaha da Musa Zubairu ya fitar da maitarsa a fili ya nuna su yake goyon baya. Wannan al’amari ba }aramar illa ya jawo wa wannan kwamitin ri}on }warya ba, domin tun lokacin da ya janye jikinsa daga tsofaffin ‘yan jam’iyyar ta PDP ya rungumi MAS da Mallaha da Musa Zubairu, dukkan shimfi]ar ta aka yi ta rushe. Da farko rikici ya sake ~arkewa tsakanin ~angaren Malam Yahaya Abdulkarim }ar}ashin jagorancin Ambasada Adamu Umar da kuma ~angaren Janar Ali Gusau }ar}ashin jagorancin Alhaji Namadi Ango. A ~angare ]aya kuma, shugaban kwamitin ri}on }warya tare da wasu ‘yan tsirarru sun shirya mago-mago, suka ce za a yi za~en shugabannin jam’iyya amma kuma sun shiga sun shirya wa]anda suke son su yi shugabancin jam’iyyar tare da tabbatar da cewa, manyan mu}aman jam’iyyar duk an bayar da su ga na hannun damar gwamna Mahmuda Shinkafi, musamman mu}amin shugaba da sakataren jam’iyya a matakin jiha. Sai dai kuma wannan shirin bai yi ba, domin hukumar za~e mai zaman kanta ta }asa ta }i ta amince da a gudanar da sabon za~e a Jihar Zamfara domin a cewar hukumar, wa’adin da aka bai wa shugabannin da aka za~a a shekarar 2007 bai cika ba, saboda haka ba wata hujja ko madogara da ake da ita na sake yin za~e. Baya ga wannan tsari da aka bi wajen rushe za~a~~un shugabannin jam’iyyar }ar}ashin jagorancin Alhaji Namadi Ango ya sa~a wa kundin tsarin jam’iyyar PDP. Kamar yadda yake a cikin kundin jam’iyyar, sai idan akwai rigingimu a cikin shugabancin jam’iyya ne za a kira taron shugabannin zartarwa na jam’iyyar inda za su tattauna, su amince da maganar rushe shugabanninsu kuma daga nan sai su rubuta wa babban kwamitin zartarwa ta }asa na jam’iyyar tare da hujjoji a rubuce da ke tabbatar da cewa, akwai bu}atar rushe za~a~~un shugabannin, su kuma a matakin kwamiti, sai an sami amincewar kashi biyu bisa uku na mambobin kwamitin kafin a rushe shugabannin. Sai dai kuma a Jihar Zamfara, Gwamna Mahmuda Aliyu Shinkafi da wasu na kusa da shi na ganin cewa, irin yadda suka ci karensu ba babbaka a jam’iyyar ANPP, haka za ta kasance a jam’iyyar PDP, sai ga shi ruwa ya doke su, sun kasa }wace ragamar jam’iyyar PDP a hannun tsofaffin magoya bayanta. Wannan ne ma ya sanya ake ta ya]a jita-jitar cewa, wasu ne daga cikin magoya bayan jam’iyyar PDP a ~angaren Janar Ali Gusau suke ta }o}arin hura wutar rashin zaman lafiya. Maganar gaskiya ita ce, jam’iyyar PDP ba kamar jam’iyyar ANPP ba, cike take da tsofaffin ‘yan siyasa da tsofaffin sojoji da tsofaffin ‘yan boko da ma’aikatan gwamnati da tsofaffin lauyoyi da masu shari’a da ke da ilimi kuma suna ganin zai yi wuya haka kawai wani ya zo daga sama ya hau su, ya wuce. Saboda haka ba }anshin gaskiya a cikin maganar da ake cewa su Namadi Ango sun koma Abuja abinsu, suna hura wuta, maganar gaskiya ita ce dole ne MAS da ‘yan kazaginsa, su Mallaha da Musa Zubairu su fahimci yadda siyasar PDP take, su fahimci manufofi na a}idun jam’iyyar, su tabbatar da cewa duk abin da za su yi dole ne su yi la’akari da tsarin mulkinta, idan ba haka ba za su ci gaba da tafka shirme a matsayin gwaninta daga, baya ruwansu ya bayar da su. Ba yadda za a yi irin ‘yan siyasa da ‘yan bokon da ke cikin jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara su bari da rana tsaka a amshe masu jam’iyya don kawai gwamnatin da ke mulki a jihar ta shigo cikin jam’iyyar. Wani babban kuskure da MAS da magoya bayansa suke yi shi ne irin yadda suke }o}arin raba kan ‘ya’yan jam’iyyar PDP tsofaffi ta hanyar yi masu tayin mu}amai a matsayinsu na ]ai]aiku, ba a }ungiyance ba, wani lokacin har abin ya kai ga tafka shirme. Yaya za a dubi mutum irin Alhaji Namadi Ango a yi masa tayin mu}amin kwamishina a cikin gwamnatin Alhaji Mahmuda Aliyu Shinkafi? In har da kyakkyawar manufa za a yi wannan, to, kamata ya yi gwamnatin MAS ta zauna da tsofaffin ‘ya’yan jam’iyyar PDP a yi yarjejeniya ta gaskiya da su yadda za a raba mu}amai a matakin gwamnati da kuma na siyasa. Ba wanda zai ce dole ne a ]auki dukkan muhimman mu}amai a bai wa ‘yan tsohuwar jam’iyyar PDP amma kuma matu}ar ana neman goyon bayansu da samun nasarar wannan tafiya, dole ne a yi tafiyar tare da su, ba tare da an nuna masu cewa su ‘ya’yan agola ba ne. Wani babban kuskure da aka yi shi ne bai wa shugabannin }ananan hukumomi 14 mu}aman shugabannin ri}on }warya na jam’iyyar PDP, yayin da aka bar tsofaffin shugabannin jam’iyyar ANPP da PDP hannu rabbana. Me ya hana a ha]a shugabannin ANPP da na PDP ]in a waje ]aya a ba su shugabancin ri}on }waryar sabuwar jam’iyyar PDP? Ba shakka da an yi haka da ba a sami wannan ~araka a jam’iyyar ba. Baya ga wannan matsalar akwai irin yadda ri}on sakainar kashin da Gwamna Mahmuda Aliyu Shinkafi ya yi wa sabuwar jam’iyyarsa ta PDP, maimakon ya ri}e matsayinsa na jagoran jam’iyyar ta hanyar bada umarnin a yi duk wani abu da ya dace a jam’iyyar, sai ya bar jam’iyyar a hannun Mallaha da kuma Musa Zubairu, wa]anda ba su da wani burin da ya wuce su mallake jam’iyyar, su mayar da ita mallakarsu, sai yadda suke so za a yi a cikinta. Akwai bu}atar Mahmuda Aliyu Shinkafi ya nuna cewa, ya gama ]aukar karatun sanin }abli da ba’adin siyasa, idan har yana da sha’awar ganin cewa, Mallaha da Musa Zubairu sun shugabanci jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, to, ai a siyasance zai iya wannan, domin zai iya kiran duk wani jigo a cikin jam’iyyar ya bayyana masa wannan }uduri ko buri ko sha’awar da yake da ita a kan hakan, kuma ba shakka zai iya samun goyon bayan jama’a har ha}arsa ta cimma ruwa. Wata babbar matsala da MAS ya ci karo da ita, ita ce ta yadda aka fita batun gina jam’iyya da yi wa jama’a aiki aka mayar da hankali ga MAS 2011. Kusan daga lokacin da Mahmuda Aliyu Shinkafi ya shiga jam’iyyar PDP har zuwa yau ba wani aikin kirki da gwamnatinsa ta ci gaba da shi, kullum ana wayar gari ne ba wata magana da ake yi illa ta MASS 2011, wannan ne ma ya sanya da yawa daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar PDP tsohuwa suke zargin cewa, kamar shi MAS yana yi masu kallon wa]anda bai amince da su ba, domin idan ba haka ba ne, yaya za a yi mutumin da suka bai wa tabbacin shi ne ]an takarar su zai zo ya mayar da hankalinsa wajen ya}in neman za~e tun lokaci bai yi ba, maimakon ya du}ufa wajen yi wa jama’arsa aiki. Gaskiya ]aya ce, ya kamata Mahmud Aliyu Shinkafi ya mayar da hankalinsa waje ]aya, ya ci gaba da shirinsa na ‘mu gani a }asa’ ya inganta rayuwar jama’ar Zamfara ta hanyar gudanar da ayukkan raya jihar da suka ha]a da samar da ingantattun ruwan sha, kiwon lafiya, bun}asa sha’anin noma da hanyoyin mota a karkara da birni da kuma uwa-uba sama wa matasa aikin yi. Ya kamata gwamnan ya san cewa, lallai yana da }alubale a gabansa na ganin cewa, ya sauke nauyin da jama’ar jihar suka ]ora masa tare da taimakon Ahmad Sani Yariman Bakura, wannan abu ne ka]ai zai sanya a gano wanda ke da gaskiya tsakaninsa da Yarima, domin har gobe akwai masu yi masa kallon cewa, ya yi wa Yarima butulci ne kuma komai nisa, komai rintsi, gaskiya za ta yi halinta. Idan ana son tabbatuwar zaman lafiya da ]orewar nasarar jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, ya zama wajibi MAS ya kira tsofaffin ‘ya’yan jam’iyyar PDP a jihar }ar}ashin jagorancin Alhaji Namadi Ango a ~angare ]aya da kuma sauran ~angarorin Malam Yahaya Abdulkarim da kuma M. Z. Anka domin a yi kyakkyawan sulhu na tsakani da Allah da zuciya ]aya a yi aiki da tsarin da jam’iyyar PDP ta }asa ta bayar da kuma hukumar za~e mai zaman kanta a ciyar da jam’iyyar PDP gaba a Zamfara. Wannan ne ka]ai zai iya tabbatar da nasarar jam’iyyar PDP, ya kawo }arshen wannan rikita-rikita. Ba wani wanda ke iya yin wannan sulhu da ya wuce mai girma gwamna domin shi ne uba kuma jagoran jam’iyyar PDP a jihar. Da ma Hausawa na cewa “wanda ya ]aure kura shi ya san hanyar da zai bi ya kwance ta.”
Muhammad ya rubuto wannan ma}ala ne daga Unguwar Gwaza, Gusau, jihar Zamfara. mkmgwaza@ymail.com
|
|||
©2005 New Nigerian Newspapers Limited.
Webmasters: Emmanuel C. Bello & Suleiman A. Adamu