Dimokura]iyya A Shekaru 11: Makomar Arewa Da Masu Yi Mata Zagon {asa
Daga Jubair Jayawa Malumfashi
NIJERIYA }asa ce mai ]auke da ababen mamaki iri-iri wa]anda wasu ba a ko ta~a tunanin suna iya faruwa kamar yadda suka faru ba, har kuma }urar faruwarsu ta wuce a hakan, ba tare da barin wani abin-a-zo-a-gani ba.
Mussaman idan an yi la’akari da irin wutar rigingimun da suka taso a lokutan da suka gabata dangane da tazarcen mulkin tsohon shugaban }asa, Cif Obasanjo da kuma yadda lamarin ya so ya shafi mulkin dimokura]iyya, ganin yadda Arewa ta ]auki lamarin.
Ba shakka Nijeriya da ‘yan Nijeriya sun }ware sosai wajen janyo da kuma magance matsalolinsu da kawo }arshen kowace irin fitina ta rikita-rikitar siyasa da kuma kutungwila ta ‘yan sai mun kai ga inda muke bu}ata, wa]anda ke }ara ruruta wutar rikici a lokuta dabam-daban a }asar nan.
A ranar 29 ga watan Mayu na kowacce shekara ne ‘yan Nijireya ke murnar zagayowar bukin kafuwar dimokura]iyya, a bana ma an yi wannan buki inda ababe masu yawa suka }ara bayyana a kan makomar siyasar a dimokura]iyyance.
Shekaru 11 na kafuwar wannan dimokura]iyya a Nijeriya cike yake da kwazazzabai da kuma rafuka wa]anda aka tsallake tun ma ba na koyo da kuma nuna }warewa ga wasu wa]anda ke ganin tafiya fa ta fara yin nisa, mussaman ga ‘yan arewa ba.
A arewacin Nijeriya ba shakka shekaru 11 lokaci ne na zaman makoki da juyayi ga duk ]an arewa nagari, sakamakon fa]awa da yankin ya yi cikin wata mummunar masifar kissan mummu}e da kuma nuna bambanci na siyasa da fin }arfi da wa]anda ke mulkin Nijeriya a wannan lokacin suke yi wa yankin.
Tun daga lokacin da gwamnatin dimokura]iyya a }ar}ashin jagorancin Cif Olusegun Obasanjo ta shigo a shekarar 1999 har zuwa yau arewar ce da ‘yan arewa ake ci gaba da muzguna masu ta hanyoyi barkatai, ya Allah da sanin manyansu ne koko a’a, Allah ne Masanin gaibu.
Wannan lamarin kuwa ko bai shafe ka ba, to ya yiwu ya shafi ko wani jininka ko kuma ma}wabcinka ko kuma ]an garinku ko ]an unguwarku ko ]an jiharku ya shafe shi.
Kusan duk sauran yankunna Nijeriya idan ka ]ebe arewa ba wanda ya fi shan wahala da kuma ha]uwa da }as}ancin mulkin kama-karya na waccan gwamnati ta farko ta Obasanjo . Wannan kuwa duk da kasancewar yankin ne ya samar da kusan kashi saba’in da biyar na yawan }uri’un kafa ita gwamnatin. Shin wannan zan ce dara ta ci gida kenan ko kuwa me?
Waiwaye dai in ji Bahaushe ‘ado ne ga tafiya’ na tuna an kori muhimman ‘yan arewa wa]anda ke ri}e da muhimman mu}amai masu muhimmanci a cikin gwamnatin tarayya, haka kuma an tsare wasu sanannun ‘yan arewa domin }iyaya ta siyasa da ~angaranci, ga kuma wasu muhimman ‘yan arewa sun yi asarar dukiyoyinsu da sunan bincike marar kan gado.
Haka ma arewa ta jigata a fannin kasuwanci, tattalin arzi}i da kuma ilimi da muhimman ayyukan ci gaba na gwamnatin tarayya. Arewa ta yi asarar wasu muhimman mu}amai da ke da muhimmanci ga sha’anin tsaro, ilimi, tattalin arzi}i da kuma kasuwanci.
Masana’antun arewa sun fi na kowanne yanki saurin dur}ushewa, tun farkon waccan gwamnati, sakamakon rashin kulawa da kuma zagon }asa da wasa da hankullan ‘yan arewa ga lamarin samar da isasshen makamashi wanda zai zama sinadari ga ci gaban bun}asar tattalin arzi}in yankin.
An rufe kamfanoni masu yawa a arewa ga kuma korar ma’aikata masu ]imbin yawa da kuma watsi da abin da a da ko a mafarki ba zai ta~a faruwa ba, wato arewa ta koma jujin zuba kowane irin tarkacen ababen da suke da muzanatawa ga daraja da mutuncinta.
Wasu jihohin arewa ma albashin }arshen wata ya fara wuya, muddin suna son aiwatar da ayyukan raya }asa ka’in da na’in, a sakamakon biyan jihohi ka]an wato rage ku]a]en kaso-kaso da ake bayarwa na rabon arzi}in }asa, yayin da wasu kuma suka }ara komawa turun bashi.
Irin haka ne bukin cikar dimokoradiyya shekaru 11 ya riske mu a yau, musamman sauran wa]anda muka rage muna da rai, (Allah Ya ji}an ire-iren ‘yan gwagwarmayar ganin gaskiya na wakana a Nijeriya) da rashin kamuwarmu da ciwon suga ko na hauhawar jini ba, wata}ila ko kuma bai kai mizanin girma ba saboda tunanin bai yi yawa ba.
Mai karatu na san kana fahimtata daidai gwargwado, ko ya zuwa yau ]in nan an kai ruwa rana kan al’amurra masu yawan gaske a siyasance, amma dai jama’armu manyansu da yaransu (matasa) kamar ana }ara iza su ne su je su aikata abin da ba a so a yankin na arewa. Kai al’amarin ya kai inda ya kai za~a~~unmu ma sun sayar da martabarmu da mutuncin arewa baki ]aya.
Bayan rasuwar shugaban }asa, Alhaji Umaru Musa ‘Yar’aduwa an ta samun hayaniya da kwakwazo daga mutane da dama kan batun mayar da mulkin }asar nan hannun mataimakinsa, Goodluck Jonathan da kuma batun mayar da mulkin a hannun ‘yan arewa kamar yadda yarjejeniyar da jam’iyyar PDP mai mulkin }asar ta cimmawa na yin shekaru 8 cur a gadon mulki kamar yadda ]an kudancin }asar nan, wato Cif Obasanjo ya yi.
Kodayake ga wanda hankalinsa bai gushe daga jikinsa ba, yakan gane cewa, kusan daga shugabanninmu har zuwa talakawan da ake mulka kanwar ja ce, domin kuwa kusan duk an mance da Allah da horan da Ya yi mana tare da koyarwar Manzo (SAW), kan yadda za mu tafiyar da rayuwarmu baki ]aya. Kai Allah Ya sani wasu za su shiga cikin u}ubarSa dalilin son ransu kawai.
A sanina dai a yanzu a arewa, muna da manyanmu kamr su, tsohon shugaban }asa Muhammadu Buhari, IBB da tsohon mataimakin shugaban }asa Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa akwai kuma wasu Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai, ‘yan majalisun tarayya da na jihohi, wasu muhimman sarakunan gargajiyya, manyan ‘yan boko, ‘yan siyasa da wasu masu kishin ci gaban Nijeriya a cikin }ungiyoyi da kuma malamai da wasu daga sauran talakawan }asa.
Baki ]aya wa]annan sai sun hana kansu barci dare da rana su ci gaba da addu’ar ganin wargajewar wannan shirin da ya kunno kai bayan za~u~~ukan fitar da gwani na jam’iyyun siyasa musamman ma ganin yadda aka gabatar da ‘yan takarar kamar su Goodluck da Riba]o wa]anda ana zargin yaran tsohon shugaba Obasanjo, sannan mu kuma talakawa mu tabbatar mun za~i na }warai da zai fitar da yankin namu kunya, idan ba haka ba kuwa, baya ga mamakin da za mu sha, Allah ba Zai }yale mu haka nan ba sai Ya jarabce mu a nan duniya ko kuma a can lahira.
Ha}i}a da yawansu yau sun fito fili cikin mutunci da daraja a idon mutumen Nijeriya musamman ]an arewa a kan abin da suke }o}arin yi na ceto }asar daga wargajewa da kuma }ara }aimi wajen nuna Nijeriya a gaba fiye da komi a rayuwarsu, musamman ma yahkinsu na arewa.
Wannan zai zama abin alfahari ga talakawan arewa muddin dai tunanin na shugabannin namu a zahiran gaske ne, to, muna iya cewa a zahiri da ba]ini sun yi bamban da sauran wasu ma}iya arewa daga cikin jinin arewar, wa]anda suke yi wa arewa yankan baya domin su cimma biyan bu}atar kansu, wa]anda kuma daga }arshe muke sa ran za su ]auki kunyarsu a hannu.
Daga cikinsu ire-iren wa]annan mutane akwai gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisar tarayya, shugabannin jam’iyyu, ‘yan siyasa da sarakunan gargajiyya da wasu malaman }arya da ~ata gari wa]anda suka yi ban kwana da mutanensu suka sanya son kai da nuna rashin kishin al’umma domin biyan bu}atar kansu da kansu.
Zargin da ake yi shi ne, ]an dattijo Cif Obasanjo da na kusa da shi baya son arewa kuma yana amfani da wasu marasa kishin }asa daga cikin arewa domin wargaza ha]in kai da mutuncin arewa. Wannan na daga cikin dalilan da tun farko, muka karanta cewa Alhaji Sani Zangon Daura ya bayyana dalilansa na ficewa daga cikin majalisar ministocin Obasanjo a wancan mulki, tun ma tafiyar bata yi nisa ba.
Cin mutuncin arewa da ‘yan arewa ya fara ne lokacin da gwamnatin Obasanjo ta yi wa manyan sojojin arewa masu yawa ritaya haka kuma ta kori wasu sanannun manyan ma’aikatan gwamnati ‘yan arewa daga aiki, musamman yadda aka yi wa sauran }wararrun ‘yan arewa a wurare dabam- daban abin takaici ne.
Kamar yadda na fa]a tarihi ba zai ta~a mantawa da takardar da tsohon gwamna Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa ya gabatar a taron dattawan arewa wanda aka yi a watan Maris na shekarar 2002 a garin Kaduna, yau shekaru 9 kenan, inda a taron Bafarawa ya ta~o maganar lallacewar ha]in kai da kuma matsalolin da arewacin Nijeriya ke fuskanta tun lokacin hawan waccan gwamnatin ta Cif Obasanjo bisa karagar mulkin }asar nan. Musamman ganin irin kisan mummu}e da aka yi ta yi wa arewa da kuma uwa uba rashin tasiri ga ci gaba da yin gum da baki da jama’ar wannan yankin suke yi.
Wata babbar matsalar da gwamnatin Cif Obasanjo ta }ara jawo wa arewa, inji [alhatu Bafarawa duk da wannan dimokura]iyya ita ce, ta }arin tashe-tashen hankula a tsakanin al’umma dabam dabam a cikin wannan yankin wanda aka sani da zaman lafiya. To, har ya zuwa wannan shekara ta 2011, arewacin Nijeriya an sanya masu gaba a tsakaninsu ya’alla ta fuskar addini ko }abilanci suka yi ta kashe junansu, dubi misalin Jos mana!
Fa]ace-fa]acen }abilanci da kashe-kashe da kuma fashi da makami sakamakon rashin aikin yi da }aruwar sace-sace da rashin tsaro suna ta yawaita a cikin arewa cikin ]an lokaci }an}ane.
Wa]anan matsalolin sun janyo }arin ci baya ga arewa da kuma su kansu ‘yan arewa a cikin ]an lokaci }an}ane kuma a cikin mulkin dimokura]iyya. Haka kuma arewa na ci gaba da ganin tasku ga jinsin }abilun da kae ganin su ne marasa rinjaye ga }asa.
Wannan matsalar ce yau ake ciki lokacin da arewa da sauran ‘yan uwansu ‘yan Nijeriya ke ganin cewar, dimokurad]iyya ta cika shekaru 11 Wannan lokacin da ma}iya arewa na zahiri suka }ara fitowa fili tare da }iyyayarsu a kan mutunci da darajar arewa. Ba shakka wannan ba }aramar matsala ba ce ga ganin ]orewar ci gaba da samar wa yankin arewa wata makoma wadda za ta kai gaci kafin za~en shekarar 2011, lokacin da ake ganin lokaci ne na raba gardama ga wa]anda suka yi wa arewa butulci.
Wa]anan masu butulci ga arewa da suka yi amfani da ku]a]en jihohinsu ko kuma na al’umamrsu da kuma mu}amansu domin tallata ba}ar haja ta ]orewar ma}iyan arewa bisa mulki wani sabon salo ne da ake so a yi amfani da shi a cimma burin da ake da na }as}anatar da girma da darajar arewar.
Irin haka ya sanya ru]u da firgita ta fara kama wasu daga cikin wa]anda suka ~atar da dukiyoyinsu ga neman wargaza matsayin arewa amma ba su yi nasara ba. Daga cikinsu akwai gwamnoni, ‘yan majalisu, sarakunan gargajiyya da kuma ‘yan siyasa, ‘yan boko, ‘yan kasuwa da sauran irinsu da yanzu kunya ta dabaibayi su ga abin da suke han}oro basu samu nasara ba.
. Ha}i}a wasu daga cikinsu (‘yan uwanmu) sun nuna bajinta ga gaskiya da tsare amanar arewa da ta jama’arsu. Sun ha]u da }iyayya tare da hassada ga wa]anda ke ganin sun fi su cancanta dangane da abin da ya shafi arewa.
Irin yadda a fili aka ~atar da ku]a]en talakawa domin cimma wani buri wanda ba zai amfani al’ummar }asa ba, wani abin takaici ne. Yadda aka hana idanu barci aka ]auke hankalin jama’a da surutai marasa kan gado, domin ganin an samu cimma biyan wata bu}ata ta son kai abin tir ne.
Yanzu ‘yan Nijeriya musamman a arewacin }asar nan suna da bu}atar ganin an ceto su tare da ‘ya’yansu tare da ganin kafuwar dimokura]iyyya ta gaskiya da ba su ha}}insu da kundin tsarin mulki ya basu da ]orewar ha]in kai . Har yanzu fa, arewa ba ta da murya ]aya da take iya magana da ita domin yin fito na fito ga duk wanda ke tsokanarta. Wata}ila a tawa fahimtar talakawa za sun iya canza al’amarin da }uri’unsu masu albarka.
Wasu ‘ya’yan kunama daga cikin ‘ya’yan arewa wa]anda ake ganin sun fi kowa isa ga arewa ne suka janyo mata wannan taskun, hakan ya }ara tabbatar da cewar akwai aiki ja domin magance wannan matsalar da kuma kai }arshen yin maganin lamarin baki ]aya.
Idan har hakan ta faru to, kuwa ba wani mamaki arewa za ta sha kuma zat a samu wata ingantacciyar al}ibla wadda shugabanninta da suka shu]e irinsu Sa Ahmadu Bello Sardauna da Sa Abubakar Tafawa |alewa da malamanta irin su Sheikh Abubakar Gumi da ‘yan siyasar gaskiya irinsu Malam Aminu Kano da sauran ire-irensu suka yi }o}arin kafawa.
[an arewa zai tashi cikin farin ciki da fahimtar ]an uwansa ba tare da nuna bambancin addini ko }abila ba a cikin arewa. Wannan lokacin arewa ta gaskiya da ‘yan arewa nagari za su bayyana a idon }asar nan. Lokacin ne ]an arewa ba zai koma ]aukar wula}anci ko cin mutunci ga duk wani bare ba.
Ba shakka za mu iya samun sabuwar arewa, wadda za ta gina kishin jama’a da son gaskiya a cikin zukatan al’umma maimakon son kai da alfahari. Wannan lokacin }alubalen gaskiya zai fito na gano al}iblar arewa da kuma masoyan arewa.
Za a iya maganin kowane Gwamna ko ]an majalisar da ke ganin ya fi }arfin arewa kuma yana yin yadda ya so wajen sayar da nasa mutunci da na jama’arsa, domin samun kar~uwa ga idon mahassadan arewa. Wa]annan kuwa sun }unshi wa]anda ake bai wa ku]a]e domin su zagi arewa ko wani ]an arewa babba da kuma janyo wa arewa zubar da mutuncinta a idon duniya har ta kai ana ce wa yankin ‘yan ta’adda, kuma abin mamaki ba mai iya nuna ba haka ba ne..
Idan manyan namu suka dawo mana da mutuncinmu, wanda idan suka }i yi Mai duka Zai tambaye su a gobe, lokacin ]an arewa zai iya maganin duk wanda yake cutar da arewa, domin kwa]ayinsa bisa mulki ko samun abin duniya ]an arewa ne koko ba ]an yankin ba ne.
Abin dai sani shi ne, ba shakka arewa za ta ci gba da tafiya tare ko ba tare da wa]annan }ayoyin da ke janyo mata zagi a idon duniya ba. Kuma ba shakka arewa za ta fa]a]a da wasu ‘yan kishin }asa masu son ci gbanta.
Lokacin ne za a fitar da wasu sababbin jini wa]anda ba neman suna dai suke so ba, har ma da samun nasara ga abin da al’ummarsu ke bu}ata. Za a samu arewa ta ‘yan arewa masu bu}atar ci gaban arewa, masu kuma mutunta arewa.
Arewa ta fi kowane ]an arewa girma ga ]orewarta, domin wannan duk wani zagon }asa ko kuma }ulle-}ulle ba zai kai ko ina ba, illa janyo asara da kuma ~ata lokacin mai yin sa.
Arewa barka da ganin dimokura]iyya! ko kuma in ce barka da ganin }umbiya]iyya ne?
Jubair Jayawa Malumfashi, ya rubuto ne daga Kaduna.
|