| |
Litinin 17 zuwa Laraba 19 ga Disamba, 2007
Tunawa Da Kisan Gillar Thomas
Sankara
Daga
ATTAHIRU KAWU-BALA
A cikin tarihin mulkar
al’umma akwai mutane wa]anda jagorancin jama’a bai zama musu wata hanya ta su
cika aljihunsu da ku]a]en jama’a ba, sai dai wata hanya ta yin ayyukan kishin }asa
ga ]imbin jama’a.
Irin wa]annan mutane sun sha fa]a cewa, yin mafarki kawai na gyaran al’umma wani
abu ne da ba zai je ko’ina ba sai an aiwatar da shi a aikace. Kyaftin Thomas
Noel Sankara, yana daga cikin irin wa]annan mutane da ya kasance wani gwarzo ba
kawai a }asarsa ta Burkina Fasso ba, har ma da Afirka.
Ranar 15 ga watan Oktoban da ya wuce ita ce ta zama shekara ashirin da kisan
gillar da aka yi wa Thomas Sankara, shugaban }asar Burkina Fasso. Abin da ya }ara
tuna mana cewa, har yanzu dai Afirka da sauran tafiya a gabanmu. Ya zama wajibi
a tuna da wannan gwarzo.
Muna tunawa da wannan gwarzo ne saboda har yanzu Nahiyar Afirka yun}uri take yi
wajen samun shugabanni nagari, wa]anda ke da hangen nesa kuma masu gaskiya da
ri}on amana, ba ’yan amshin shata ba.
Domin kuwa har a yau ]in nan, rayuwa da manufar Thomas Sankara suna da
muhimmanci wajen nuna irin mulki na misali a kullum aka wayi gari idan an yi
la’akari da irin halin da wannan nahiya ta shiga na bada}alar mulki da hayaniyar
ya}e-ya}e na son zuciya da ke nuna sai kowa ya yi mulki ko da kuwa ba abin da
shi mai son mulkin nan zai kawo na ci gaba ga ]imbin jama’ar da suke cikin }uncin
rayuwa.
Mafi yawancin kashe-kashen magabata musamman ma shugabanni na Nahiyar Afirka sun
faru ne saboda son zuciya da suka haifar da kashe masu matu}ar kishin }asa, maza
da mata. Duk kuwa ba saboda wani dalili na shari’a ba sai don wa]anda suka
aikata hakan su hole tare da wa]anda suka ba su kwangilar aikatawa: Raba arzi}in
Nahiyar Afirka kamar su gwal da sinadarin uraniyum da kuma ci da gumin mutane.
A nahiyar nan, an yi kashe-kashen-gilla masu yawa, wasu ma an manta da su.
Wahalar da nahiyar ta shiga sakamakon mulkin danniya na ’yan mulkin mallaka da
kuma mulkin wariyar launin fata na ‘apartheid’ da aka yi a Afirka ta Kudu, sun
haifar da munanan abubuwan da tarihin wannan nahiyar ba zai ta~a mantawa da su
ba.
An kashe Victoria Mxenge da Ruth First da Steve Biko da Amilcar Cabral da Samora
Machel da Chris Hani da Eduardo Mondlane da Dedan Kimathi da Janar Murtala Ramat
Muhammad da sauransu.
Amma abin da ya bambanta kisan gillar da aka yi wa Sankara da Lumumba duk da
irin takaicinsu kamar yadda Mukoma Wa Ngugi, wani mai yin sharhin al’amurran
siyasa a cikin mujallar ‘BBC Focus on Africa’ ya fa]a, “shi ne sanin cin amanar
da makusantansu suka yi. Kuma wa]anda suka gaje a fili yake sun komar da
al’ummominsu da }arfi baya sosai daga hanyar da aka fara bi ta ci gaba.”
Sankara, kyaftin ]in soja ne mai farin jini, wanda ya hau karagar mulkin Burkina
Fasso, bayan wani juyin mulki da aka yi a shekarar 1983, juyin da ya samu goyon
bayan jama’a sosai a lokacin. Nan da nan bayan hayewa kan gadon mulki, sai
Thomas Sankara ya kafa wasu shirye-shirye na ci gaban zamantakewa da tattalin
arzi}i da za a iya cewa, shi ne wani yun}uri da za a ce gagarumi ne da aka yi a
Nahiyar Afirka. Saboda ya nuna da gaske yake yi.
Tun daga farko ma Kyaftin Sankara ya canza sunan }asar da wanda ’yan mulkin
mallaka suka bayar na ‘Upper Volta’ zuwa Burkina Faso, wato, ‘{asar Mutanen {warai’.
Bayan ya hau kan mulki, ya rage yawan albashin jami’an gwamnati, wanda ya ha]a
da nasa, ya kuma hana yin amfani da motar Marsandi irin wadda manyan shugabanni
ke amfani da ita da hana sayen tikitin jirgi na babbar kujera idan za su yi
tafiya.
Yana daga cikin shugabanni na farko da suka lura cewa, ginshi}in ci gaban
Burkina Faso da ma na Afirka, shi ne a ciyar da matsayin mata gaba. Shi ne
shugaba na Afirka da ya fara bai wa mata mu}amai da kuma sa su a cikin ayyukan
soja. Ya kuma hana auren dole tare da nuna goyon baya ga yin aikinsu da zuwa
makaranta ko da kuwa suna da juna-biyu.
Sankara yana daga cikin masu kishin muhalli na farko, inda ya shuka bishiyoyi
fiye da miliyan goma saboda a raya }asar noma da kuma da}ile kwararowar hamada
ya zuwa yankin Sahel.
Ya kuma taimaka an yi kamfe na allurar rigakafi da a cikin mako guda aka yi wa
fiye da mutum miliyan biyu da rabi, wanda wannan ya kafa abin tarihi a duniya.
Ya kuma ciyar da noman auduga gaba da taimaka wa masu sana’o’in hannu.
Ya raba gonaki wa]anda aka kar~e daga hannun mahandama zuwa ga talakawa kai
tsaye. Wannan ya jawo }aruwar noman alkama a cikin shekara uku kacal, wanda ya
haifar da samar da abinci mai yawa a }asar.
Sankara, har ila yau, ya fara wani shiri na gina hanyoyin mota da jiragen }asa
wa]anda za su ha]e duk }asar, kuma ba tare da taimakon }asashen waje ba, sai dai
kawai ta hanyar albarkatun da suke cikin gida, da yin amfani da zimmar dogaro da
kai da ’yan }asar ke nunawa.
Abubuwan da Sankara ya so yi, sun sami kar~uwa a sassa da dama da suka wuce
}asarsa ta Burkina Faso, wanda wannan ya jawo tsoro ga masu fa]a a ji musamman
ga halin mamaya da }asar Faransa ke nunawa ga }asashen da ta yi wa mulkin
mallaka a yankin Afirka ta Yamma da kuma shugabanni ’yan babakere da suke
wa]annan }asashe da suke kewaye da }asarsa.
Sankara ya sha yin jawabai masu gamsarwa a taruka da dama kamar su OAU a lokacin
wa]anda ke inkarin mulkin mallaka na zamani wanda ake yi ta hanyar kasuwanci da
hul]o]in ku]i. Ya yi adawa da taimakon tallafi daga }asashen waje inda ya ce,
“duk wanda ya ciyar da kai, to, shi ne ke mallakar ka.”
A yau ana yawan maganar matsalar basussukan da ake bin }asashen Afirka da kuma
hanyar mafita. Sankara kuwa yana da maganin matsalar shekaru da dama kafin ma a
zo maganar yafe basussukan da ake bin }asashen Afirka a kewayen tsarin banki na
duniya. Ya yi kira cewa, a ha]a kai a }i biyan basussukan na }asashen waje. A
cewarsa, talakan da aka zalunta ba wajibi ba ne ya biya bashin wanda ke zaluntar
sa. “Bashi wata hanya ce ta mulkin mallaka” a fa]ar Sankara.
Sankara ya }ara da cewa: “Wa]anda suka sa muka shiga harkar bashi caca suke yi,
kamar suna gidan yin caca. Idan har suna samun nasara, ba wata matsala. Yanzu
kuwa suna samun matsala shi ya sa suke cewa a biya.” A hikimar Sankara, sai ya
ce, “to, sun gama yawo”. Don haka kada a biya.
Wannan na daga cikin shawarar da masanin tattalin arzi}i, Jefferey Sachs, kuma
mai bayar da shawara ta musamman ga tsohon sakatare-janar na Majalisar [inkin
Duniya, Mista Kofi Annan, ya ta~a fa]a wa shi, Mista Sachs, a shekarar 2004.
Ya ce ya kamata Afirka ta manta da bashin fiye da Dala biliyan ]ari biyun da ake
bin ta don ta cimma ci gaban da take bu}ata. Abin da Sankara ya }ara a matsayin
}a’idar yin haka a taron Afirka na shekarar 1985, shi ne sai da ha]in kan
}asashen tukuna, kowa ya }i biya kawai.
Saboda wa]anda ba su san wane Sankara ba, ta}aitaccen bayaninsa zai wadatar. A
ranar 25 ga Nuwamban shekarar 1980, bayan an yi wasu zanga-zanga ta ma’aikatan
}wadago a fa]in }asar Burkin Faso, wasu gungun sojoji sun yi juyin mulki a
}ar}ashin jagorancin Kanar Saye Zerbo, wanda kuma tsohon ministan harkokin
}asashen waje ne a gwamnatin da ta gabata a lokacin. Abin da ya jawo ham~arar da
Janar Sangoule Lamizana wanda ya kasance a kan mulkin tun Janairun shekarar
1966.
Bayan an yi wannan juyin mulki sai }ananan sojoji suka nuna rashin jin da]insu
wanda hakan ya sa dole sai da gwamnatin ta za~i ]aya daga cikinsu, Kyaftin
Thomas Sankara, ba tare da an tuntu~e shi ba, sai ta na]a shi ministan labarai.
Wannan ya yi kama da abin da ya faru a Nijeriya. Idan an duba littafin da Janar
Joe Garba ya rubuta mai suna ‘Diplomatic Soldiering’, za a ga cewa, Janar
Murtala ya zama shugaban }asa ne ba da ya nema ba.
To, Sankara ya }i wannan mu}ami da aka ba shi wanda sai da lallami ya kar~a. Duk
da haka, sai da ya fa]a, cewa, shi zai sauka daga baya, ba zai wuce Janairun
shekarar 1982 ba. Hakan kuwa aka yi. Sankara ya sauka daga mu}aminsa a gaban
wani taron ’yan jarida a Afrilun shekarar 1982 wanda ya tabbatar da al}awarinsa
a cikin takardar saukarsa cewa, ya yi haka ne saboda mulkin ya zama na ’yan
tsiraru, jama’a da yawa ba sa jin da]i. A shekarar 1983, Sankara ya zama
shugaban }asa bayan wani juyin mulkin soja da ak a yi, juyin da ya zama na a}ida
ba kawai saboda ya hau karagar mulki ba.
Saboda ya ya}i da rashawa, abin da ke cin tuwo a }waryar Afirka, Sankara ya nuna
misali da kansa, inda ya }i kar~ar albashi fiye da ku]in albashin kyaftin duk da
cewa, shi ne shugaban }asa. Ire-iren wa]annan halaye su ne ba su ji da]i ga
sauran mu}arrabansa ba. Wani mutumin }auye da aka yi hira da shi kwanan nan a
wani shafin intanet, ya ce: “Ban yi mamaki na kashe shi (Thomas Sankara) da aka
yi ba, juyin juya halin ne ya ba ni mamaki ba kashe shi ba. Yana kewaye ne da
mutanen banza, mutanen da ke son su ci bulus da tu}a manyan motoci. Abubuwa da
yawa sun canza a cikin juyin juya halin. Kuma ba ta hanyar da ta dace muhimmiya
ba. Amma saboda juyin juya halin mun ]an san wani abu ka]an game da irin ’yan
siyasar da muke bu}ata.”
Da ma Hausawa suna cewa, mutum tara yake bai cika goma ba. Masu yin sharhin sun
kawo irin abubuwan da ke sa rashin cimma manufofin gwamnati tagari ko da kuwa
shugaban yana da halaye na }warai. Tsohon shugaban Nijeriya, Alhaji Shehu
Shagari ya kawo wannan a cikin littafinsa mai suna ‘Beacon to Serve’, inda ya
kawo yadda manyan jami’an gwamanti ke bayar da shawara ga shugaba duk da cewa,
sun san ba ta dace ba. A }arshe sai ka ga an kai shugaba an baro shi, jama’a
kuwa su ri}a ganin laifin shugaban kai tsaye.
Thomas Sankara, kamar yadda masu yin sharhin lamurran yau da kullum suka }ara
fa]a, “mutum ne mai gaggawar ganin abubuwa sun tafi daidai”. Shi ne wai ya jawo
abin da ya faru da shi. To, amma wannan hasashe idan an lura da halin da
Sankaran ya sami kansa a lokacin, dole sai an yi wuta-wuta! Idan ba saboda ya yi
abin a-zo-a-gani ba, me zai sa mutanen duniya su yi tarukan tunawa da shi a yau?
Wannan kuwa ba sai an je nesa ba, saboda shugabannin }asar ba irin abin da ba su
yi ni ganin cewa, an manta da shi amma sai ga shi abin da Sankara ya ci nasarar
yi a zamaninsa suna nan a cikin zukatan mutanen Afirka da ’yan kishin }asa na
sassan duniya.
Wa]annan abubuwa kuwa sun ha]a da share basussuka da gwagwarmaya da mulkin
danniya da ya}i da rashawa da ci gaban mata da ci gaban karkara da son }asa da
kuma kiwon lafiya ko ilimi. Mene ne aka daina magana a kansa a yau? Kuma wa]anda
suke ganin sun kashe shi, shin sun huta da fitina, me suka cimma a }ar}ashin
mulkinsu? Idan ka cire ru]ani da suka jefa al’umma da rashawa da zalunci, me
suke da shi da za su nuna ya zuwa yau?
An haifi Thomas Sankara a ranar 21 ga Disamban shekarar 1949 a Yako ta }asar
Burkina Faso. Ya shiga makarantar share fagen aikin soja ta Ouagadougou a
shekarar 1966, inda ya gama a shekarar 1969.
A shekarar 1970, ya koma }ara samun horo a makarantar aikin soja a Antsirabe, da
ke }asar Madagaskar. Ya kuma halarci wani samun horon a Faransa a shekarar 1972.
A wannan lokaci ne ya sami wayewa a kan harkokin siyasar kishin }asa wadda ta
zame masa ja gaba ga fahimtar al’amuransa.
An kashe Thomas Sankara a ranar 15 ga watan Oktoban shekarar 1987 tare da wasu
abokansa guda goma sha biyu. Kisan gillar da ake zargin abokinsa, Blaise
Campaore, ne ya jagoranta. To, Sankara ba ya nan, an kashe shi, an bisne a cikin
rami a gefen titi na wajen Ouagadougou saboda kawai a ga an manta da shi, amma
tarihinsa har yau ana sake fitowa da shi don na baya su gane wasu darussa da za
a koya ga irin aikace-aikacen da Nahiyar Afirka ke ciki, kuma suka }i ci suka }i
cinyewa.
Kowa sai ya ware ’yan sojojinsa, ya ce wai gyara yake so ya yi a bisa tsaunukan
dazuka, ana ta kashe-kashe. Ana ta ]ai]aita ha]in kan al’umma don cimma burin
kai kawai. Abin fata a nan, shi ne darussa dai ga su nan ba iyaka. ko Afirka za
ta koyi abin da zai fitar da ita daga wannan }angi na ru]ani?
Haka kuma a mulkin Sankara ma akwai abin darasi, saboda an ce shi ne shugaban
}asa a lokacin mafi talauci a duniya (saboda ya bar duniya da mota guda, kekuna
hu]u, tsohon firji da wasu abubuwa ka]an). Shi ne kuma wanda ya }i yin amfani da
iyakwandishan ]in ofis ]insa saboda a fa]arsa jin da]i ba kowa da kowa ne ke jin
sa a }asar ba!
Shin wannan ba darasi ne babba ga wa]anda ke cewa, su, shugabanni, ne ba?
Attahiru Kawu Bala ya rubuto wannan ma}ala ce daga titin Faru}, Unguwar Tsakuwa,
Azare, Jihar Bauci.
atkaba@gmail.com.
|
|